Hukuncin Matar Da Take Rage Kuɗin Cefane

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin Ya Halatta Mace Ta Dunga Rage Kuɗin Cefane Da Mijinta Yake Bata Tana Bukatunta Dasu?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله.

    Idan miji baya ciyar da matarsa da 'ya'yanta ciyarwa tawajibi, ya halatta tadunga diban abun da zai ishesu suci su sha ita da 'ya'yanta ba tare da ɓarna ko wuce gona da iri ba, ba tare dasanin mijinba, saboda hadisin A'isha Allah yakara mata yarda ta ce: hindu bintu Ut-bah tace ya manzan Allah ﷺ lallai Abah sufyan mutum ne mai makwo, baya bani abun da zai isheni nida 'ya'ayana sai abun da nake ɗauka daka dukiyarsa ba tare da saninsa ba, sai ya ce: (kiringa ɗaukar abun da zai isheki da 'ya'yanki da kyautatawa ba tare da ya sani ba). Bukhari (5364).

    Shaukani rahimahullah ya ce: A cikin hadisin Akwai dalilin dake nuna wajibi ne miji yaciyar damatarsa, haka kuma akwai wajabcin Uba dole ne yaciyar da ɗansa, malamai sun yi ijma'i akan hakan.

    Haka duk wanda ciyar damutum yake wajibi a kansa yahalatta wanda ake ciyarwar yadunga tsakurar abun da zai isheshi idan wanda keciyar dashi ɗin baya kamantawa, kuma yanaci gaba dayi masa kwauro, Nailul Audaar (6/383).

    Haka kayan gyaran gida kona shimfida dana cin abunci dana kwanciya bacci da tufafi yahalatta mace tadau kuɗin mijinta ba tare da ya sani ba ta siya inyaki yimata ko baya mata ba tare da sanin sa ba, duka wajibi ne a kansa yasamar dasu ga matarsa da 'ya'yansa.

    Ibnu ƙudama rahimahullahu ya ce: wajibi ne miji yasamarwa matarsa abun da zata bukata nashimfida tai bacci, kama daka katifa, bargo, gado, mayafi, filo, gaba daya zai samar mata gwar-gwadon yanda al'adar garinsu tagudana akai sune mace take amfani dasu wajan kwanciya, da abun da zatake zama da rana natabarma yanda aka saba agarinsu shi ne akasan matar aure tana tanadarsu, da darjumar sallah, tabarmar tsakar daki ko kafet, mai kudi komai arziki dai-dai arzikin miji ko samunsa, talaƙa zai yi shima dai-dai matsayinsa batakurawa akai kowa dai-dai samunsa da arzikinda Allah yahore masa. Al-Mugni (8/169).

    Amma indai ba irin wannan bane damukai bayani haramun ne mace tarage kuɗin cefane tana wasu bukatunta, sai ta tambayeshi yabata nasauran bakatunki wanda suma kinada haƙƙin yabaki kuɗi kiyisu indai basufi karfinsaba ko kuma basu da wani tasirinda zaki damu kanki.

    Hakan yana cikin cin amana da ha'inci wanda haramnne amusulunci baya daka cikin dabi'u na mutanen kirki.

    Saidai akwai mazan dasuke bayarda kuɗin cefanen dasunsan yafi karfin cefanen daza'ayi suna bayarwane dama daniyyar abun da yaragu kiriƙe kiyi amfanin kanki dasu, wannan baza'ace haramun bane bal-ma yana daka cikin kyautatawa.

    Da irin wannan ne wasu masu tausayi dahankali daka cikinku suke adashi da kuɗin dan lokacin da aka samu tasgaro ko matsalar abun yauda kullum sai wadannan kuɗaɗe da miji kebayarwa suyi masa rana kuma kikara ƙima da daraja azuciyarsa yakara nutsuwa dake soyayyarki takaru a cikin zuciyarsa.

    Kawai abun da zakiyi shi ne kizaunar dashi cikin hikima da zolaya da fira tajan hankali kibugi cikinsa ki nuna masa kuɗin cefanenda yake baki shin yana sane dacewar sunfi karfin cefanenku atsaka tsakiyar cefanen daya kamata kuyi, wanda babu ɓarna a cikinsa, ko barnatar da dukiya, inyana sane kin ga kin san matsayin abun da kike ragewar halalne tsantsa, inkuma kawai yana bayarawane anufinsa shi ne abun da zai isheku saiki nunar masa cikin hikima dawayo cewa anya baya yawa kuwa ko kuma ya yi yawa, saiki nunar masa wani lokacin kina ragewa kina danyin wasu harkokinki inya amince koyaci gaba dabaki yanda yasaba koya kara duk baki da matsala dankin rage.

    Amma haka siddan baki fahimci mijinki yana bakine acewar yana sane sunfi karfin cefanenku kawai danki rike sauran yake bakiba, kidunga rage wani abu kina bukatunki, babu shakka wannan kus-kurene babba wanda duk randa yagano zai iya haifar muku da mummunar matsala tsakaninku.

    Allah maɗaukakin sarki yatsaremu daka shawara da kuduba irinta Shaiɗanun aljanu da mutane.

    WALLAHU A'ALAM

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.