Ticker

6/recent/ticker-posts

HUKUNCIN YIN MU'AMALA DA MATAR DA BA MUHARRAMINKA BA

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aslm alkm, ina yima malam fatan alheri da karin ilmi mai amfani. a baya gaisawa ta haɗani da wata budurwa, to sai kauna ta shiga tsakani, dana fahimci akwai wanda iyayenta sukeso ta aura saina ba ta hakuri saboda girman iyaye, to yanzu nida ita duk munyi aure.  abin da ke damuna duk  abin da ya faru a gidana sai tazo kuma koba wata hidima wajena tana aiko man da kuɗi. shin ya matsayin wannan kuɗin aguna?.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Bai halatta ka cigaba da wata mu'amala da wannan yarinyar ba, tunda yanzu matar wani ce, Kuma kai ba Muharraminta bane.

Manzon Allah ﷺ Ya ce: "KU KAME DAGA MATAYEN MUTANE, SAI MUTANE SU KAME DAGA MATAYENKU".

Don haka nake jan hankalinka cewa kaji tsoron Allah ka yanke wannan alaƙar tunda zata iya zama sanadiyyar rabuwar aurenta watarana. Duk sanda mijinta ya fahimci akwai wata alaƙah irin wannan atsakaninka da matarsa, zai iya daukar matakin shari'a akanka, ita kuma zai iya sakinta. Kaga ta dalilinka sharri ya sameta.

Kuma Manzon Allah ﷺ ya yi gargadi mai zafi akan duk wanda ya yi sanadiyyar mace ta kangare wa mijinta. Ya ce "BAYA TARE DAMU DUK WANDA YA LALATA MACE GA MIJINTA, KO YA LALATA BAWA GA UBANGIDANSA".

Abu Dawud da Nisa'iy da Ibnu Hibban suka ruwaitoshi.

Watakila za ka ce ai kai ba zugata kakeyi ta bijire wa mijinta ba. Amma kar ka manta cewar hankalin mace ba irin na namiji bane. Zata iya yiwa mijinta kowanne irin laifi tare da gadarar cewar ai idan ya saketa zata fito ta aureka.

Shi kuwa kyautar da take yi maka, idan kudinta ne na halal to babu komai. Amma idan satowa takeyi daga dukiyar mijinta, to kaima kasan  abin da kaci (HARAM NE).

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

 

Post a Comment

0 Comments