Shin Ya Halasta Saurayina Ya Taɓa Jikina Don Kawai Ya Kawo Sadaƙi?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, Mlm so nake ai min bayani saurayi ne yakai kudi, da sa rana har kayansa ya kai na lefe, to sai aka ja lokacin da yawa, to mlm ya kasance saurayin in dai ya xo xance sai ya yi ta kokarin taɓa ni ko taɓa wani waje daga jikina, ni kuma ba na son haka, mlm har faɗa muke yi da shi wai a kan ba na ba shi jikina, wai sai ya ce min ai na riga na xama matarsa, kawai ai rana ake jira, ni kuma mlm abun yana damu na, to shi ne nake son na tsaya a kan tafarki guda 1, na yi masa nasihar cewa babu kyau ya ki ya gane, yana cewa ai ni na xama mallakinsa, dan Allah mlm ka fahimtar da ni hakan da ya fada gaskiya ne ko na ki shi ko da kuwa xai fasa aurena? Wannan ita ce tambayata, kuma ina rokon malamina ya taimaka ya amsa min, na gode.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salamu, Subhánallah! Allah ya ƙara tsare mana imaninmu, ‘yar uwa lallai abin da wannan saurayi naki ya faɗa maki ba gaskiya ba ne, har yanzu ke ba matarsa ba ce, saboda addinin Musulunci ya tabbatar cewa babu aure har sai an sami abubuwa guda huɗu kamar haka:

    1.Waliyyi.

    2.Sadaƙi.

    3. Shahidai biyu adilai.

    4. Siga.

    Babu aure sai da waɗannan abubuwa guda huɗu kamar yadda malaman Fiƙhu suka tabbatar. Waliyyi shi ne mai aurar da mace, sadaƙi kuma shi ne haƙƙin da Allah ya ce namiji ya ba macen da zai aura, shahidai biyu adilai su ne za su shaida cewa waliyyin wance ya aurar da ita ga wane, ɗan gidan Alhaji wane ko malam wane, siga kuma ita ce maganar da waliyyinki zai faɗa cewa ni waliyyin wance na aurar da ita ga wane bisa sadaƙi kaza, sai wakilin ango ya ce na karɓa masa zan kai masa, in kuma angon ne da kansa sai ya ce na karɓa.

    To ‘yar uwa malaman fiƙhu sun ce babu aure sai da waɗannan abubuwa, wasu malaman kuma sun taƙaita ne ga waliyyi da sadaƙi da shaidu adilai guda biyu. Don haka ‘yar uwa wannan saurayi naki bai gama cika sharaɗin mallakarki ba har sai an ɗaura maku aure, saboda haka kada ki yarda ki amince masa ya taɓa jikinki kwata-kwata, yin haka haramun ne, har yanzu ke ba matarsa ba ce, sa rana ba ɗaurin aure ba ne.

    Idan kuma ya ƙi dainawa ki yi masa barazanar cewa za ki faɗa wa magabatanki, in Allah ya so zai ji tsoro ya kiyaye. Kuma duk masu yin haka su tuba wa Allah su daina, in dai an yi tuba ingantacciya wadda babu tunanin komawa ga saɓo, tare da yin nadama ga abin da wuce, to tabbas Allah yana karɓar irin wannan tuba kamar yadda ayoyin Alƙur'ani da dama suka tabbatar. Allah ya shiryar da mu.

    Kuma al''adu masu wahalarwa da ake shigowa da su cikin harkar aure duk su suke ƙara haifar da waɗannan matsaloli, saboda al'adun nan na kashe kuɗi su suke sa a ja lokaci mai tsawo kafin aure har ta kai ga hakan ya sa shaiɗan ya shiga saƙanin saurayi da budurwa, don haka sai mu ji tsoron Allah, duk wani abin da bai zama dole ba a harkar aure mu daina matsa wa kanmu da su, yin hakan zai taimaka wajen yin aure cikin ƙanƙanin lokaci kafin a kai ga fara zakkewa saɓon Allah.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.