Ticker

6/recent/ticker-posts

Taƙaitaccen Bayani A Kan Zikiri

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. lna kwana malam barka da warhaka Malam don Allah haske nake son a kara min akan Azkar da abubuwan da ake faɗa yayin Azkar, na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, to ita dai kalmar Azkar kalmace ta Larabci, kuma jam'i ne na kalmar Zikir, wadda ke da ma'anar ambato, ko tunawa dasauransu. Amma a Musulunci idan aka ce Azkar (أذكار) ana nufin zikirori da suka ƙunshi karatun Alƙu'ani da addu'o'i da salatin Annabi ﷺ da istigfári da kuma abin da ya jiɓanci hakan.

Mafificin zikiri shi ne karatun Alƙu'ani mai girma, duk wani zikiri da mutum zai yi yana bayan karatun Alƙur'ani mai girma ne. Kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya yi umurni da yin zikiri a wurare da dama a cikin Alƙur'ani mai girma daga ciki sun haɗa da inda Allah yake cewa:

1- "Ya ku waɗanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa".

Suratul Ahzáb: 41.

2- "Ku ambace ni zan ambace ku, kuma ku gode mini kada ku kafirce min".

Suratul Baƙara: 152.

3- "Ku roƙi gafarar Ubangijinku, sannan ku tuba zuwa gare shi".

Suratu Huud: 3.

4- "Ku roƙi gafarar Allah, lallai Allah mai gafara ne mai rahama".

Suratul Baƙara: 199.

Ku roƙi gafara a nan ana nufin ku yi istigfári. Daga cikin zikirori akwai zikirin Safiya da Yammaci, da zikirin kwanciya barci da na tashi daga barci, da na shiga banɗaki da na fita, da zikirin shiga gida da na fita, da zikirin hawa ababen hawa, sannan akwai zikirorin da ake yi bayan an idar da sallar Farillah, don samun zikirorin da ake yi bayan an idar da sallar farillah sai a duba Amsoshin Tambayoyinku na 144, sai kuma a duba amsar tambaya ta 123 don samun zikirin da ake yi idan mutum ya shiga matsananciyar damuwa ko baƙin ciki.

A tambaya ta 003 kuma za a sami addu'ar da Manzon Allah ﷺ kan yi wa mamaci. Sai kuma a duba tambaya ta 010 don samun addu'ar Istikhara, tambaya ta 023 za a sami addu'ar neman tsari da ake yi wa ƙananan yara, idan aka dubi tamabaya ta 047 kuma za a sami addu'o'in warware sihiri, idan aka duba tamabaya ta 054 za a sami addu'ar da ake karantawa idan wani ɓangare na jikin mutum yana ciwo.

Duka waɗannan a taƙaice ne, ki tintuɓi ingantattun malaman Sunnah don samun zikirori ingantattu na Manzon Allah ﷺ. Kuma ki nemi littafin GARKUWAR MUSULMI, wato (HISNUL MUSLIM), shi ma za ki fa'idantu ba ɗan kaɗan ba, saboda nan ba zai yiwu a iya kawo maki zikirorin nan yadda suka dace ba, sai dai kawai a yi taɓa ka lashe a nan.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments