Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar da ke Cin Abincin Mijinta Ba Tare Da Saninsa Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam barka da wuni ya iyali ya kokarin hakuri da Jama'a Allah SWT ya yi sakayya da alkhairi. Malam don Allah Ina tambaya ne Minene hukuncin Matar da mijinta yake kawo nau'ukan abinci kamar dangin Su nama kifi Kwai da sauransu ya saka ta ta girka mashi ya zauna a gabanta da kananan yayansu ya cinye tas ba tare da ya samma Su ko loma ɗaya ba, shi ne Matar takan dan debi kaɗan yadda ba zai gane ba ta baiwa yaran Wani lokacin Idan da yawa ita ma tana ci shi ne take tambaya shin Allah zai kamata da laifin yin sata?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

A'a wannan ba laifi ba ne, kuma ba sata ba ne. Duk da cewar tana dauka ne ba tare da saninsa ba. To amma hakkinta ne da ita da 'ya'yanta cewa mijinta ya rika ciyar da ita idan shi ya ci. To ballantana kuma abin da ita da kanta ta girkashi ta dafashi, sannan shi kuma ya zauna a gabanta ya cinye shi ka'dai ba tare da ya ba ta da ita da 'ya'yanta ba.

Hindu bintu Utbah matar Sayyiduna Sakhru bn Harb (Abu Sufyan) bayan ta musulunta aranar Fathu Makkah, ya yin da ta zo yin Mubaya'a ga Manzon Allah sai ta tambaye shi tace : "Ya Rasulallahi mijina Abu Sufyan yana da kwauro (wato rowa). Ba ya ba ni abin da zai isheni dani da 'ya'yana, har sai na dauki wani abu daga cikin dukiyarsa ba tare da saninsa ba". Sai Manzon Allah ya ce mata "KI DAUKI GWARGWADON ABIN DA ZAI ISHEKI da ke DA 'YA'YANKI TARE DA ADALCI".

Irin wannan rowar tana daga cikin nau'o'in rowa mafi muni domin kuwa Allah ya damka wa kowanne magidanci amanar ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, ilmantarwa da kuma tarbiyyantar da iyalansa. Amma cin abu mai daɗi a gaban iyalai tare da hanasu, to tamkar karkatar da tarbiyyarsu ne. Domin kuwa, da sannu za su fara tunanin yin sata ko bin wata mummunar hanyar domin su rika samun dandana irin wannan abun.

Kuma Allah ya ce "HAKIKA ALLAH YANA YIN AZABA GA WANDA YA KASANCE MAI GIRMAN KAI, MAI YAWAN ALFAHARI, su ne WADANDA KE YIN ROWA KUMA SUNA UMURTAR MUTANE DA YIN ROWAR, KUMA SUNA ƁOYE ABIN DA ALLAH YA BASU DAGA CIKIN FALALARSA...."

Wani mutum ya tambayi Manzon Allah cewa "Ya Rasulallahi mene ne hakkin matar 'dayan cikinmu akansa?". Sai ya ce "Ka ciyar da ita idan kai kaci, kuma ka suturta ta idan kai ma ka suturta kanka". Amma fa duk matar da take satar kuɗi ko kayan abincin mijinta tana sayarwa domin ta yi biki ko zubin adashe da kuɗin, ko turawa iyayenta da kayan satar ko kuɗin satar, to wannan kam barauniya ce. Ta cutar da mijinta Kuma Allah zai karba masa hakkinsa aranar hisabi.

 

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments