Kishi Rahama Ne Ko Azaba? // 35

     MASOMIN KISHI A MATATTARARMU

    Wasu lokutan mukan ga mace mai azabar kishi in aka duba mamanta ko 'yan uwanta ko gidan da ta fito sai a taras ba haka suke ba, to me ya haifar da wannan uban kishi haka? Da ma  abin da ake cewa in ana tsoron kishin "Ya mamanta take?" Ko "Ya 'yan uwanta suke?" In aka sami suna da irin wannan baÆ™in kishin sai ka ga mutum yana baya-baya, don bai tabbatar wa kansa mace daya zai aura ba. Ko ma ba haka ba galibin matsalolin da ake ambatowa anan mutum bai ma kai ga Æ™aro auren ba uwargida ta addabe shi, matsalar yau daban ta gobe daban.

    Bari mu yi ƙoƙarin raba abin kashi-kashi yadda za mu ji dadin yin bayani. Akan sami mace da mummunan kishi a dalilin:-

    1) TASOWARTA: Tun yaranta iyayen sun dan gaza wurin yi mata abubuwan da take buÆ™ata, ko dai da kuskure saboda rashin  abin da za su ba ta din, Æ™awayenta na manyan makarantu ita tana ta gwamnati, ko dukansu suna makaranta daya amma wannan za su zo makaranta da gasassar kaza ita za ta zo da gurguru ko dumamen tuwo miyar kuka, a hankali ta fara jin me ya sa uwayenta ba za su ba ta  abin da ake ba wancan ba?

    Ko ta ce me ya sa aka kawo ta wannan makarantar da ba a karatu sosai? Me ya sa ba za a kaita inda mafi yawan ƙawayenta suke karatu ba? Da zarar ta fara jin haushin wannan a dalilin yaranta to kishi ya fara shiga kenan, to bare kuma a ce dukansu yaran mutum guda ne amma wadannan an kai su makaranta mai tsada ita ba a kai ta ba. Ba za ta lura da dalilin da ya sa aka kai wadancan wancan makarantar ba, wace ya kamata ta taimaka sosai wurin magance matsalar uwar ce, yadda za ta kwantar wa yarinyar da hankali ta yi mata bayani har ta fahimta, in hakan bai samu ba to babbar matsala ta samu anan gaba. Don koda ta sami karatun za ta ce "Mu da ba a so mu samu Allah ya yi!"

    To bare kuma a ce 'ya'yan kishiya ne, Æ™ila Æ™aninta ko wanta Allah ya hore masa, 'yar uwarsa ta roÆ™i ya taimaka wa 'ya'yanta. Uban yaran dai taimakonsa aka yi, koda a irin makarantun sauran yaran za a saka su an dauke masa nauyinsu. To bare kuma a ce babbar makaranta ce wace ake biyan kudi sosai kafin yaro ya yi karatu. Zai ji dadi amma sauran yaransu za su fara tunanin to su mai zai hana a hada da su? In suka fara jin haushin hakan to  abin da ba a son ya faru ya fara ke nan daganan, domin a duk lokacin da suka ga wadancan sun saka kayan makarantar ransu zai baci.

    To bare kuma su ga nan da nan sun iya wani harshe da su ba su iya ba, ko sun iya wani karatu da ba su iya ba. Abin zai ci gaba a hankali- a hankali yadda za su ga ana ware su an fi fifita yaran wancan dakin da su, in suka fara tattauna hakan a tsakaninsu abin ya baci, taimakon da uwaye za su yi anan tun farko su hana faruwar hakan ta wurin nuna wannan fa ba wani abu ba ne, dama ce Allah SW ya ba uwar wadannan yaran, kuma ko ita ce ta samu haka za ta yi, a Æ™arshe alkhairinsu ne gaba daya tunda gidansu daya, ubansu daya, duk  abin da suka zama za su ce "Ai yayana ne" ko "Ƙanwata ce".

    In ba a iya maganin wannan matsalar a matakinnan ba har ya zama wa yarinya jiki, ta girma da wannan ginannar dabi'ar da ta taso da ita a gida nan duk  abin da ta gani zai yi mata tasiri tsakaninta da abikiyar zamanta tunda acikin irinsa ta taso, to bare kuma a ce ta girma tana ganin irin wadannan 'yan taÆ™addamomin tsakanin mahaifiyarta da kishiyarta. Yadda duk wani laifi uban ya kwaso zai sauke a kan mahaifiyarta, wani lokacin ma har ta shiga rigimar uwayen tana kare mahaifiyarta. Irin wannan ba rabuwa da ita zai yi ba, in ta yi aure ma yananan, za ta fara tunanin ba za ta bari a yi mata  abin da aka riÆ™a yi wa tsohuwarta ba.

    .

    To zai yuwu kuma yarinya ba ta sami ƙaunar da take buƙata ba ne a wurin mahaifan, ƙila mamanta ba ta a gidan a dalilin saki ko mutuwa, ko kuma tana wurin riƙo. Wannan babbar matsala ce domin yaro kan ga cewa ba a yi masa adalci ba, da a ce mamansa na gidan da ba za a yi masa irin wannan cin kashi ba, in ya fara wannan tunanin tabbas nan gaba kadan zai fara jin haushin wadanda yake ganin ana fifita su a kansa, kishi ya sami wurin da zai kurdado kenan, to in mace ce ko ta yi aure tananan tana tunano iri riƙon da aka yi mata, in wancan ta sami miji mai hali za ta fara ganin ita ba a bari ta auri mai kudi ba don mamanta ba ta a gidan, in kuma ita ce ta auri mai kudin za ta fara cewa "Wadanda ba a so din dai su Allah SW ya daukaka".

    .

    To bare kuma a ce an yi wariyar tabbas amma ita din ma da dalili, misali amaryar ta rasu amma 'yan uwanta masu kudi ne suna yi wa 'ya'yan 'yar uwansu komai, sai suka ga to ai wadancan uwarsu nanan don haka ba sai an yi musu ba. Ko kuma ba su ga dalilin da zai sa su yi wa 'ya'yan wancan ba. In dai wadancan suna ganin  abin da ke faruwa tabbas kishi ya shiga, in aka Æ™yale su kuma ko sun girma sun yi aure sai an sami tasirinsa a zamantakewarsu.

     

    Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.