Ticker

6/recent/ticker-posts

Haƙƙoƙin Maƙwabtaka (Tsaraba Ga Maƙwabci, Maƙwabciya, Maƙwabta)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aslm Dan Allah inada tambaya. MENE NE HAKKIN MAƘWABTAKA meya kamata kayima Maƙwabcinka ka fita hakkinshi

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu wajibi ne kowane Musulmi ya san Haƙƙoƙin Maƙwabcinsa da suke kansa, tare da sanin ladaban zama da shi, idan ya san hakan, shi zai sa ya zauna da Maƙwabtansa kamar yadda addini ya tsara.

Malamai sun bayyana Maƙwabci cewa shi ne wanda in ka ƙidaya gidaje arba'in daga jikin gidanka hagu da dama gaba da baya.

A tsarin Musulunci Maƙwabta sun kasu zuwa kashi uku, kowanne da irin Haƙƙoƙin da ke kansa, akwai mai hakki ɗaya da mai hakkoki biyu da kuma mai hakkoki uku.

1. Maƙwabci Musulmi, makusanci (Ɗan'uwa): Shi wannan yana da hakkoki uku, hakkin Musulunci ga hakkin Maƙwabtaka, ga kuma hakkin 'yanuwantaka, wanda yake tsan-tsan ya ga ya dauke dukkan waɗannan hakkoki.

2. Maƙwabci Musulmi: shi wannan yana da hakkoki biyu ne kawai, wato hakkin Maƙwabtaka, sai kuma hakkin Musulunci.

3. Maƙwabci wanda ba musulmi ba: shi ma nan yana da hakki ɗaya ne kawai wato hakkin Maƙwabtaka.

Ubangiji mai girma da daukaka

ya fada cikin littafinSa mai girma, cikin suratul Nisa’i aya ta 36 cewa: “ KU BAUTATAMAN KARKUYI SHIRKA A GARE NI ku yi IHSANI GA IYAYE A KYAUTATA MUSU, DA MAKUSANTA, DA MARAYU, DA MABUKATA, DA MAƘWABCI NA KUSA. ” hai izuwa karshin ayar.

Ayoyi da hadisai sun karfafa hakkin Maƙwabci a kan Maƙwabcinsa. Jibrilu (AS) bai gushe ba yana yi wa Annabi Muhammad wasiyya a kan Maƙwabci har sai da ya yi tsammanin Maƙwabci zai yi tarayya da Maƙwabicnsa a cikin gado. Don haka babu mai munana wa Maƙwabci ya cutar da shi face la’imi marar son alheri kuma abin kyama. Mai aikata dukan fasadi a bayan kasa. 

Manzon Allah yana cewa: “Wallahi bai yi imani ba! Wallahi bai yi imani ba! Wallahi bai yi imani ba! Aka ce, “Ya Manzon Allah! Hakika wannan kuwa ya tabe kuma ya yi asara, wane ne shi?” Ya ce: “Wanda Maƙwabcinsa bai kubuta daga bawa’ikahu ba. Suka ce: “Mene ne bawa’ikahu?” Ya ce: “Sharrinsa.”

Har ila yau, Manzon Allah ya ce: “Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to, ya girmama Maƙwabcinsa, kuma wanda ya kasance ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to, ya girmama bakonsa, kuma wanda ya kasance ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to ya fadi alheri ko ya yi shiru.” Kuma Manzon Allah ya ce: “Mumini, shi ne wanda mutane suka aminta da shi. Musulmi kuma shi ne wanda Musulmi suka kubuta daga harshensa da hannunsa, mai hijira kuma shi ne wanda ya kauracewa mugun abu. Na rantse da Wanda raina yake hannunSa, wanda Maƙwabcinsa bai kubuta daga sharrinsa ba, ba zai shiga Aljanna ba!”

Idan muka yi duba ga wannan Aya da waɗannan Hadisai za mu fahimci girman kyautatawa Maƙwabci da girmama shi, domin girmama shi ma yana nuna cewa mutum ya bayar da gaskiya da Allah da ranar Lahira.

 

Abin kunya ne gare ka ya kai Musulmi! A ce ka kwana a koshi, amma Maƙwabcinka ya kwana da yunwa! Abin kunya ne gare ka a ce ka yi sababbin tufafi amma ka yi rowar tsofaffin tufafinka ga Maƙwabtanka marasa tufa! Kuma abin kunya ne gare ka a ce kana jin dadi da dadadan abinci da abin sha, amma Maƙwabtanka suna neman kasusuwa da sauran abinci, alhali kana sane da fadin Manzon Allah : “Kada Maƙwabciya ta raina abin da za ta ba Maƙwabciyarta ko da kashin hakarkarin akuya ne kuwa.” Kuma ya ce da Abu Zarri (RA): “Ya Abu Zarri idan kana dafa nama ka yawaita ruwan (romo) don ka ba Maƙwabtanka.”

 

Ya kai Musulmi! Lallai daga cikin Haƙƙoƙin Maƙwabci a kanka akwai cewa, ka yi masa sallama idan ka hadu da shi, kuma ka je gaida shi idan ba ya da lafiya, kuma ka raka gawarsa idan ya rasu, kuma ka kasance uba ga ’yan’yansa bayan rasuwarsa kamar yadda shi ya kasance musu a rayuwarsa. Ka tsaya a gefensa (tare da shi) a cikin kunci da yalwa da tsanani da wadata. Wata maganar hikima na cewa: “Wanda amfanar da ’yan uwansa ta kubuce masa, kada ya yarda amfanar da Maƙwabcinsa ta kubuce masa!” Kuma Manzon Allah ya ce: “Mafi alherin aboki a wurin Allah Madaukaki, shi ne wanda ya fi alheri ga abokinsa, kuma mafi alherin Maƙwabci a wurin Allah Madaukaki shi ne wanda ya fi yin alheri ga Maƙwabcinsa.”

