𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne Haƙƙin
Mace Akan Mijinta, Da Haƙƙin Miji Akan Matarsa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله. سبحانك
اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.
Musulunci ya
Wajabta wasu haƙƙoƙi akan miji ga matarsa, da haƙƙin miji akan matarsa.
Cikin
Wadannan Haƙƙoƙi akwai waɗanda Sukai tarayya tsakanin Miji da Matarsa..
Haƙƙin Mace
wanda ya keɓanta da ita kaɗai, akwai haƙƙi na dukiya da wanda Bana dukiya ba,
Na dukiya sune: Sadaki, da ciyarwa, da Mazauni.
Waɗanda bana
dukiya ba Sune: Adalci wajan rabon kwana idan su biyune, da Mu'amala bisa kyautatawa,
da rashin cutar da ita.
Allah
madaukakin Sarki ya ce: ku baiwa mata Sadakinsu na Wajibi.
👉 CIYARWA: Wajibi ne miji ya ciyar da Matarsa, da Sharadin
in tana bashi kanta, idan bata bashi kanta, ko tazama fandararriya bata
can-canci ciyar da ita ba.
👉 MAZAUNI: Wajibi ne miji ya samawa matarsa mazauni
gwar-gwadon Samunsa.
Allah
madaukakin Sarki ya ce: Ku Zaunar da Matayenku inda zaku zauna gwar-gwadon
Samunku na arziƙi. Suratul dalaƙ aya ta (6).
👉 ADALCI: Shi ne dai-daito tsakaninta da Kishiyarta, wajan
abun kwanciya da ciyarwa da tufatarwa.
👉 KYAUTATA MU'AMALA: dole ne ya kyautata halayensa da
matarsa da Tausasa Mata, da gabatar da Abun da zai iya gabatar mata wanda zai
tausasa zuciyarta.
Allah
madaukakin Sarki a cikin aya ta (19) cikin Suratul Nisa'i ya ce: Ku zauna dasu
cikin kyautatawa.
Annabi
Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: Inai muku wasici akan kyautatawa mata.
Bukhari
(3153), da Muslim (1468).
👉RASHIN CUTAR DA MACE: Wannan yana daka cikin ginshiƙan
Musulunci, idan cutar da Maƙota haramun ne, cutar da Matarka shi ne yafi zama
haramun.
HAƘƘIN MIJI
AKAN MATARSA.
Haƙƙin miji
akan matarsa yana daka cikin Manyan Haƙƙoƙi, Haƙƙinsa akan matarsa yafi girma
akan nata.
Allah
Madaukakin Sarki a cikin Aya ta (228) cikin suratul Baƙara ya ce: (Maza Suna da
Daraja akan matansu) Suna da haƙƙi mafi girma akan matansu.
👉 Wajibi ne yiwa miji biyayya
Allah ya ce:
Maza Sune shugabanni akan matayensu da Abun da Allah ya fifitasu dashi a kansu.
Nisa'i aya ta (34).
👉 Taimakawa miji wajan jin dadi: idan mace ta hana mijinta
yin jima'i da ita, ta auka cikin laifi babba, sai in tana da uzuri na shari'a,
kamar haila da azumin farillah, da rashin lafiya da maka mantansu.
👉 Kada tayiwa wanda mijinta bayaso ya shiga gidansa izinin
ya shiga.
👉 Kada ki fita daka gida saida izinin mijinki, ko da zuwa duban
iyayenki ne, in basu da lafiya.
👉 Ladabtar da matarsa, idan ta saɓa umarninsa bata hanyar
saɓo ba. Domin Allah yai umarni aladabtar da mace ta hanyar Ƙaurace mata, da
duka mara illatarwa idan sukaƙi yin biyayya.
Malaman
Hanafiyyah Sukace: Ya Halatta Miji ya ladabtar da Matarsa da duka agurare huɗu.
1- Idan bata
yi masa ado, da Kwalliya. idan yana san adon da kwalliyar.
2- Ƙin Amsa
kiransa idan ya kirata zuwa jima'i da ita alhali tana cikin tsarki.
3- Idan bata
Sallah, kuma tana cikin tsarki.
4- Fita daka
cikin gida ba tare da izinin saba..
Dalili shi
ne fadin Allaha madaukakin Sarki cikin suratul nisa'i aya ta (34). (Waɗanda
kukaji tsoran fandarewarsu kuyi musu wa'azi ku ƙaurace musu wajan kwanciya, ku
dakesu).
Da fadinsa cikin
Suratul Tahreem Aya ta (6) { Yaku waɗanda sukai Imani, ku tsare kawunanku dana
iyalanku daka wuta, wacce maka mashinta shi ne mutane da duwatsu.
Ibnu kaseer ya
ce: Ku umarcesu da biyayya ga Allah, ku hanasu aikata saɓo, ku tsayu a kansu
akan umarnin Allah, ku umarcesu da bin umarnin Allah, ku taimakesu wajan bin
Allah, idan kukaga za su saɓi Allah kuyi musu wa'azi, ku tsoratar dasu akai,
Tafseer ibnu kaseer (4/392).
👉 Yiwa miji Hidima, kamar yanda shaikul islam ya fada a
cikin littafinsa fatawa kubra (4/561).
👉 Miƙa wuya ga miji, da bashi yanayi mai kyau, yanda zaiji
daɗi dake matarsa.
👉 Zama da miji da kyautatawa.
👉 Tausasa lafazi da tauna magana yayinda ake magana da
miji.
👉 Kiyaye masa dukiyarsa da kanki idan baya nan.
👉 Riƙe sirrinsa da Amanarsa ta dukiya data magana.
👉 Kula da dukiyarsa da 'ya'yansa da kanki.
👉 Girmama iyayensa da mutunta 'yan'uwansa.
👉 Taimakonsa wajan aikin Allah da taimakon 'yan'uwansa,
kada ki zamo mai rabashi da 'yan'uwansa.
waɗannan
Sune ataƙaice Abun da za mu iya gutsurowa dangane da Haƙƙin mace akan mjinta,
da Haƙƙin miji akan matarsa.
WALLAHU
A'ALAMU.
🖊 Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.