Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar AlÆ™asim ya rubuta
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 09)
Baban Manar Alƙasim
Abubuwan da suke gina soyayya ta ƙwarai kamar
yadda muka fada guda uku ne:- 1) Huduwar ginin jiki, ta yadda uba zai gina
yaronsa har ya tabbatar da cewa yana da ƙarfin da zai
iya daukar nauyin kansa da na waninsa nan gaba, zai iya neman na kansa ba tare
da ya tsaya sai wani ya ba shi ba, zai iya tsayawa a inda Allah SW ya ajiye
shi, ba zai riƙa kallon wasu ya sanya kansa dole sai ya yi irin
abin da suke yi a gidajensu ba, ya gamsu da cewa shi fa namiji ne, kuma an yi
shi ne masamman don ya bayar, yanzu ya zama dole ya nema din don ya miƙa.
In ya zama namiji yana buƙatar wannan
tarbiyyar a waje don ya zama kamar sauran maza, mace kam sai dai a cikin gida
tare da uwa ta gari, yadda za ta saba da aikin cikin gida tun tana ƙarama, koda
kuwa mahaifanta masu hali ne, dole ta iya tsaftace daki da bandaki, ta saba da
wanki da wanke-wanke, har ya zama ma ta jiki, yadda za a cire ma ta kasalar
hidimar miji da tsagina-gini, a koyar da ita cewa sirrin zaman aure yana kan
hidimar miji ne da kauce wa gasa da shi, sau da yawa in mutum ya saurari
uwayemmu zai ji suna cewa zaman aure shi ne "Yi na yi, bari na bari"
sai kuma gudun ƙiwa (ƙyuya) waɗannan abubuwa
ba za su taba samuwa ba sai uwaye sun gina 'ya'yayensu ta hanyar da za su iya
musayar ƙauna a tsakaninsu.
2) Sai haduwa ta hanyar mu'amalla da iya
zamantakewa, yara sukan fara koyon wannan ne daga mahaifansu, in mahaifan ba su
da kyakkyawar mu'amalla ga junansu to za su zama makaranta, dole uwa ta ba
diyarta kyakkyawar tarbiyyar da za ta iya zama da miji ta hanyar yadda take
mu'amalantar na ta mijin, haka uban zai ba wa na sa dan ta hanyar yadda yake
zaune da uwarsu, kenan kafin yara su fara kwafo dabi'un waje, sai sun ƙoshi da na
cikin gida tukun, sai uwaye su kula da abokai, ƙawaye, maƙwabta,
matattara, da makaranta, don waÉ—annan suna gyarawa kamar yadda suke batawa.
3) Haduwar manufa ga kowani yaro ko yarinya don
fuskantar hadaddiyar soyayya, dole su sani cewa aure fa rayuwa ce ta har abada
wace ba a fatar rabuwa, sai a fara duba É“angaren addini sama da komai, domin komai lalacewar mutum
ya san akwai Allah, masamman lokacin da ya sami kansa a wani runtsi, to bare
kuma aure wanda ba zama ne na rabin wuni kamar aikin gwamtati ba, zama ne na ba
dare ba rana har sai ta Allah ta kasance, Hausawa kuwa suna cewa "Zo mu
zauna, zo mu saba" dole kowanne cikinsu ya san cewa aure fa ibada ne, abin
da yake yi ga masoyinsa ba don shi yake yi ba don Allah yake yi, in ya zama
yana yi dominsa zai rabu da shi idan ya saba masa, in kuwa yana yi don Allah
ne, to ko ya saba masa yana tare da shi, don wanda yake yi dominsa yana ganin
abin da yake yi kuma yana farin ciki.
Da wannan 'yar shimfidar za mu fahimci duk wasu ƙarairayi da ake
yi gabanin aure na zaman zance ko na hira a waya ko danna-dannar hanyoyin
sadarwa kan cewa "Wallahi ina bala'in son ki da ƙaunarki, in ba
ki ba zan iya rayuwa ba, ba zan ko iya cin abinci ba, muryarki ita ce abinci
na, ganinki shi ne ruwan shana, sadurmu dake ita ce rayuwata, ni ko zagina kika
yi dadi zan ji" wace ta yarda da wannan laffuzan alhali ba ta ko shiga
gidan mijin ba ta yaudari kanta, matakin farko ta tambayi duk wata matar aure
ta ji, za ta iske cewa ita ma ta ji sama da haka, kuma ta gasgata, amma da ta
shigo gidansa ba haka ta sami zancen ba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.