Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukunce-Hukuncen Idda Da Takaba

IDDA: Ita ce lokacin da musulunci ya sanya bayan rabuwa tsakanin mata da miji, saboda saki ko mutuwa ko abu mai kama da su, wadda ya zama dole mace ta yi shi kafin ta sake aure.

HUKUNCIN TA

Iddah dole ce a kan mace a lokacin da aka samu sababin ta, saki ko mutuwa ko abu mai kama da su.

IRE-IREN IDDA

1• Iddar wacce aka saka ko mijin ta ya rasu kafin ya sadu da ita.

 Idan sakinta yayi kafin ya sadu da ita, babu idda akanta.

 Idan mutuwa yayi kafin ya sadu da ita, zatayi idda wata huɗu da kwana goma.

2• Iddar wacce aka saka bayan an sadu da ita.

 Idan har tana yin jini, iddar ta ita ce jini uku, jinin haila kenan.

 Idan ba ta jini saboda yawan shekaru ko ƙarancin su (tsufa ko yarin ta), iddarta ita ce wata uku.

* Iddar wacce mijinta ya rasu, idan ba ta da ciki iddarta ita ce wata huɗu da kwana goma.

 Idan tana da ciki kuma iddar ta tana ƙarewa ne a lokacin da ta haihu, koda kuwa bayan ya mutu da kwanaki ne, ko banbancin wasu mintuna.

 Misali da zai mutum da safe sai ita kuma ta haihu da rana, to haihuwarta ta fitar da ita daga iddah.

* Iddar wacce jinin hailar ta ya daina zuwa.

Idan aka saki mace sannan sai jinin hailar ta ya daina zuwa ba tare da ta san dalili ba, to iddarta ita ce shekara ɗaya.

 Amma banda wacce ta yi planning kamar tasa roba ko Allura ko wani abu, ana magane ne a kan wscce hailarta ta ɗauke haka kaeai batadsn dalili ba.

TAMBAYOYI DA AMSOSHIN SU

TAMBAYA:

 Mace ce mijinta ya sake ta sakin kome ɗaya ko biyu, sai ya rasu tana cikin idda ya zatayi?

AMSA:

Za ta bar yin iddar saki, ta yi iddar mutuwa wata huɗu da kwana goma, daga lokacin da ya rasu, kamar yadda za ta ci gadon sa, saboda ya mutu tana matsayin matarsa.

ALLAH shi ne mafi sani.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments