𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀��𝐀❓
Assalamu Alaikum. Mal Khamis da
fatan ka tashi lafiya. Allah ya saka da alkhairi bisa ga gudummawar da kake
bayarwa a wannan group mai albarka. Muna karuwa sosai. Amma ina da ƙorafina a
wannan group nakan turo tambaya a wannan group mai albarka amma bana samu amsa.
Ko me ya sa haka?
Nagode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Walaikum sallam warahmatahi
wabarkatahu
To yar'uwa Kiyi haƙuri duk wanda
yaga/taga ba Amsa tambayarta ba to Bai cika ka'idojin group ɗin bane.
Inhar Allah ya sa kin cika ƙa'idojinda
muka gindaya a cikin group kuma kin jiramu har muka samu lokaci toh In shã
Allahu komai jimawa zakiga anbaki Amsa.
Dalilanda ke kawo jinkirin Amsa
tambayar suna da yawa Daga cikinsu shi ne: AJIZANCI NA ƊAN ADAM wato kamar
mantuwa gajiyawa da sauransu. Da kuma YAWAITAR SAƘONNIN MUTANE ta yadda kafin
ka kai ga buɗe sakon wasu saƙonnin sun sake shigowa, domin dazarar an buɗe
sakon mutum idan ba a san amsarba nan take ana cewa ba a san amsarba Idan kuma
fahimtar tambayarne ba a yi ba Ana sake neman karin bayani.
▪️Kasancewar tambayoyi sun yi mana
yawa bamu amsa tambayar da muka amsa Irinta a cikin group.
▪️ Bamu amsa tambaya da ba tada
muhimmanci kamar fassara suna ko fassara mafarki da sauransu.
▪️A facebook bamu Amsa Tambaya ta
comments sai ta private chat (inbox).
▪️ A WhatsApp Bamu Amsa Tambaya
ta voice ko ta voice call ko video call.
▪️ Bamu Amsa Tambaya ta kira
(phone call) Ko ta text message ko ta e-mail.
Ku sani cewa, gaskiya ba za mu
iya Amsar Tambayar kowa da kowa ba, saboda Tambayoyin suna da yawa sosai. a
kowace rana tambayoyi sun kan iya kai 50 ko sama da haka, To kunga ba za mu iya
Amsar su duka ba. Saboda haka duk wanda bai samu Amsar tambayarsa ba, to ya yi haƙuri.
Wannan shi ne bayani game da
korafinku a takaice.
Daga karshe, Ku taya mu Yaɗa
wadannan Fatawoyin da muke turawa a wannan Group, domin Yaɗa ilimi yana daga
cikin Abubuwan da suke kusanta bawa ga Mahalicci. Amma Kuji tsoron ALLAH, kada
ku kwafa (copy) ku goge wani abu daga ciki, ko da Links ne. Ga wanda yaga Gyara
Ku sanar damu.
Yazo a hadisi cewa duk wanda ya
yi nuni zuwa ga Aikin Alheri, Ladansa kamar wanda ya Aikata Alherin ne. Manzon
Allah ﷺ Ya ce: Na rantse da Allah, Allah Ya shiryar da wani a dalilinka, yafi
maka Alkairi sama da a baka jajayen raƙuma.
"Ku Tunatar Domin Tunatarwa
Tana Amfanar Mumini"
[Ƙur'an/51:55]
ALLAH Ya Kara mana ilimi Mai
Amfani, ya sa mu Amfana da Ababen da muke Rubutawa da kuma karantawa, ALLAH
Yarda damu da Ayyukan mu. Allah ya sa faɗakarwan nan ta Amfani Al'ummah ga baki
ɗaya. ALLAH Ya sakawa kowa da mafificin Alkhairi. Ya haɗa fuskokinmu a cikin
Aljannah.
Ameen Ya Hayyu Ya Ƙayyum🤲🏻
Daga Admin:
𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟
+2347042085123
Zauren Tambaya Da Amsa Abisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.