 

Haram ne a kanka ya kai Musulmi! Ka rika leka gidan Maƙwabcinka alhali bai sani ba, ko ka ha’ince shi game da iyalinsa. Duk wanda ya leka gidan Maƙwabcinsa ba tare da izininsa ba, Allah zai cika idonsa da wutar Jahannama. Kuma haram ne a gare ka rika kashe kunne domin ka ji abin da yake fada a cikin gidansa ka zama kamar mai leken asiri da maganarsa da aikinsa ba za su kubuta daga gare ka ba.

 

Kuma idan ba za ka iya kyautata wa Maƙwabcinka da dadada masa ba, to ka kame daga cutar da shi, kada ka cutar da shi ko da da gaisuwa don ya samu ya huta a cikin gidansa. Idan ya kira ka, ka amsa masa, idan ya nemi shawararka ka ba shi shawara tagari, idan aka zalunce shi ka taimaka masa, idan shi yake zaluncin ka hana shi. Idan ya kyautata ka gode masa, idan ya munana ka yi masa afuwa, idan ya aikata fasadi kada ka karfafa shi a kai, domin da yawa Maƙwabci zai rike wuyan Maƙwabcinsa a Ranar kiyama ya ce: “Ya Ubangijina! Lallai ne wannan ya rufe min kofarsa, ya ki yi min nasiha, ya gan ni ina aikata sharri bai hana ni ba.” Wani mutum ya ce, “Ya Manzon Allah! Lallai ana ambaton yawan Sallar wance da azuminta, sai dai tana cutar da Maƙwabcinta.” Sai ya ce: “Tana cikin wuta!” Sai ya ce: “Ya Manzon Allah! Lallai wance ana cewa tana da karancin Sallah da azumi, amma tana yawan sadaka… kuma ba ta cutar da Maƙwabtanta.” Sai ya ce: “Tana cikin Aljanna.”

 

Manzon Allah ya ce: “Abubuwa hudu suna daga cikin sa’ada: mace tagari da gida yalwatacce da Maƙwabci nagari da abin hawa mai lafiya. Kuma abubuwa hudu suna cikin shakawa (tabewa da rashin sa’a): mugun Maƙwabci da muguwar mace da mugun abin hawa da kuntataccen gida.”

 

Yana daga cikin Haƙƙoƙin Maƙwabtaka a kyautata masa ta kowanne hali, kamar aika masa da abin da ka dafa, bashi shawarwari da za su amfane shi, a kansa ko iyalansa, ko 'ya'yansa, tsawatarwa 'ya'yansa a kan abin da aka ga zai cuce su, domin kyautatawa Maƙwabci yana kai mutum zuwa Aljanna.

 

 "wani mutum ya je wajen Manzon_Allah ya ce:"Ya Ma'aikin Allah shiryar da ni a bisa wani aiki, idan na tabbata a kansa zan shiga Aljanna, sai ya ce: "Ya Ma'aikin Allah ta ya ya zan san ni mai kyautatawa ne? Sai ya ce: Tambayi Maƙwabtanka idan suka ce kai mai kayutatawa ne to shi ne, amma idan suka ce kai ba mai kayuatatawa ba ne, to ba shi ba ne".

Wannan Hadisi yana nuna mana cewa idan mutum yana son ya san matsayin sa, to ya tambayi makotansa su ne shaidarsa a kan shi mai kyautatawa ne ko a'a, don haka wajibi ne mu zamo masu kyautata musu don mu samu kyakkyawar shaidar cewa mu masu kyautatawa ne, don in muka zamo masu kyautatawa, to mun kama hanyar zuwa Aljanna.

Ibn Umar ya kasance yana da Maƙwabci Bayahude, idan ya yanka akuya sai ya ce: ku kai wa Maƙwabcina Bayahude wannan (Abu Dawud da Tirmizi).

Har ila yau, kiyaye mutuncinsa (Maƙwabci) dana iyalinsa da dukiyarsa suna daga cikin kyautatawa, domin Annabi ya ce: "Mutum ya yi zina da mataye goma shi ya fi sauki a gare shi da yin zina da matar Maƙwabcinsa, mutum ya yi sata a gidaje goma shi ya fi sauki a gare shi da ya yi sata a gidan Maƙwabcinsa" (Ahmad).

Ya zo cikin sunani Abu Dawud daga Aba Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: "wani mutum ya zo wajen Ma'aikin Allah ya kawo karar Maƙwabcinsa, sai ya ce da shi, ka je ka yi hakuri, sai ya sake zuwa na biyu ko na uku, sai Manzon Alla ya ce: jeka ka debo kayanka ka zuba a kan hanya, sai ya je ya sanya duk lokacin da mutane suka zo wucewa sai suka tambaye shi bisa halin da yake ciki, sai ya basu labarin irin cutar da Maƙwabcinsa yake yi masa Sai suka rinka la'antar Maƙwabcin, sai Maƙwabcin ya zo gare shi ya ce: ya dan uwana mayar da kayanka gidanka ba za ka kara ganin wani abu na rashin kyautatawa ba daga gare ni har abada".

Ya bayin Allah! “Lallai ne Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta (hakkinsa), kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci, Yana yi muku wa’azi tsammaninku za ku yi tunani.” Don haka ku tuna Allah Mai girma da daukaka, sai Ya tuna da ku, kuma ku gode maSa a bisa ni’imominSa, sai Ya kara muku. Kuma ambaton Allah ne mafi girma. Kuma Allah Yana sanin abin da kuke aikatawa.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments