Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 12)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  12)

Baban Manar Alƙasim

Sau da dama samari sukan ƙi yin aure bisa wasu 'yan dalilai da suke ganin cewa hujjoji ne masu ƙarfi a wurinsu na yin hakan, za ka ga 'yammata da dama a gari suna tafiya daga nan zuwa can, ba wai ba sa son yin aure ne ba, samarin ne suka ƙi motsawa, abin haushi kuma wannan matattatar ta mu ta hana mace ta nuna wa namiji kai tsaye aurensa take so ta yi, kamar yadda shi din in ya ga wace yake so zai iya nema, to ya budurwa ko bazawara za ta yi? Na farko dai sai an ce ana son ta, na biyu kuma aure ba a hannunta yake ba bare ta ce "Zan yi aure kafin lokaci kaza" sai in ku samari kun motsa, galibi dalilan da matasa suka fi kafawa a kansu su ne:

1) Tsoron irin kudaden da mutum yake kashewa kafin maganar ta kai ga daura aure, ko kuma wadan da zai kashe bayan haka, ko tsakankanin daura auren akwai su da dama, in saurayi ya ga ko na karyawa da ƙyar yake samuwa zai yi wahala ya yi tunanin auren wuri kuma, amma sau da yawa wanda bai kai ka ƙarfinka ba yakan nema kuma ya yi, har ma ya sanya maka abinci.

2) Sai zancen kammala karatu, wani lolacin budurwar ake jira, wani sa'in kuma saurayin ne, wani tun farko yakan sanya wa kansa cewa ba zai yi aure ba sai ya kammala karatunsa, Diploma, Degree ko NCE, wannan ba wai don riƙon takardar a hannunsa ne ba, a'a, ya riga ya gama lissafin cewa in dai yana da takarda kaza, kenan zai sami aiki iri kaza, wanda za a ba shi albashin kaza a wata, sakamakon haka ba zai yi aure ba sai ya kammala wannan karatun.

3) Sau da yawa ma babu wani dalili sai tsabar boko kawai, inda wasu za su sanya wa ƙanninsu ko 'ya'yansu cewa ba wace za ta yi aure sai ta gama sakandare, ko sai ya gama digirinsa na farko, irin waɗannan dokokin su ma sukan kawo jinkirin aure, wani wurin ma hakan ya riga ya zama al'ada, yadda mai ƙasa da shekara 30 ya san bai isa aure ba, don haka ko nema ba zai yi ba, koda kuwa yana da kudin da zai yi, yana jiran sai shekarunsa sun kai yadda zai fara, amma fa zai iya danne 'ya'yan jama'a.

4) Rashin aikin yi ko kama sayar babban dalili ne da samari suke fakewa da shi wurin win neman auren, wannan kuwa ko shari'a ta amince da shi, don kuwa ta ce: Wanda zai iya daukar nauyin aure to ya yi. Kenan wanda ba zai iya ba bai zama wajibi ba kenan ya nema, don umurnin ga wanda zai iya ne, ba wai kuma mutum ya noƙe ya ƙi motsi ba, hakan zai iya haifar da matsaloli, na taba ganin wata yarinya da ciki, sai aka ce wani arne ne ma ya yi ma ta, na ce wannan za ta bar iyaye da takaici, ita kuma kasuwarta ta fadi.

To jinkirin aure zuwa shekaru da dama, kamar 30 ko 40 in dai babu matsaloli ai abu ne mai sauƙi, sai dai a daidai wannan lokacin wutar sha'awar namiji ta ya kusanci jinsin mace take matuƙar balbala da habaƙa a zuciyarsa, ta yadda indai ba ya ma'amalla da mata ko rigar nono ya gani a kasuwa ana sayarwa sai zuciyarsa ta kada, to bare kuma ya shiga matsatsi a inda dole sai an yi gogayya, irin wannan matsa wa kai na jinkirin aure shi yake jefa samari da 'yammata cikin halin ni 'yasu, har wanda tsautsayi ya fada wa diyarsa ya tashi ba nauyi. Sakaci da wannan masifa yake jefa samari cikin bala'in soyayya da matan banza, har ka ga an lalace, kamar yadda wani ya zo min cikin damuwa, kai da ganinsa ka san mai sukuni ne, don shaddar da take jikinsa ban taba sanya irinta ba, ya ce min shi sana'arsa sayar da gwala-gwalai ce, kuma tsakani da Allah yana samun kudin da bai taba tsammani ba, sai dai matan wasu ne yake bi su ba shi maƙudan kudi, yanzu ba zai iya lissafa wadan da ya yi lalata da su ba, kuma ya ce wallahi ya sani duk matan aure ne, alaƙarsa da wata take janyo wata. Abin mamaki yana fadi yana kuka, yana neman mafita, ya tambaye ni ko Allah zai yi masa gafara?

Na tambaye shi ko yana da mata? Ya ce bai taba yin aure ba, na ce to ya je likita ya gwada shi, in lafiyarsa lau, ya canja sana'arsa gaba daya, ya bar kasuwar kwata-kwata, ya fara karatun addini, ya fara azumin tadauwa'i da salloli a kan lokaci kuma cikin jam'i, ya yawaita yin istigfari, ya riƙa yin nadamar abin da ya yi a baya, in zuciyarsa ta tsarkaka ya ji lallai ba zai sake kusantar wata mace ba in ba matarsa ba, to don Allah ya tuntube ni don mu yi tunanin yadda za a yi kuma. Haƙiƙa akwai sauran imani a zuciyarsa, ba don haka ba ci gaba zai yi da holewa da matan jama'a ko 'ya'yansu har sai mutuwa ta kwashi kafarsa, matsalar jinkirin aure kenan, wata mata ma ta same ni bayan wata lacca da na ƙaddamar a wani babban masallaci take ce min "Malam matar da ta yi ta holewa da wanda za ta aura, sai ya zama sun yi auren ba tare da yin istibira'i ba, yanzu ga su da 'ya'ya manya, suna ma jami'o'i, ya matsayin aurensu? Kuma waɗannan 'ya'yan shegu ne ko suna da uba? Koda yake ta ce ba ita ba ce amma da ka gan ta a rikice take, shi ya sa in an dubi fa'idar jinkirin aure, yana da matuƙar kyau kuma a dubi illarsa sai a kwatanta. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  12)

Post a Comment

0 Comments