Ticker

6/recent/ticker-posts

Hakkokin Aure Abisa Alƙur'ani Da Sunnah Darasi Na 37 - Kuskuren Ma'aurata Na Kaisu Ga Zaman Zina

Wasu daga cikin maza sukan shar'antawa matansu wani sharaɗi na cewa idan kika fita daga gidan nan ko idan kika aikata abu kaza, to abakacin aurenki.

 Wani kuma matar ce zata nemi zuwa unguwa shi kuma sai ya ce idan kika wuce lokaci kaza to a bakin aurenki.

 Wani kuma zaisa mata dokar shiga wani gida a maƙobtansu, harma ya ce idan kika shiga gida kaza to a bakin aurenki.

 Wani kuma zaice ne idan kika aikata kaza a cikin gidannan to abakin aurenki, dadai makamantan irin waɗannan maganganun.

 Cikin ikon ALLAH sai kuma a samu matar ba ta iya tsallake wannan sharaɗin sai ta aikata  abin da mijin nata ya haneta, to da zarar ta aikata wannan, to ta zama sakakka, idan sukaci gaba da zama a haka ba ta sanar dashi ba suna zaman zina ne, amma laifin yana kanta.

 Amma idan da ta sanar dashi kuma ta nemi afuwarsa to saisu sasanta junansu, amma dai saki ɗaya ya faru a tsakaninsu.

 Sannan kuma maza kudaina saka irin waɗannan sharaɗi mai tsauri haka a tsakaninku da matanku, gwara kuja musu kunne sosai, amma banda saka sharaɗin saki a tsakanin juna.

 Kudaina cewa idan matarka ta aikata kaza ko da a bayan idonka ne a bakin aurenta, wannan kuskure ne babba.

 Sannan kuma mata kuji tsoron ALLAH ku daina irin wannan aikin na karya dokar mazajenku, lallai ALLAH zai tambayeku akan rashin biyayya ga mazajenku.

 Amma duk matar da mijinta ya saka mata wani sharaɗi wanda har ya ce idan ta aikata abin a bakin aurenta, kuma ta aikata a bayan idonsa, to saki ya tabbata.

 Amma da yawa daga cikin matan basa sanar da mazajensu cewa itafa ta karya dokar nan, amma tana neman afuwa ya yafe mata bazata sake ba, domin tunda ya riga ya ƙudurta wannan hukunci tun kafin aikatashi, to saki ya tabbata sai dai ya idan maidake nan take.

 Don haka ina kira gareku ma'aurata maza da mata, kuji tsoron ALLAH a cikin kalamanku, maza kudaina saka irin waɗannan sharaɗi akan matanku, ku kuma mata ku rinƙa kiyaye dokokin mazajenku.

ALLAH ka bamu ikon aiki da  abin da muka karanta.

ALLAH ka yafe mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments