SHIN IN AMARYA TA KAURACEWA MIJINTA, ZAI IYA ZUWA GA UWARGIDA?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Dan Allah inada tambaya mutum ne matansa biyu so ranar girkin amaryan sai suka yi faɗa taki sauraransa, kuma yana cikin bukatuwa da ita Sai kawai yazo wajen uwargidan yasamu nutsuwa shin dan Allah meye hukuncin hakan.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu.

    Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

    Yayi daidai wallahi, babu komai, ya yi daidai, ko lahira baki binsa bashin zance. Domin kuwa babu inda aka ce mace ta ƙauracewa mijin ta don sun samu saɓani. Miji ne aka baiwa wannan damar, shi ma ba haka nan kawai don saɓani ko son rai ba, sai don ladabtarwa. Allah ya ce:

    .. وَٱلَّـٰتِی تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَٱهۡجُرُوهُنَّ فِی ٱلۡمَضَاجِعِ وَٱضۡرِبُوهُنَّۖ فَإِنۡ أَطَعۡنَكُمۡ فَلَا تَبۡغُوا۟ عَلَیۡهِنَّ سَبِیلًاۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِیࣰّا كَبِیرࣰا

    [Surah An-Nisa' 34]

    Wannan aya ta bai wa maza damar ɗaukar matakin wa'azi, ƙaurace wa mata daga barin shimfiɗar ta (jima'i) da duka. Duk waɗannan matakan don ladabtarwa ne, ba don sun samu saɓani ba.

    Saɓani tsakanin ma'aurata dole ne ya auku, amma yana da kyau idan ya faru, mu kuma samu mataki da hanya mafi dacewa da wacce zamu ɗauka ba tare da ta ci karo da ta shari'a ba, kuma ba ta zalunci abokin saɓani ba.

    WALLAHU TA'AALA A'ALAM

     Amsawa

     Malam Aliyu Abubakar Masanawa

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.