HUKUNCIN TARAYYA A KAN LAYYA

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    shin ya halatta mai layya da wanda yakeson yin walima su haɗu su sayi saniya ko raƙumi suyi layya?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله

    Ya Hallata tarayya akan saniya ko raƙumi, koda Wasu daka cikin Waɗanda aka yi taraiyyar dasu, su ba layya suka niyya taba, kawai suna San Samun namane don suyi Walima dashi, ko don suci, ko dan Sayarwa da sauransu.

    Nawawi Allah yajiƙansa da rahama  acikin Al-maj-mu'u (8/372) ya ce: Ya halatta Mutum bakwai su hadu akan raƙumi ko Saniya don yin layya, mutanen gida daya ne gaba dayansu, ko gidansu daban, Ko Nama sukeso kawai, Wanda ya niyyaci layya cikinsu ta Isar masa, layyar Bakance ce kota Nafila, Wannan shi ne mazhabar mu, Imamu Ahmad ya fada da jamhur din Malamai.

    Ibnu Ƙudama acikin Al-Mugni (13/363) ya ce: Raƙumi Ya Isarwa mutum bakwai, haka Saniya, wannan Shi ne Zancen mafi yawan Malamai, Wanda Suka hadu akansu mutanen gida daya ne, ko ba mutan gida daya bane, Layyar wajibi kota Nafila, Nama Wasunsu suke so, ko wanne daya daka cikinsu kasonsa ya isar masa, niyyar wani ba ta cutar dashi.

    Babu laifi kayi taryya da Abokanka ku bakwai kuyanka saniya, dakai Da wanda yanaso ya Samu nama ne dan ya yi walima, ko ya Sayar ko yaci.

    Shekarun da ake buƙata wajan layya da Saniya Shi ne shekara biyu, wacce ba ta kai hakaba bai halatta layya da itaba, koda tana da yawan Nama.

    Wallahu A'alamu.

     Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.