Ticker

6/recent/ticker-posts

Makaɗan Jama'a

Wannan rubutu ya yi taƙaitaccen sharhi game da makaɗan jama'a a ƙasar Hausa.

Abbas Musa Jega
abbasmusajega750@gmail.com.
Ɗalibi A Sashen Harsunan Nijeriya Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

Kayan Kiɗan Hausawa


Gabatarwa

Makaɗan Jama'a su ne waɗanda ba su tarar yi wa kowa kiɗa. Watau ba sai kana sarauta kaza ba ko kana sana'a kaza, a'a duk wanda ya ba su shi ne uban gidansu. Haka haka suke yi wa Basarake su yi wa mai kuɗi kuma idan ta kama su yi wa talaka. A taƙaice dai wannan rukunin na makaɗa jama'a su makaɗan kowa da kowa ne.

Irin waɗannan makaɗa akan same su suna wasa a ƙofar gidan wani, ko a kasuwa, ko kuma a gefen hanya ko wani keɓattaccen wurin shaƙatawa inda sai an biya za a shiga. Makaɗan jama'a sun kama daga ƴan wasan raha, kamar ƴan kama da ƴan gambara da ƴan ƙoroso. Sun haɗa har da manyan makaɗa kamar su Shata da Ɗanmaraya da Amadu Doka da sauransu.

Watau dai duk wanda ya ɗauki sana'arsa ta kiɗa kamar kasuwanci yana sayar wa kowa fasaharsa sai a ce shi makaɗin jama'a ne.

Ibrahim Yaro Yahya da wasu (1992) ya ce; "Makaɗan jama'a su ne makaɗan da ba su dogara ga wani mutum ɗaya ya zama ubangidansu ba. Sukan yi wa kowa da kowa waƙa saraki da masu kuɗi, da talakawa kai har ma ga karuwai da ɓarayi.


Bello Bala Usman (2021) ya ce; "Makaɗan jama'a su ne waɗanda ake yi wa kirari da cewa kowa ya sha kiɗa abin sa ya bayar. Wanda ya fi kowa shahara a wannan rukunin na makaɗa shi ne Alhaji Mamman Shata".


Daga cikin abin da ke rarrabe makaɗan jama'a da sauran makaɗa shi ne;


1. Ba su da takamaimen ubangida

2. Suna iya yin waƙa a ko'ina

3. Suna yawan yabon halin mutum

4. Suna faɗin duk abin da suka so

5. Suna yawan faɗin sunan wanda ya ba su kuɗi.

6. Suna yin waƙoƙin gargaɗi

7. Suna yin waƙoƙin talla 


 Abdulƙadir Ɗangambo (1982) ya ce "Makaɗan jama'a su ne makaɗan da suke yi wa kowa da kowa waƙa, ba sai mai sarauta ko mai wani mai babban muƙami ba. Su duk wanda ya ba su, ko kuma idan suka ga dama, to, sai su yi masa waƙa". 


 Misalan waɗannan su ne:


Alhaji Mamman Shata

Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos

Muhammadu Ganga-ganga

Haruna Oji

Garba Sufa

Hassan Wayam

Audu Karen Gusau.

Ɗangoma

Sa'idu Ziti

Hussaini Jikan Boka

Sani Ɗan'indo

Babangida Kakadawa

Bello Ɗan sha biyu

Gero Zarto

Audu Wazirin Ɗanduna

Alh. Shehu Ajilo Ɗanguzuri





Makaɗan jama'a sukan gina waƙoƙin ne a kan yabo, wani lokaci kuma sukan yi zambo. Idan za su yi yabo sukan yi yabo da alheri, da gwanancewa a sana'ar wanda za su yaba. Kuma sukan haɗa da yi masa kirari da iyayensa da matansa da ƴaƴansa.


 Kamar yadda Ali Ɗan Saraki yake cewa Alhaji Mamman Ɗangwate;


"Mai-ƙi-faɗi na Mariya Sanusi, Alhaji Ɗangwate

Mijin Tasidi Alhaji Mamman Ɗangwate

Ɗan Ali baban Ali

Wannan yana da ɗab'iar arziki.


