Ticker

6/recent/ticker-posts

Matsalolin Mata

 Sun kwanta barci, ya kalli matarsa ya ce, ko kin san sau nawa Sayyidina Ali ya yi aure koh ?

Matar Ta kalle shi a fusace ta ce, me yasa ba za ka tambaye ni adadin yaƙoƙinsa ba kafin ya yi auren ba!!..?? Saboda kai matsoraci ne kuma raggo ne, ba don haka ba kai ma ka san ba zan auri raggon namiji ba. Ta juya baya.

Mijin Ya ce, Kaico! Ina ma ban tambayeta ba...!!!

Ta juyo ta kalle shi ta sake cewa, me yasa baka ba ni labarin yadda Sayyidina Ali ya buɗe ƙofar "Kaibar" ba. kai rannan da na ƙulle ka a banɗaki ai kasa buɗewa ka yi...!!! 

Ta ja bargo, shi kuma yana jan "Hasbunallahu wa ni'imal wakil"

Ta sake juyowa ta ce, Sayyidina Ali ya kasance yana tsayuwar dare, in yana karatun Ƙur'ani har suma yake yi saboda jin tsoron Allah. Ban taɓa ganinka kana sallar dare ba, sau ɗaya ka taɓa suma, ranar da Ɓera ya shigo mana ɗaki ka kasa fitar da shi....!!!!

Kaico, da ban tambaye ta ba, da mun yi barci cikin nutsuwa.....!!!! 😂😂😂

Matsalolin Mata

Post a Comment

0 Comments