7) HADUWA KO RABAWA: Wannan ma wani abu ne da mata suke kishi a kai. Akan sami wata ta daki ƙasa ta ce wa maigidan in dai ya nace sai ya ƙaro wata matar to ba dai a hada su a gida guda ba, ba za ta juri kullum in ta fito ta riƙa ganin tashi hankali ba. Wace ta san yarinya za a auro takan fake da cewa ba za ta yi kishi da sa'ar diyarta ba, don haka ta je can ta yi yarantanta a wani wuri. Na ga wace ta gaya wa mijin cikin sanyin murya da fahimta cewa ita fa mace ce mai zafin kishi, in har za ta ga wata matar a matsayin matar mijinta hankalinta zai tashi, gwara a kai ta nesa, ba ta ƙaunar ko abin arziƙi ya hada su bare na tsiya!
Irin wadannan matan akwai su da yawa, na ji da kunne na wata Balarabiya tana magana da wani dan jaridan BBC na harshen Larabci cewa ta kwashe shekaru da dama ba ta taba yin ido biyu da kishiyarta ba, kuma ba ta buƙatar Allah ya hada su. Al'adarsu daban, amma mu anan matattararmu ta Hausa, ban san yadda hakan za ta kasance ba, don in abin farin ciki irin su suna ko biki ko taron sauka ko tarewa a sabon gida bai hada su ba dole na baƙin ciki kamar rasuwa ko asarar wani abu zai hada su. Shekaru ta ce ta yi da mijin amma ba su taba hadua da kishiyar ba.
Da dan jaridan, wato Nuruddeen Zurgi, ya tambaye ta dalili sai ta ce "Ni kyakkyawar mace ce ta sosai ma kuwa, na san idan matarsa ta gan ni zaman lafiya kuma ta ƙare tsakaninta da maigidammu, ni ba son damuwa a rayuwata, shi ya sa kawai na ja gefe guda!" To rediyo ne bare mutum ya ce tabbas abin da take fadi gaskiya ne ita kyakkyawar ce. Mu dai anan Nigeria ko na ce a matattararmu mace na ƙin a hada ta da wata ba don tsoron ba ta wa kishiya ne rai ba, kanta kawai take ji. Ta dauki gidan a matsayin nata daga ita sai 'ya'yanta sannan za a kawo wata matar su zama su biyu yau miji yananan gobe yanacan?
An yi wata matar da ta ƙi yarda maigidan ya kama wa amaryarsa gidanta na daban, da farko ta fito masa ne a matsayin mai tausayi, tana ganin da a ce ya kashe kudinsa wajen kama wa amarya gida, ga sha'anin biki, ga kudin makarantar yara ba gwara ya gyara turakarsa kawai ya ƙara fadinsa ya mai da gidan tsarin mu hadu a falo ba? Abinka da wanda zai yi sabon aure sai ya dauka a matsayin ƙauna da tausayi, ashe abin da uwargidan take so ta cimmasa daban, so take amaryar ta zo da kayanta a saka a falo, ga ta da yara masu ƙiriniya. An yi auren amma ko wata hudu ba a yi ba an karairaya kujerun, ƙananan yaranta duk sun fitsare su, kusan duk kayan da aka yi wa amaryar sun canza sun koma wasu abubuwan daban.
Irin wannan nau'i na kishi ba kasafai maza ke iya gane shi ba, saboda sun riga sun saba da uwargida kuma sun san irintausayin da take da shi masamman wurin kula da gida, ko ba boka ba malam in har uwargidan za ta yi aiki da wannan damar dole amarya ta fito a matsayin mai kishi mara son zama lafiya, duk bayanin da za ta yi wanda zai nuna cewa uwargidan na cutar da ita gani muke yi kamar ita ce mai kishin, ba ta ƙaunar wata ta amfana da kayanta. Yarinyannan dai ba ta wuce wata shida ba uwargidan ta fitar da ita ƙarfi da yaji, ba abin da maigidan ya iya yi.
Zan tuna abubuwa biyu da suka taba faruwa ba zan manta da su ba. Zan kawo su ne don a dauki wani darasi a ciki, ba wanda ya san ko su waye bare a yi maganar an yada sirrinsu. Wata 'yar ƙasar Indonesia ce ke cewa in za ta yi aure a Nigeria ba za ta auri mai mata guda ba, ban san hujjarta ban kuma tambaya ba, sai dai ta ce dole maigidanta ya hada ta da kishiyarta a gida guda. Wannan ne nake ganin kamar sabon abu shi ya sa na tambayi dalili. Ta ce tana so ne ta kasa ta tsare, ba za ta yarda a riƙa cutarta ba, komai za a yi musu sai dai a riƙa yi musu tare. Kar a zo tana zato namiji na wajen nema musu abin da za su ci ashe yana gidan kishiyarta ne, ita da kiwo wata na can tana tatsar mata sa.
Wannan yarinya ce ba ta taba aure ba, ina da hujja in na ce ba ta san kan rayuwar ba ne, sai ta yi aure tukun. Ta biyu kuwa baturiya ce ƙila su haka yake a ƙasarsu Allah ne masani. Sai dai kuma bai wuce shekara biyu ba na yi arangama da wata matsalar irin wannan a ƙasata, inda uwargidar ta tsaya kai da fata ba za ta yarda maigidanta ya yi wa amaryarsa gidanta daban ba, na sha raba rigingimu inda matan ke cewa ba za su zauna da kishiya ba a gida guda ba, ga dalilannan an zayyano su a baya.
In ka ji mata ba sa son zama da kishiya da wahala ka tarar cewa gasa ba ta daga cikin abubuwan da suke hanawa. Na sha ganin ana hada gida amma a raba ban-daki da kici. Sau tari gasa ake tserewa ma. To in mata suka ce dole sai an hada su wuri guda me suke nufi? Wannan dai uwar mata ce, ta kwashe kusan shekara 20 tana tare da mijin, ta yi duk ƙoƙarin da za ta iya wurin ganin ta hana auren amma ya ƙi hanuwa, to a ganinka, mai karatu, me ya sa ta nace sai an hada ta gida daya da amaryar?
Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.