Namiji Keda Haƙƙin Kiran Matarsa Ga Shin Fiɗa Ko Kuwa Mace Ma Nada Haƙƙi

    Annabi {s.a.w} Ya ce: Idan mutum ya kira matarsa zuwa ga shinfiɗarsa, sai taƙi, mala'iku za su la'ance har sai mijinta ya daina fushi da ita.

     A wata rayuwar kuma, idan da daddare ne har sai gari ya waye.

    Wannan hadisi yana magana ne akan mata, domin su mata sunada makirci sosai, sannan kuma namiji yafi saurin bayyana sha'awarsa ga mace, sama da ita mace tana iya ɓoye tata ko da kuwa tana da buƙata.

     Sai dai kuma ko wanne daga cikinsu matar ko miji kowa nada haƙƙi akan kowa.

     Mace zata iya neman biyan buƙatarta ga mijinta, kuma wajibi ne ya biya mata mutuƙar lafiyarsa ƙalau babu wani dalili na larura mai ƙarfi da zai hana.

     Kamar yadda shima namiji zai iya zuwa wa matarsa da bukatarsa kuma itama dole ta amsa mutuƙar babu wani dalili na larura mai ƙarfi da zai hana.

     Amma wasu mazan suna tauye haƙƙin matansu ta wannan gaɓar, wanda hakan na zama zalunci a cikin zaman-takewa.

     Mutuƙar za ka tauye mata haƙƙinta, kuma a dalilin wannan haƙƙin ta shiga damuwa to kaima ka sani sai ALLAH ya ƙwata mata wannan haƙƙi nata a ranar alƙiyama.

     ALLAH baya barin haƙƙin wani akan wani komai ƙanƙantarsa, dan ba a ambata wani sakamako ba akan maza kamar yadda aka bayyana akan mata ba, hakan baya nufin ALLAH ba zai yi tambaya akan haƙƙin kowa ba.

     Indai matarka ta shiga damuwa a dalilinka na minti 1 akan haƙƙinta to ALLAH ba zai yafe maka wannan haƙƙi nata ba, har sai ta yafe maka tun anan duniya.

     Kamar yadda idan itama ta tauye maka haƙƙinka itama ALLAH ba zai yafe mata ba sai ta biyaka wannan haƙƙin naka a gaban ALLAH.

     Don haka mu sani lallai babu wani haƙƙi da miji zai tauyewa matarsa ko mace ta tauyewa mijinta face sai ALLAH ya yi sakayya a kansa komai ƙanƙantarsa.

    ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.

    ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.