Ticker

6/recent/ticker-posts

AURAN KAFURAI KAFIN SU MUSULUNTA INGANTACCE NE!!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaykum, don Allah ina son a tambaya min malamai wannan tambaya: Wani bawan Allah ne ya musulunta shi da iyalansa ta dalili na, kuma ni na basu kalmar shahada. Su na da yara manya da kanana, sai suka tambaye ni ya ya matsayin auren su nace auren su na nan kamar yadda shariar musulunci ta tsara, sai ya ce min to yaya matsayin yayan su? To gaskiya wannan ne ban sani ba shi ne nake son a mika min wannan tambaya ga malaman Allah yataimaka ameen.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum assalam, To ɗan'uwa auran da kafurai suka yi kafin su musulunta ingantacce ne mutukar sun yi shi akan ƙa'idoji da sharuɗan da suka yarda da su na auratayyarsu, saboda Annabi ﷺ bai canza auran kafiran da suka musulunta ba a zamaninsa, ya tabbatar da su kuma ya yarda da 'ya'yayansu da suka haifa ta hanyar wancan aure. Sahabban Annabi ﷺ da yawa an haife su ne ta hanyar auratayyar zamanin maguzanci kuma musulunci ya yarda da dangantakarsu zuwa iyayansu, wannan ya sa duk ɗan da kafurai suka haifa ta hanyar aure za mu danganta shi zuwa iyayansa bayan sun musulunta.

In kafirai suka yi zina suka haifi Ɗa ba za'a danganta shi zuwa babansa ba bayan ya musulunta.           

Don neman karin bayani duba: Al-mugni na Ibnu Ƙudama 7/115 da kuma sharhul Mumti'i 12/239.

Allah ne mafi Sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments