Na Haɗu Da Budurwa A Facebook, Tana So Na, Ina Son Ta, A Ba Ni Shawara

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Warahmatullah wabarakatuhu. Dafatan malam da iyalan malam suna lpa, Allah ya sa haka Amin summa Amin. Don Allah malam a yi ta haƙuri da mu. Malam ga tambayata gareka:

    Malam Allah yahada ni da wata yarinya a Facebook, to malam tace tana sona kuma nima inasonta hartakai munhadu munga juna. Yanzu malan don Allah at emaka man da shawara yadda za mu yi lbr da ita na soyayya wanda musulunci ya yarda da shi, da kuma hanyoyin da zan bi domin in ga taƙara sona, ni bantaba soyayyaba malam sai a kanta. Don Allah ayiman wannan temako na gode Allah yaƙara bada ilimi mai albarka

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Wa Alaikum Assalam Wa Ramatullahi Wa Barkatuhu:-

    Zaka sami wani da ka sani a wannan Garin da yarinya take, ya yi maka Binciken Dabi'arta da ta Iyayenta. Sabida ba a Aure sai Da Bincike. Duk Auren da aka yi babu Bincike Akwai Matsala.

     

     Daga nan kuma sai ka tura Iyayenka bayan ka Amintu da Tarbiyyarta da Ta Yan Gidansu. kai ma Kuma Ka Basu dama Su zo Garinku su yi Bincike akanka. Addinin ka da Kuma Yaya dabi'unka suke? Ya Kamata Mutane suke ganewa. Akwai Banbanci Tsakanin addini da kuma Dabi'a ko in ce da halayya ko kuma Ince yadda ka Iya Mu'amula. Wani Namijin yana da Addini, Amma bai Iya Mu'amulantar Mutane ba. Idan ya zo Neman Auren Diyarki ba za ku gane hakan ba. Sabida Nema ya zo yi. Zai boye duk wani Halayyar sa Maras kyau, ya Bayyana Kyawawan. Da zarar an yi Aure, sai Abubuwa su Chanja su Rikirkice. Sai ya zama kamar ba Wanda Kuka sani ba.

     Shi ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihin Wasallam Ya ce DUK WANDA YA ZO NEMAN AUREN DIYARKU, IDAN KUN GAMSU DA DABI'UNSA DA ADDININSA, SAI KU AURAR MASA. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihin Wasallam Ya ce a Bincika Dabi'u. Domin Nagartacciyar Dabi'ah ce take zaunar da Aure. Akasin Hakan Kuma yana Lalata Aure. Sabida haka kai ma ka ba su dama su Bincikeka Daidai Gwargwadon yadda za su Iya gamsuwa da kai su Baka Aure.

    Allah shi ne Masani.

    Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    ************************************** 

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.