Shi kuwa  Alhaji Mamman Shata ga abin da yake cewa Alhaji Magaji Ɗankamasho.


Shugaban ƴan kamasho

Magaji mai ido ɗaya

Mil ɗaya in ya ce sule,

Dole sulen za ka biya

Mil biyu in ya ce dala

Dole dalar za ka biya

Mil arba'in ya ce kwabo

Ka ga kwabon za ka biya

Direba ba za ya ƙi ba.



Waƙar Indon Musawa Ta Shata


"Wata yarinya ga kyan diri

Da kyan tsari Indon Musawa


Wata mace ce mai kyau Indon Musawa


Wata ƴar yarinya mai kyan diri da kyan tafiya Indon Musawa


Ta yi zaune kamar kumsa


Ta ɗan karkace kamar rufu'a


Ga daɗin faɗi kamar basin, lallan hakuri


Ga kuma daɗin riƙo Kamar carbi Indon Musawa


Ga alƙawar da son jama'a Indon Musawa.


Daga cikin waɗannan makaɗan zan ɗauki ɗaya daga ciki in yi bayanin tarihi, kayan kiɗi da kuma wasu daga cikin waƙoƙin da ya yi. Wanda zan ɗauka a cikin wannan rukunin na makaɗa na jama'a shi ne Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos.


Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos an haife shi a garin Ɓukur cikin jahar Filato a shekarar 1964, sunansa na yanka shi ne Adamu. Ya tashi yana maraya ne, mahaifinsa ya rasu a lokacin yana da kwana saba'in a duniya, mahaifiyarsa ta rasu kafin ya isa zangon yaye. Wannan shi ne dalilin da ya sa mutane suke kiran sa ƊANMARAYA.


Asali:

Mahaifin Adamu Ɗanmaraya Basakkwace ne, ana ce da shi Malam Wayya, shi kuma makaɗin kotso ne na sarakuna. Ya yo ƙaura da iyalinsa zuwa Ɓukur a sababiyar yawace-yawacen kiɗa ya zauna wajen Sarkin Ɓukur Alhaji Muhammadu ya zama Sarkin Kiɗan Kotsonsa. Ashe ke nan, ta duba asali, Adamu Ɗanmaraya Jos mutumen Sakkwato ne.


Raino da ƙuruciya da sana'a:

Bayan rasuwar malam Wayya mahaifin Ɗanmaraya, sai Sarkin Ɓukur Alhaji Muhammadu ya ɗauki rainonsa tamkar ɗansa. Ya sanya shi makarantar boko tare da ƴaƴansa, amma bai yi nisa ciki ba. Ya kuma tura shi makarantar allo inda ya sami gwargwadon karatu. Ɗanmaraya ya so ya fuskanci sha'anin sana'a da kasuwanci amma sai sha'anin waƙa ya ɗauke masa hankali. Ya yi biyar mota tare da karnukan mota tun kafin ya kai shekaru goma sha biyu, daga nan sha'anin waƙe-waƙensa ya ƙara kankama.


Fara waƙarsa:


Ɗanmaraya ya fara waƙe-waƙe tare da yara ƴan'uwansa tun da ake tura shi makaranta sai ya janye jiki ya bi su yana yi musu waƙoƙi. Haka kuma ya taɓa biya ga wata zabiya, mawaƙiya Mamu. Zabiya ce mai yin waƙoƙi tana yawon kiɗa, har Allah ya kawo ta Ɓukur inda Adamu ya taɓa biya tare da ita da yaranta  guda biyu wato Audu da Idi. 


Kamar yadda na nuna a lokacin da yake biyar mota waƙoƙinsa suka fara kankama. Waƙarsa ta farko ita ce ta "karen mato". Ya sami basirori game da zaman direba da karen mato da fasinjoji da rikicen-rikicen karen mato, musamman a ci tuwo ba biya da sauransu. Bayan wannan waƙa kuma sai ta "ƴan amalanke" daga nan tafiya ta miƙe. Saboda zaman cuɗanya yau da gobe ya janyo sha'awar Ɗanmaraya ya soma yi musu waƙa don kada ya bar wannan wannan ilmi da ya samu ya tafi a banza.


Kayan ƙidansa

  

Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos yana amfani da kayan kiɗa ne nau'in Isga, wato kayan kiɗa ne waɗanda ba nau'in ganga ba.



KUNTUGI

 Yadda ake haɗa kuntugi shi ne, ana samun gwangwanin kifi ne irin wanda ake haɗa kuntugi da shi, da itace kamar na darbejiya ko na ƙirya wanda za a fiƙe, sai a sami yisgar doki a shirya kuntugi. 


Kuntugin Ɗanmaraya na farko yana yaro ƙarami ya sami fankon ashana da tsinken tsire da yisgar doki ya harhaɗa shi.


A yau akan yi amfani da gwangwanin kifi sadin da itace fiƙaƙƙe da yisgar doki da fatar damo ko wata dabba wajen haɗawa da shirya kuntugi.


Daga cikin makaɗan da ke amfani da kuntugi bayan shi Ɗanmaraya sun haɗa da Babangida Kakadawa da Sani Ɗan'indo da sauransu.


DOKTAN KIƊA


Jami'ar Jos ta yi la'akari da taimakawar da Adamu Ɗanmaraya yake yi ta fuskar habaƙa adabi da al'adun al'ummarsa sai ta girmama shi da ba shi Digirin Dokta, a lokacin bikin saukar karatu na jami'ar na shekarar 1990/1991.


Waƙar karen mato Ɗanmaraya ya yi ta ne a lokacin da yana da shekaru goma sha biyar. Ga misali daga cikinta.


To Bismilla Malam nabaya

Ga faralin Malam nabaya

Ga tarihin Malam nabaya

Aura dillalin ƙuli-ƙuli.


Ga tarihin Malam nabaya

Ɓaleri karen mato

Aura babban kaftaninka rana

Ɗan baƙi mai buje da rana.


Na-innako takalminka la

Ga babban faci a tsuli

Gago mai ɗinki da basilla

Ɗan-baƙi mai totur da sakaina.


Karen mato yai girman kura

Ga gashin baki ga gemu

Ga hana ƙarya ga saje

Sannan kuma ga rinto gidan tuwo.


Ɗanmaraya ya yi waƙoƙi da yawa dangane da fannonin rayuwa daban-daban. Akwai waƙoƙinsa shahararru waɗanda mutane suke sha'awa suke ƙaruwa da ilmantuwa. Daga cikin waƙoƙinsa akwai:


Waƙar Lebura

Waƙar Jawabin aure

Waƙar Malalaci

Waƙar Talakawa

Waƙar Sojoji

Waƙar Ɗangaye

Waƙar Ɗan'adam

Waƙar Tica

Waƙar Sisi Legas

Waƙar Falmata

Waƙar Ƴankamasho



Dubi yadda ya bayyana rayuwar yau da gobe daki-daki cikin waƙar Lebara;


Yau Lebura wai kamar zakka

Aiki rani zuwa kaka

In gwamnati za ta sa doka

Shi Lebura ba shi karya ta


Aiki aiki cikin taro

Ana abu sai ka ce horo

In dai Allah ake tsoro

Da Lebura bai talauci ba

Dubi tara gyaɗa kamar dala

Ƙauye da cikin Kano jalla

A ɗauki guda a ɗora ta

Amma ba za ta goce ba.


Ɗanmaraya ya rasu a ranar ashirin ga watan Yuni na shekarar 2015, ya rasu ba tare da Allah ya nufe shi da haihuwa ba, sai dai ya riƙa yara da yawa a gidansa.


17011443H

26082021M


MANAZARTA

Ɗangambo, A. (1982), Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa.

Gusau, S.M (1987), Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Littafi na ɗaya. Usman Al-amin publishing company, Kano, Nigeria.

Galadanci M.K.M da wasu. (1992) Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare 2. Siga Press Ltd.

Zarruƙ, R.M (2005) da wasu. Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun  Sakandare. Littafi na biyu. University Press PLC Ibadan.

Gusau, S.M. Ƙamusun Kayan Kiɗan Hausa (2016). Century Research and Publishing Ltd. Kano-Nigeria.

Usman, B.B (2021). Laccar aji da aka gabatar a gabatar a sashen nazarin harsunan Najeriya, Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Post a Comment

0 Comments