Ticker

6/recent/ticker-posts

A Cikin Azumi

 Jiya da yamma wuraren ƙarfe biyar na wuce wajen wani gida sai na ga wani tanki a sama ya cika yanata zubar da ruwa a ƙasa. 

Duk da ina azumi sai na ga kamar al'mubazzaranci ne a bar ruwa suna zuba ga banza. Shi ne na je na ɗan tara bakina 🙄🙄🙄, kun san wani abu? Ba'a wuce minti ɗaya ba duk ruwan ya jiƙa ni. Ashe su ma ba yanda suka iya ne shi ya sa suka ƙyale yake ta zuba. 

Sai na tafi kawai.

A Cikin Azumi

Post a Comment

0 Comments