Ticker

6/recent/ticker-posts

Wanda Ya Ƙi Sharar Masallaci Zai Yi Na Kasuwa

 Za mu fara sallah ke nan liman ya waiwayo ya ce "Dan Allah jama'a a taimaka a sa waya a silence." Kowa ya yi shiru ya yi fuska. Sai wani soja ya waigo fuska murtuƙe 😡 ya ce "Duk wanda ana sallah wayar shi ta yi ringing ni da shi ne." 

Nan take se ga jama'a kowa ya sa hannu aljihu ya na zaro waya. Ni ma na zaro tawa duk da na san tana silent amma dan in ƙara tabbatar wa. Duk da haka ban gamsu ba na sa hannu na cire batirin na watsa su aljihu. Na Ƙara sa hanu aljihu na zaro batirin na canja mai aljihu. Tunani na idan suna aljihu ɗaya za a iya samun akasi wayar ta kunnu saboda kayan bature ba tabbas🙄🙄

Wanda Ya Ƙi Sharar Masallaci Zai Yi Na Kasuwa

Write your comments below or send us jokes to upload. 

Rubuta tsokaci a ƙasa (comment), ko ku turo mana labaran barkwanci domin mu ɗora a kafar.

Post a Comment

0 Comments