Ticker

6/recent/ticker-posts

Kullum Sai Naji Sha'awar Mace, Menene Mafita?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Mallam Tambayata anan shi ne na kasance matashi yaro mai kimanin shekara 20 kuma ina da wata sha'awa sosai wacce idan ta tashi hankalina baya kwanciya, kuma ga yawan mafarki ina saduwa da mata kala kala kuma kusan kullum sai nayi sha'awar mace ???

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam To duk wanda yake son ya kubuta daga shaukin mata da kuma da kallon haram, to ya nemi taimakon Allah, sannan ya dawwama akan salloli guda biyar, domin ita sallah tana hana alfasha da mummunan aiki, sannan kuma kar ya manta da addu'a da Kankan da kai a lokutan amsar addu'a ga Allah maɗaukaki, (kamar lokacin sahur da tsakanin kiran sallah da ikama da cikin sujjada) ya dinga yawaita cewa:

يَا مُقَلِّبَ الْقُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ

Ya Muƙallibal ƙulub, sabbit ƙalbi ‘ala dinik.’

Ya mai jujjuya zukata ka tabbatar da ni akan addininka.

Ya kuma yi kokari wajan nisantar wuraren fitina ta hanyar canza su da halal mai tsarki, ya dinga tuna faɗin Annabi ﷺ cewa : (Duk wanda ya bar abu saboda Allah, to Allah zai canza masa da abin da ya fi shi alkairi).

Ibnu Mas'ud yana cewa : "Duk wanda wata mace ta burge shi, to ya tuna kazantarta (Fitsarinta da bahayarta) " saboda hakan zai sa ya shi ba ya sha'awarta.

Sannan ka yi kokari wajan yin azumin litini da alhamis, saboda yana rage sha'awa, ka kuma nisanci yawan cin kayan-marmari, saboda suna tada sha'awa, kuma mutukar mutum yana cin su, to ko ya yi azumin ba zai rage

masa sha'awa ba yadda ya kamata.

Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments