Neman taimakon wanin ALLAH a abinda ALLAH kaɗai keda iko da wannan abin, yana kaiwa ga shirka.
Lallai ALLAH TA'ALAH shike da iko da saukar da ruwan sama, ko ɗaukewarsa.
Shi keda iko da saukar da zafi ko sanyi.
Shi keda iko da yayewar masifa ko saukar da ita.
Shi keda iko da yayewar talauci ko saukar dashi.
Shi keda iko da cusa ilimi a cikin ƙirjin abinda ya halitta ko toshe kirjinsa ya kasa fahimtar komai.
Shi keda iko da azurtawa ko talautawa, shi ya sa idan yaso sai ya talauta musulmi ya azurta kafiri, kuma babu wanda ya isa ya ce danme.
Shi keda iko da ba da lafiya ko sakko da rashin lafiya ga abinda ya halitta.
Lallai mu sani a cikin waɗannan abubuwa babu wanda ya isa dasu sai ALLAH, shi kaɗai, babu wanda yake da iko dasu, idan ka roƙi waninsa su, to ka rasa musuluncinka.
ko da Annabi ne ko mala'ika ko wani salihin bawa mai tsoron ALLAH.
Kaɗai ana iya zuwa ga Annabi ko wani salihin bawa ace ka roƙa mana ALLAH ya yaye mana talauci, ko ya saukar mana da ruwan sama, ko ya bamu dukiya mai albarka, ko ya yaye mana rashin lafiyar dake damunmu da sauransu.
Idan wannan Annabi ya yi roƙo a gurin ALLAH, idan ALLAH yaso sai ya amsa masa nan take ya kuma yaye wannan damuwa, idan kuma yaso sai ya jinkirta sai zuwa wani lokaci, wannan ganin damarsa ce.
Lallai ALLAH shi ne wanda ya saukar da rashin lafiya, sai ya ce a nemi magani amma hakan baya nufin shi likitan shi ne zai baka lafiya, shima likitan idan ya baka magani daga ƙarshe zaice ALLAH ya baka lafiya, kenan lafiyar ba a hannunsa take ba tana hannun ALLAH.
Haka zalika, neman albarkar wani abin halitta shima baya daga cikin koyarwar Annabi {s.a.w} ko sahabbansa ko wanin haka.
Domin ita albarka ALLAH kaɗai ke saukar da ita, babu mai iko da ita sai ALLAH, shiyasa ko abu ka siya sai kaji ana cewa ALLAH yasanya alkhairi, ma'ana ALLAH ya sa albarka.
Kamar yadda idan kayiwa wani babba abin kirki ko iyayenka za kaji suna cewa ALLAH ya yi maka albarka, hakan na nuni da cewa ALLAH kaɗai ke saukar da albarka ga bayinsa, ba wanin ALLAH ba.
Akwai masu cewa dan albarkacin Annabi {s.a.w} wannan baya daga cikin koyarwasa, kuma ba a taɓa samu wani sahabi ko tabi'i ya faɗi hakan ba, sannan kuma dukkan aiki baya zama aiki sai aikin da aka koyoshi daga sahabbansa {s.a.w}, domin sune madubin dubawarmu.
Duk da cewa ALLAH bai taɓa halittar wani abin halitta mai girman daraja kamarsa Annabi {s.a.w} ba, amma ba a cewa dan albarkacin Annabi kamin abu kaza da kaza ko albarkacin wani mala'ika, wannan baida asali a cikin littafin ALLAH, ko ayyukan sahabbai, kuma ba'ayi agabansa ba ya yi shiru.
Sai dai ana iya cewa dan albarkacin Alƙur'ani, mene ne dalili kuwa, saboda shi Alƙur'ani ba halitta bace, zancen ALLAH ne, shiyasa aka halatta rantsuwa da Alƙur'ani kamar yadda ake rantsuwa da ALLAH.
Amma rantsuwa da wani Annabin ALLAH ko mala'ika yana kai mai rantsuwar ga shirka, ALLAH ka karemu.
Amma a babin neman taimako ana iya neman taimakon wanin ALLAH kaɗai ne a mahallin da yake shi yana da ikon ya taimaka.
Kamar yadda sunna ta koyar, kaje gurin ɗan uwanka ka nemi ya taimakeka da wasu kuɗi ko abinci ko wanin haka, wannan kuwa Alƙur'ani da hadisai sun tabbatar da haka, domin su ababene da mutum ɗan uwanka zai iya taimaka maka dasu,
Amma duk abinda yake ALLAH kaɗai yake da iko dashi to haramun ne a nemi taimakon wannan abin agurin wanin ALLAH.
Don haka ba a neman taimakon wanin ALLAH wani abu wanda ALLAH kaɗai keda iko dashi, kamar yadda ba a neman albarka gurin wanin ALLAH, sai dai ana iya cewa ka yi mana addu'a domin kusancinka da ALLAH, yafi namu, kamar yadda iyaye suke addu'a wa yaransu ALLAH ya yi musu albarka da sauransu.
ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.