WANNE AIBU NE WANDA BA'ASAN SAMUNSU A DABBAR LAYYA?

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    wanne aibu ne wanda ba'asan samunsu a dabbar layya?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Malamai sun yi ittifaƙi akan wadannan aibuka:-

    - Makanta, bayyananniya.

    -Rashin lafiya bayyananne, kamar zazzaɓi wanda yake hanata ci kosha ko kuzarin jiki wanda kana ganin dabba za ka gane batada lafia. ko rauni wanda yakeda tasiri ga namanta, ko raunin dayake babba wanda yakeda tasiri alafiyarta.

    - Gurguntaka shi ne rauni akafa ko karaya wanda yake hana dabba lafiyayyar tafiya.

    - Yamushashshiya bushashshiya wacce batada karfi batada maiko, saboda abunda yatabbata acikin muwadda lokacinda aka tamabayi Annabi sallallahu Alaihi wasallam wadanne dabbobine za'a nisanta wajan yin layya dasu? ( Sai ya yi Nuni da hannunsa ya ce huɗu ne,, Wacce take da matsala akafarta ba ta tafiya normal, da mai ido ɗaya wanda yabayyana, damara lafiyarda rashin lafiyar yabayyana, dawacce take ramammiya mara nama)

    Imamu malik yaruwaitoshi acikin muwadda daka hadisin bara'u bin azib.

    Awata ruwayar datazo acikin sunan daka bara'u bin Azib yardar Allah takara tabbata agareshi ya ce: ( Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yamike acikinmu ya ce dabbobi huɗu basa halatta yin layya dasu.

    Malamai sun yi saɓani akan dabba mai yankakken kunne komai yankakkiyar jela, magana ingantacciya yahalatta yin layya da ita, domin naman kunne ko jela baya tauye naman dabba kuma dabba ba ta cutuwa darashinsa, ita ce maganar Abdullahi dan Umar da ibnu musayyeeb da sauransu.

    Ya halatta yin layya da ragonda aka dandakeshi, Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya yi layya da raguna manya manya danda ƙaƙƙu, saboda naman layyar yafi dadi, shi ne maganar jamhurdin malamai, ibnu ƙudama ya ce: Bamusan wani saɓani akaiba.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.