Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Shiga Banɗaki Da Waya📲

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh

Allah shi gafatta malam barka da safiya, malam Ina tambaya, Na kasance idan zan shiga banɗaki Ina shiga da wayata, Ina yin charting a kan turomin sakon addu'a kamar haka "Ina maka fatan alkhairi" ko kuma " Allah ya karɓi addu'armu" ni kuma sai na amsa kamar hak " Allahumma ameem ya hayyu ya ƙayyum" Kuma a cikin banɗaki, to shin malam ya matsayin wannan abun yake? Na gode Allah ya saka da alkhairi

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa Alaikumus salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Godiya ta tabbata ga Allah. Ɗan uwa Mafi rinjayen malamai sun tafi a kan cewa makruhi ne a shiga banɗaki da duk wani abu da aka ambaci/rubuta sunan Allah a cikinsa, sai dai idan da larura, kamar tsabar da aka rubuta sunan Allah a kansa.

 Malamai da dama sun bayyana cewa idan sunan ya ɓoye, to babu laifi a cikin haka.

 

 Ibn Ƙudamah (rahimahullah) yana cewa: Idan mutum yana son shiga bayan gida yana da wani abu da aka ambaci sunan Allah a cikinsa, to mustahabbi ne ya ajiye shi a gefe... idan ya kiyaye abin da aka ambaci Allah ɗin a cikinsa kuma tare da shi ya kiyaye kar ya fado, ko kuma ya juya dutsen zoben zuwa cikin tafin hannunsa, babu laifi a kan haka.

 

 Ahmad ya ce: Idan zobe yana da sunan Allah a kansa sai mutum ya juya zuwa cikin tafin hannunsa, ya shiga bandaki (wannan halal ne).

 

 Ikrimah ya ce: Ya juyar da ita kamar haka zuwa cikin tafin hannunsa, ya nannade hannunsa. Wannan kuma shi ne mahangar Ishaƙ, kuma irin wannan rangwame da Ibn al-Musayib da al-Hasan da Ibn Sireen suka yi.

 

 Ahmad ya ce dangane da wani mutum da ya shiga banɗaki ɗauke da tsabar kudi: Ina fatan babu laifi a ciki.

 

Ƙarshen magana daga littafin al-Mughni, 1/109.

 

Haka an tambayi Shaikh Ibn Usaimin (rahimahullah) cewa: mene ne hukuncin shiga dakin wanka da takarda wacce da sunan Allah a kansu? Sai ya karɓa masa da cewa: Ya halatta a shiga dakin wanka da takardu wanda da sunan Allah a cikinsu, matukar suna cikin aljihu, ba a fili suke ba, sai dai a ɓoye a rufe.

 

 Ƙarshen magana daga Fataawa al-Tahaarah, shafi na 109

 

 A kan haka babu laifi ka shiga banɗaki da wayar hannu wacce akwai rubutun Sunan Allah a ciki, ko saƙonni irin wanda ka ce, ko sunan Allah a kan screen ɗin ɗauke da kalmar “Allahu akbar”, matukar ka sanya ta cikin aljihunka, ta yadda ba za ta fito a fili ba.

 

Kuma shi kan sa chart ɗin a banɗaki ya saɓa da ladabtarwar da musulunci ya yi na shiga banɗaki, so ake da ka shiga ka yi maza ka gama buƙatarka ka fito, ba zama charting tare da Shaiɗanu ba.

 

 Kuma Allah ne Mafi sani.

 

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EPG7wVPlgxRFR4R9CdR8xY

 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments