𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum Malam dafatan kowa lfy Malam Nice na sanya turare mai kamshi asaman
kayana tom danaje gidan kanin mamata sai yake min fada wai hakan bai dace ba
infita ina kamshin turare har jama'ar waje suji ina son karin bayani malam
Nagode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikum
Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu
To ‘yar’uwa
ya haramta ga mace Baliga ta sanya turare, ta fita unguwa, saboda faɗin Annabi ﷺ
“Duk matar da ta sanya turare, ta wuce ta wani majalisi, to ta zama mazinaciya,
kamar yadda Abu dawud ya rawaito.
A wani
hadisin kuma yana cewa: “Duk matar da ta sanya turare, kar ta halarci sallar
Isha tare da mu.
Daga Ubaidu
Yace : "Lallai Abu Hurairata, ya haɗu dawata mãta wacce ta sanya Turare,
Sai Yace Mata: Ina kikeson zuwa ne haka Baiwar Allah? Sai mãtar ta ce:
Masallaci zanje. Sai Ya ce: Saboda zaki Masallacin ne kika sanya Turare? Sai
mãtar tace eh, Sai Abu Hurairata Yace Lallai nãji Manzon Allah ﷺ Yace "Duk
mãtar da ta sanya turare tafita da nufin zuwa Masallaci, to Allah mai girma da
Ɗaukaka ba zai karbi sallarta ba har sai ta dawo ta yi wanka Irin wankanta na
Janaba."
{Ibn mãjah
ne ya ruwaito shi a cikin KITABUL FITAN babin Fitnatun Nisã'i (4002)
Malaman
Muslunci sun inganta hadisin, Sheik Nasurudden albany ya yi ta'aliƙi akan haka,
yakara dacewa"Idan har(sanya turare saboda) zuwa Masallaci ya zama Harãmun
toya (ake tunanin) hukuncinsa zai Kasance akan wacce ta sanya shi saboda zuwa
Kasuwa, titi da kuma hanyoyi? Babu makawa yin hakan yafi tsananin haramci, Amma
ya halatta taci ado maikyau da turare mai kamshi a gidan mijinta da kuma muharranta
kamar yanda ya zo a Alkur'ani suratul an-nor (31)
Imam
at-taimey yana fada a cikin (Az-awãjir 36/2) Lallai fitar mace da za ta yi tana
mai sanya Turare kuma tana mai kwalliya, yana daga cikin MANYAN LAIFUFFUKA kuma
ko da mijinta ne ya yi Mata izini, kuma duk Waɗannan Hadisan waɗanda suke nuna
haramcin sanya turare ga mace idan zata fita waje) baki Ɗayansu sun shafi gaba ɗayan
lokuta ne Mukhtasar Kitãbu jalbãb Al-mar'atul muslimah (shafi na 44)].
Nassoshin da
suka gabata suna haramta sanya turare ga mace balagaggiya idan za ta fita, kuma
ba su bambance tsakanin matar aure ba da budurwa ko bazawara, wannan sai ya
nuna gamewarsu ga dukkan mata waɗanda sharia ta hau kansu, tun da ba a samu
abin da ya keɓance wasu nau’i ba, sannan kuma an haramta sanya turaren ne:
saboda yana kaiwa zuwa tada sha’awar Maza, wannan kuma baya bambanta tsakanin
matar aure da wacce ba ta yi ba. Amma za ta iya sanyawa ta zauna a gida mijinta
ya ji kamshi, in ta yi hakan za ta samu lada. Haka ma budurwa, za ta iya
sanyawa a tsakanin ‘yan’uwanta mata, ko gaban muharramanta waɗanda ta san ba za
su yi sha’awarta ba.
WALLAHU
A'ALAM
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.