Baya ga karin harshen Hausa da ake samu a yankuna daban-dabam na ƙasar Hausa, haka ma ana samun karin harshe na rukunin al'umma daban-daban. Karin harshen rukuni kan samu ne, ko dai dalilin matsayi ko muƙami ko aiki ko jinsi ko addini ko ilimi ko kuma shekaru. Wannan bincike ya yi nazarin wani nau'in Hausa na rukuni wadda ake samu a shafin jaridar Aminiya, mai suna 'Shafin Makaranta Hausa’. Binciken ya yi ƙoƙarin fito da nau'in Hausar da shafin ke amfani da ita tare da ƙoƙarin kawo bambancinta da Hausar da aka saba da ita yau da kullum, wannan shi ya ƙara tabbatar da Hausar shafin makaranta Hausa a matsayin wani nau'in karin harshe na rukuni.
Karin Harshe Na Rukuni: Nazarin Hausar Shafin Makaranta Na Jaridar Aminiya
DAGA
Nazir Ibrahim Abbas
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto
Imel: ibrahimabbasnazir@gmail.com
Gsm: +2348060431934
Gabatarwa
Karin harshe wani ɓangare ne na ilimin walwalar harshe a cikin kimiyyar harshe. Karin harshe ya danganci bambancin da ake samu na magana a cikin harshe ɗaya, wanda bai kai ga ya haifar da rashin fahimta kwata-kwata ba tsakanin masu magana da harshen, sai dai ga waɗanda na ‘yan rukunin da ake amfani da shi ba. Ana iya nazarin karin harshe ko ta ɓangaren yanki ko kuma rukuni. Karin harshe na yanki ya danganci bambancin da ake samu a cikin harshe dalilin yanki ko wurin da al'umma suke zaune. Yanki yana iya haifar da nau'in bambancin magana a cikin al'umma masu harshe ɗaya, wanda shi ne ake kira karin harshe na yanki ko nahiya.
Wani nau’in karin harshe, shi ne karin harshe na rukuni. Karin harshen rukuni shi ne wanda ake samu dalilin alaƙa ta rukuni a cikin al’umma. Alaƙar karin harshe na rukuni na iya kasancewa ko dai don shekaru ko matsayi ko ilimi ko addini ko jinsi ko aiki ko kuma muƙami. Wannan rukunin shi ma ya kan haifar da nau’in magana daban, daidai rukunan da muka ambata a sama.
A wannan takardar an yi bincike mai taken: ‘Karin Harshe Na Rukuni: Nazarin Hausar Shafin Makaranta na Jaridar Aminiya’, za a duba wani nau’in Hausa na rukuni wadda ake yi a wani shafin jaridar Aminiya mai suna ‘Makaranta Hausa’. Hausar shafin makaranta ta danganci wani rukunin al’umma keɓantattu da ke matsayin ɗaliban makaranta da malaminsu mai suna Ɗodo’. Ita wannan Hausa, ɗaliban da masu karanta shafin a kai a kai ne kaɗai ke iya fahimtar abin da take nufi kai tsaye. Kalmomin da ake amfani da su a shafin na Hausa ne amma rukunin ɗaliban makarantar da malaminsu ne suke tsara su, suna kuma amfani da su, kuma su ne suka fi sanin hanyar da suke bi wajen ƙirƙiro kalmomin da kuma jumlolin daga cikin Hausar da aka saba da ita.
Sha’awar Hausar shafin ta la’akari da hikimomin da ke ciki, shi ya sa na yi nazari a kan Hausar a matsayin wani nau’in karin harshe na rukuni.
Bayanan da za mu yi amfani da su mun tattara su ne daga cikin jaridu goma sha uku (na makawanni 13) da ke ƙunshe da shafin na ‘Makaranta Hausa’. Shafin yana fitowa a shafi na goma sha huɗu (14) na jaridar ta Aminiya wadda ake bugawa a kowane sati. Mun yi nazarin Hausar kowane shafi daga cikin waɗannan jaridun a lokacin da nake gudanar da wannan binciken.
Karin Harshe Da Nau’o’insa
Masana da dama sun bayar da ma’anar karin harshe da kuma nau’o’insa. Wasu daga cikin waɗannan masanan su ne:
Skinner (1977:6) Ya kalli harshe a matsayin – ‘Wani nau’in magana a cikin harshe ɗaya, wanda ba shi ne ainihin harshen ba’.
Crystal (2008:142) Ya bayyana - ‘Karin harshe ko dai na yanki ko rukuni, a matsayin wani nau’in magana na harshe wanda ake iya ganewa ta wasu kalmomi da tsarin harshe (nahawu). Y ace karin harshe mafi yawa yana da tsarin furuci ko nau’in magana da ya bambanta’.
Mathews (1977:56) kuwa ya bayyana: ‘Karin da duk wani nau’in magana na harshe musamman kuma wanda ake magana da shi a wani sashe na ƙasa’.
Sani (2009: 02) ya kawo ma’anar karin harshe a matsayin; ‘Nau’i ne daga cikin nau’o’in harshe guda wanda ake amfani da shi musamman a wani sashe na al’umma’.
Adeyanju (1989: 39) kuwa ya kawo ma’anar karin harshe- ‘A matsayin yadda mutum ya saba yin magana a cikin gungun al’umma da yawa masu harshe ɗaya’.
Karin harshe ke nan yana nufin bambancin magana da ake samu tsakanin mutane masu harshe ɗaya wanda bai isa ya haifar da rashin fahimta tsakaninsu ba. Duk harshen da ya bunƙasa yana iya samun karin harshe a cikinsa.
Amfani (1993:02) ya bayyana: ‘Nazarin karin harshe (dialectology) a matsayin nazarin yanayin magana na harshen mutane ɗaya, waɗan da ke fahimtar juna, kuma suna da alaƙar hulɗa ta magana’.
Nau’o’in Karin Harshen Hausa
Karin harshe a Hausa yana da nau’o’i guda biyu; waɗannan kuwa kamar yadda malamai suka bayyana su ne; karin harshe na yanki da kuma karin harshe na rukuni. Karin harshe na yanki, shi ne wanda ake samu dalilin wurin zama ko yankin da al’umma suka fito. A irin wannan hali yanki ko wurin zama yana iya haifar da nau’in magana na daban ga al’umma.
A Hausa kuwa akwai kare-karen harshe na yanki, kamar yadda Bergery (1934), Ahmed Da Daura (1970), Liman (1978), Malka (1978), Amfani (1980, 1993), Zaria (1992), Sani (2003), suka bayyana waɗan da suka haɗa da: Kananci, Sakkwatanci, Dauranci, Zazzaganci, Bausanci, Zamfaranci, Adaranci, Damagaranci, Gobiranci, Kurfayanci, Canganci. Waɗannan kare-karen harshe kuwa ana samunsu ne a yankin Arewacin Nijeriya da Arewacin Jamhuriyar Nijar.
Wasu daga cikin malaman sun rarraba su a matsayin na sashen gabas da yamma ko manya da ƙanana. Yayin da wasu suka kalle su a bisa tsarin tarihin Bayajida.
Ana iya ganin bambancin karin harshe na yanki a dukkan ɓangarorin nazarin kimiyyar harshe tun daga ilimin furuci har i zuwa ga ilimin ma’ana.
A ɓangaren karin harshe rukuni kuwa, Mathews (1977:344) ya bayyana cewa: ‘Nau’in magana ne, wanda ya danganci wani nau’in al’umma ko rukunin wata tawaga ɗaya a cikin al’umma’.
Fagge (2001) Ya yi nazarin karin harshen Hausa na rukuni, inda ya kawo Hausar da ta shafi rukunin al’umma daban-daban wadda ta haɗa da Hausar: ‘Yan siyasa da Hausar gardawa da Hausar ‘Yan ƙadiriyya da Hausar ‘Yan motocin haya da Hausar ‘Yan acaɓa. Bugu da ƙari ya kawo Hausar ‘Yan Sanda da Hausar Makanikai da Hausar Ƙungiyoyin addinai (Ɗariƙa, Izala, Shi’a) da Hausar ‘Yan mata dai sauransu.
Yakasai (2012), Shi ma ya kawo irin wannan Hausa ta rukuni wadda ta ƙunshi Hausar Kasuwanci da Hausar Sarakuna da Hausar Mawaƙa da Hausar Malamai da Hausar Dattijai da Hausar Samari da ‘Yan Mata da Hausar Matan Aure da Hausar Gidana Magajiya da kuma Hausar Wurin Zaman Makoki.
Karin Harshen Hausa na Rukuni
Karin harshe na rukuni, karin harshe ne wanda ya danganci bambancin magana da ake samu dalilin matsayi ko aji ko rukuni ko shekaru ko muƙami ko jinsi ko addini ko ilimi ko kuma tarayyar aiki iri ɗaya (a irin wannan yanayi ne ake samun kalmomin fannu, da suka keɓanta ga wani aiki ko ma’aikata).
Wannan nau’in karin harshe ya sha bamban da karin harshe na yanki domin ana iya samunsa a cikin al’umma ko tsakanin mutanen da suke da tarayya ɗaya daga cikin abubuwan da muka ambata a baya na shekaru ko matsayi ko aji ko ilimi ko jinsi ko aiki ko muƙami.
Bambancin da ake samu a irin wannan karin harshe na rukuni bai yi yawan na karin harshe na yanki ba, domin shi wannan ya fi shafar kalmomi ne da ‘yan guntayen jumloli waɗan da rukunin al’ummar da ke amfani da su, sun fi sauƙin fahimtar saƙon da suka ƙunsa.
Shafin Makaranta Ɗodorido na Jaridar Aminiya’.
Aminiya wata shahararriyar jaridar Hausa ce, wadda kamfanin ‘Media Trust’ da ke da babban ofishinsa a Abuja, ya ke bugawa a kowane mako, jaridar tana fitowa a ranar juma’a ta kowane sati. An fara buga wannan jarida ne, a shekara ta 2006 kuma tana da shafuka arba’in (40) a cikinta.
Kamar mafi yawan jaridu, wannan jaridar ta Aminiya tana da shafukan da suka ƙunshi labarai na gida da na waje da shafukan ilimantarwa da na tallace-tallace da na labaran al’ajabi da rahotanni da kuma shafukan nishaɗantarwa.
Shafin da za mu yi nazari a kansa, shi ne shafin ‘Makaranta Dodorido’ na jaridar Aminiya, wanda shafi ne na, faɗakarwa da ilamantarwa da ke zuwa cikin siga ta nishaɗi. Abin da ya ja hankalina akansa shi ne, Hausar da ake amfani da ita a shafin da yadda ake sarrafata da jujjuyata da ƙirƙiowa da kalmomi abun ban sha’awa, har ya kai ga wanda ba ɗalibin makarantar ba sai ya kasa fahimtar inda aka dosa.
Wannan shafi na ‘Makaranta Dodorido’ a kowane mako yana fitowa a shafi na goma sha huɗu (14) na jaridar Hausa ta Aminiya kuma yana da siga ta nishaɗantarwa da take gudana ta hanyoyi daban-daban. Sigar tana nuna cewa ana isar da wasu saƙonni ne, na ‘yan makaranta.
Tsarin shafin ‘Makaranta Dodorido’ yana tafiya ne bisa tsarin makaranta wadda ke da ɗalibai da malami ɗaya da suke kira Ɗodo’ , wannan ne, ya sa ma akwai surar wani hoto da ba a gane kowane ne ba a saman shafin, a gefen hagu, wanda ga dukkan alamu shi ne hoton Ɗodon’ da adireshinsa na email a ƙasa mai taken ‘turakundodo@yahoo.com’.
Shafin bugu da ƙari yana tafiya ne da tsarin ko dai dodon ya bayar da labari ko kuma saƙon wasiƙu daga ɗaliban makarantar daban-daban da ke jihohin ƙasar nan, waɗan da suke rubutawa don isar da saƙonninsu. Kowace wasiƙa daga ciki tana ɗauke da take, wanda ke nuna saƙon da ta ƙunsa. Mafi yawan lokuta, shafin ya kan tattauna al’amurran da ake ciki a ƙasar nan a cikin gugar zana da nishaɗi da amfani da wasu kalmomi da jumloli na musamman.
Hausar shafin makaranta dodorido, Hausa ce ta rukunin al’umma wadda ta bambanta da Hausar da saba ji ko yi, yau da kullum. Hausa ce wadda ɗaliban makarantar da malaminsu da masu sha’awar shafin waɗan dake karanta shi yau da kullum kawai ne ke gane ta. A nan muna iya kallon Hausar shafin makaranta dodorido, a matsayin karin harshe na rukunin al’umma ɗaya wanda kuma ake iya gane siffofin shi, a misalan da za mu bayar na Hausar malamin da ɗaliban makarantar da za mu fito da su a cikin aikin.
Hausar Shafin Makaranta Na Jaridar Aminiya
Hausar Shafin makaranta dodorido ta jaridar Aminiya, wata Hausa ce ta daban wadda kalmominta da jumlolinta suka bambanta da Hausar sauran rukunin al’umma. Hausar ta ƙunshi fassara wasu kalmomi da jumloli da sunaye kai tsaye tare da ƙirƙira sababbin wasu kalmomi cikin hikima da fassara wani tunanin al’umma ta hanyar ƙirƙira ta annushuwa da gugar zana. Daga cikin irin nau’in wannan Hausa ta rukuni ne ake samun irin waɗannan ƙirƙirarrun kalmomi da kuma jumloli kamar haka:
Lamba | Hausar Shafin Makaranta | Ma’anarta | ||
1. | Direban Alli | Malami | ||
2. | Zaman Lumana | Zaman lafiya | ||
3. | ‘Yan makaranta | Ɗaliban makaranta dodorido | ||
4. | Watsattsakewa da buɗa wagegen littafi | Karatu da rubutu | ||
5. | Taliyar indon-mami | Indomi | ||
6. | Giz-baba | Malamin makarantar | ||
7. | ‘Yayan kaji waɗan da ba a ƙyanƙyashe ba | Ƙwayaƙwai | ||
8. | Ƙaramin lauje | Biyu | ||
9. | Masu hannun riga | Mahaukata | ||
10. | Yaron Daku | Jami’in tsaro | ||
11. | Haramta ƙwambo da bobon bokoko | Boko haram | ||
12. | Ɗan bayan kango | Wanda ba ɗan makaranta ba | ||
13. | ShuɗadƊ’iyar shekara | Shekarar bara | ||
14. | Haurobiyawa | ‘Yan Nijeriya | ||
15. | Ankararwa | Faɗakarwa | ||
16. | Mai-duka | Allah | ||
17. | Jihar Jijjiga ciyawa | Jihar Jigawa | ||
18. | Shugaba Mainasara | Shugaba Goodluck | ||
19. | Ɗan tallafin suɗin gambiza | Kuɗaɗen rarar man fetur | ||
20. | ‘Yan hannu baka hannu ƙwarya | Talakawa | ||
21. | ‘Yan-sa-in-ɗauka-ba-tare-da-na-ajiye-ba | Barayin gwamnati | ||
22. | ‘Yan sa-mu-raba-da-shi | ‘Yan kazagin gwamnati | ||
23. | Tamola da ƙafafun Haurobiyawa | Wasa da hankalin ‘Yan Nijeriya | ||
24. | Wasoson lalita | Satar kuɗin asusun gwamnati | ||
25. | An yi walƙiya mun je gano | Mun gane gaskiya | ||
26. | ‘Yan Allah-ba-ku-mu-samu | ‘Yan barandar siyasa | ||
27. | Jatau mai-sa-in-sa | Jonathan | ||
28. | Jan jinin Haurobiyawa | Satar dukiyar ‘yan Nijeriya | ||
29. | Batu | Magana | ||
30. | Jatau | Jonathan | ||
31. | Jihar Barnawa | Borno | ||
32. | Kwamin-titi | Kwamiti | ||
33. | Kiran sallah da usur | Abin mamaki | ||
34. | Direban mashahuriya makaranta | Malami | ||
35. | Bijiro | Kawo | ||
36. | Haurobiya | Nijeriya | ||
37. | Niyar-jari | Nijar | ||
| Yaren hau-hau wajen hawan sa | Harshen Hausa | ||
39. | Bokan turai na makaranta | Malamin makaranta | ||
40. | Yaren makaranta | Hausar shafin dodorido | ||
41. | Damƙa shi | Kai shi | ||
42. | Kurtun magana | Wayar Gsm | ||
43. | Makaranta ta dodanni | Makarantar dodorido | ||
44. | Saka-ka-tare | Sakatare | ||
45. | Bututun batutuwa | Mai magana da yawun wasu | ||
46. | Malam Dodo/Farfesa Dodo | Malamin makaranta | ||
47. | Wurin ƙwadago | Ma’aikata/Wurin aiki | ||
48. | Harubja | Abuja | ||
49. | Manja | Manaja | ||
50. | Masu hawa sa | Hausawa | ||
51. | Gwamnan Dabawa | Gwamnan Kano | ||
52. | Uwar kowa | Gwamnati | ||
53. | ‘Yan caɓawa | ‘Yan acaɓa | ||
54. | Romon makaranta | Ilimi | ||
55. | Kwankwatsa-tsiya a birnin dabo | Kwankwasiyya a Kano | ||
56. | ‘Yan ƙolaye | Ɗaliban makaranta | ||
57. | Walwalin waliyo a kan Babura | Gudu a kan babura | ||
58. | Bagas | Garaɓasar dumokuraɗiyya | ||
59. | Hana zaburar baburido | Hana acaɓa | ||
60. | Na damo | Haƙuri | ||
61. | Na mujiya | Idanu | ||
62. | Saraf-na-saɗaf | Sanusi Lamiɗo | ||
63. | Walata Ruɗani | Walter Rodney | ||
64. | Kwasar gagarumar jar miya | Sata | ||
65. | Fasko | Gano | ||
66. | Jatau ya jona tantanin mulkinsa | Jonathan ya fara mulki | ||
67. | Dama-dama da kurɗa-kurɗar siyasa | Hada-hadar siyasa | ||
68. | Shekara dubu ƙaramin lauje da sili da ƙaramin lauje | Shekara ta 2012 | ||
69. | Zagaye da madambaci da zagaye da manuniyar ƙasa, madambaci da madambaci da manuniyar ƙasa da manuniyar sama ƙaramin lauje da zagaye da manuniyar ƙasa | 08098896209 | ||
70. | Kwashi-kwaraf | Satar kuɗin gwamnati | ||
71. | Kawun Bararrajewa | Kawu Baraje | ||
72. | Baban-gada-gada mai burga da baragada | Gwamna Babangida | ||
73. | Gwamna mai sunan sulalla | Gwamna Sule Lamiɗo | ||
74. | Gwamna mai kwankwatsa-tsiya a birnin dabo | Gwamna Kwankwaso | ||
75. | Kassara al’umma | Wahalar da al’umma | ||
76. | Ba-haurobiye | Ɗan Nijeriya | ||
77. | Jihar Ni-na-ja | Jihar Niger | ||
78. | Ku-zauna-a-zaure | Kazaure | ||
79. | Garin-ja-haɗe | Garin Haɗeja | ||
80. | Jam’iyya mai ɗan boto da sanda jirge | Jam’iyyar PDP | ||
81. | Shekaru sili da ƙofar hanci | Shekaru 13 | ||
82. | Arewatawa | ‘Yan Arewa | ||
83. | Kadadawa | ‘Yan kudu | ||
84. | Makarantar masu dangwala tawada a kurtu da zayyana a kan allo | Makarantar almajirai | ||
85. | Masu laluben ɗandago da ɗan ƙanzo | Almajirai | ||
86. | Hauren haskaka Haurobiya | Kuɗin wutar lantarki | ||
87. | Hauren-Danja | Niger Delta | ||
88. | Jan linzamin tsuntsayen sama | Tuƙin jigin sama | ||
89. | ‘Yan dugwi-dugwi | Yara | ||
90. | Huta-fara | Karatun Firamare | ||
91. | Babban kusu | Barawo | ||
92. | Zagaye da kwanciyar magirbi da zagaye da manuniyar sama da kwanciyar magirbi da manuniyar ƙasa tsayuwa bisa ƙafa ɗaya da kwanciyar magirbi da manuniyar ƙasa da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya | 07067947944 | |||
93. | Loma-a-murɗe | Lamurde | |||
94. | In-gwangwaje-in-wala | Ngozi Iweala | |||
95. | Man tunkuza | Man fetur | |||
96. | Ruɓaɓɓen-abban-titi | Reuben Abati | |||
97. | Zage na ‘yan dambe | Zage damtse | |||
98. | Kwana manuniyar ƙasa | Kwana tara (9) | |||
99. | Jihar mu-muka-fara-sharia | Jihar Zamfara | |||
100. | Kurtun baburido | Bayan babaur | |||
101. | Kekerido | Keke | |||
102. | Ranar da aka haifi Ɗanladi da ‘Yar ladidiya | Ranar Lahadi | |||
103. | Mutum mai kallon alƙibla | Musulmi | |||
104. | Amintattar jarida | Jaridar Aminiya | |||
105. | Tunanin gizo da ƙoƙi | Ƙarya | |||
106. | Wadatacciyar sallama | Sallama | |||
107. | Masu bautar mahalicci sili | Masu bautar Sarki ɗaya | |||
108. | Gardawan makaranta | Ɗaliban makaranta | |||
109. | Dodo uban dodanni | Malam Dodo | |||
110. | Romon makaranta/gishirin kyautata rayuwa | Ilimi | |||
111. | Dubannin gaisuwa | Dubun gaisuwa | |||
112. | Malam mai almajirai | Malam Dodo | |||
113. | Bayan kada | Kaduna | |||
114. | Jaridar ‘Yar yau | Daily Trust | |||
115. | Jaridar Turanci ta Gadin yana | Jaridar Guardian | |||
117. | Fura mai kyau | Firamare | |||
118. | Malam Nasara El-rusau | Malam Nasiru El-Rufa’i | |||
119. | Gudun loko | Boyo | |||
120. | Batu na dokin ƙarfe | Batun gaskiya | |||
121. | Jihar Bayasa | Jihar Bayelsa | |||
122. | Janatantin | Jonathan | |||
123. | Gazdawa | Ƙauyawa | |||
124. | Man tunkuza | Ɗanyen mai | |||
125. | Damin hauro | Kuɗi | |||
126. | Barade | Sojoji | |||
127. | Ƙarfe ƙofar hanci da ƙofar hanci da zagaye na yammaci | Ƙarfe 3:30 na yamma | |||
128. | BauɗadƊ’en joji, Sissiliya, Gaulan Jatau | Bode George, Cesiliya, Gulak | |||
129. | Waf-sayoyi | Websides | |||
130. | Mafuskantar alƙiblar kaɗaita mahalicci da ibada | Masallaci | |||
131. | Makarantar dodo uban dodanni | Makaranta dodorido | |||
132. | Ranar da aka haifi Ɗanliti | Ranar litinin | |||
133. | Uwar jiki | Lafiya | |||
134. | Bututun batutuwan jatau mai-sa-in-sa | Mai magana da yawun shugaban ƙasa Jonathan | |||
135. | Shugaban masu ɗamara da launin faɗuwar rana a saman riga | Shugaban jami’an Civil Defence | |||
136. | Shaƙulatin ɓangwaro | Riƙon sakainar kashi | |||
137. | Gidan Bokan Turai | Makaranta | |||
138. | Masu addinin Ɗan Amina | Musulmi | |||
139. | Jihar Tumbin Giwa | Kano | |||
140. | Sarki Sili | Sarki ɗaya | |||
141. | Direban buzu da jan hanjin ligidi ana bugi dutsi kwas | Malamin tsibbu mai jan tasbaha | |||
142. | Babban rumbun adana damin hauro na ƙasar Haurobiya | Babban bankin Nijeriya | |||
| Garin Mugurgusa | Garin Gusau | |||
144. | Masu fuskantar alƙibla | Musulmi | |||
145. | Jar boto | Jar hula | |||
146. | Tudun ba ceto | Halaka | |||
147. | Kurtun magana na Halo-Alo | Telfon | |||
148. | Jami’ar Dodorido | Makaranta dodo | |||
149. | Na kuturu | Haƙuri | |||
150. | Abun da ya fi hauka rashin magani | Jahilci | |||
151. | Ci-ba-daɗi | Wahalar da jama’a | |||
152. | Fasa balam-balam | Fasa bam | |||
153. | Dakarun burga | Dakarun JTF | |||
154. | Santala Ƙwaiduwa | Stella Odua | |||
155. | Dokar duniya | Dokar hana fita (Curfew) | |||
156. | ‘Yan hana murƙushe gumin Ɗan Adam | Masu kare haƙƙin al’umma | |||
157. | Shekara dubu ƙaramin lauje da sili da ƙaramin lauje da sili da ƙofar hanci | Shekara ta 2013 | |||
158. | Bututun ‘yan kwakwazo da baza na mujiya | Kafafen watsa labarai na Rediyo da Talabijin | |||
159. | Bala-lura | Bala’i | |||
160. | ‘Yan hana bokoko | ‘Yan book haram | |||
161. | Gwamnan asusun ƙarfanfana | Gwamnan babban bankin Nijeriya | |||
162. | Mina-mina a jihar Ni-na-ja | Hada-hada a jhar Niger | |||
163. | Tsomomuwa | Matsala | |||
164. | Jihar Alan-goguro | Jihar Borno | |||
165. | Ɗabi’ar kifi da kada | Wanka | |||
166. | Kwana kwanciyar magirbi | Kwanaki bakwai (7) | |||
167. | Takalmin malam mantau | Mantuwa | |||
168. | Gagarumar garaɓasar dama-dama da kurɗa-kurɗar wasan Samson-siya-siya | Gajiyar Siyasa | |||
169. | Garin gano | Ganewa | |||
170. | Gusha-da-tsaf | Bula Tsaf | |||
171. | Injinmiya | Injiniya | |||
172. | Yaren kuci-kuci-hutawa | Indiyanci | |||
173. | Turkewa a sunnar Manzo | Aure | |||
174. | Birnin Zage-zage | Zaria | |||
175. | Ɗan ku-ci-ku-ba-mu | Mai roƙo | |||
176. | Masu roɗi-roɗin tufa | Sojoji | |||
177. | Hannun zinari da ƙafar gwalagwalai | Masu kuɗi | |||
178. | Mulkin mulaka’u | Mulkin wahalar da al’umma | |||
179. | Shekara dubu ƙaramin lauje da kwanciyar magirbi | Shekara ta 2007 | |||
180. | Saɓi zarce na kusu | Sata | |||
181. | Wasan Samson-siya-siya | Siyasa | |||
182. | Unguwar zomo | Uzoamaka | |||
183. | Masu ɗamara da ɗan taku da kulki | ‘Yansanda | |||
184. | Ƙaura | Canza wuri | |||
185. | Laluban na koko | Neman abinci | |||
186. | Hausam-fa | Shiyar Hausawa | |||
187. | Gwarawan-fa | Gwarimpa | |||
188. | Ɗunɗume ƙururu | Cin abinci | |||
189. | Likimo | Kwana | |||
190. | Karatun wasiƙar jakin dawa na da birni | Ƙaryar shugabanni ga talakawa | |||
191. | Masu aika-aika | ‘Yan ta’adda | |||
192. | Kuturun hasashe | Tunanin banza | |||
193. | Ranar da aka haifi Ɗanladi da Ladi ƙaramin lauje da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya | Ranar Lahadi 24 ga wata | |||
194. | Rana ta ƙaramin lauje da ƙaramin lauje ga watan janye-wuri na shekara ta dubu ƙaramin lauje da sili da ƙofar hanci | 22-01-2013 | |||
195. | Zagaye da madambaci da sili da manuniyar sama da sili da manuniyar ƙasa da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya da manuniyar sama da babban lauje da sili da babban lauje | 08161946515 | |||
196. | Kamfanin cefanar da labarai | Kamfanin dillancin labarai | |||
197. | Makon da ya arce | Makon da ya gabata | |||
198. | Ɗoki-ɗora | Tsarin zaɓen Nijeriya | |||
199. | Mai martaba babban mutum mai rawani | Sarki | |||
200. | Dirshe | Tsaya | |||
201. | Garin dama-tumatur a jihar Yawon-bebe | Damaturu a jihar Yobe | |||
202. | Karɓar na koko | Karɓar cin hanci | |||
203. | Mutum ƙaramin lauje | Talaka | |||
204. | Ƙarfe ƙofar hanci da rabi | Ƙarfe 3:30 | |||
205. | Sana’ar zabarin baburido | Acaɓa | |||
206. | Kumbon-tsotso | Kumbotso | |||
207. | Taron-rauni | Tarauni | |||
208. | Ƙurƙurido | A daidaita sahu | |||
209. | Damo-da-kura-da-ɗiya | Dumokuraɗiyya | |||
210. | Malala gashin tunkiya da ‘yan matsabbai | Da yawa | |||
211. | Gandun aika-aika | Ganduje | |||
212. | Hauro dubu ɗari babban lauje | Naira dubu ɗari biyar | |||
213. | Damin hauro sili da zagaye da zagaye da zagaye | Naira dubu goma | |||
214. | Babban lauje da zagaye da ƙaramin lauje da zagaye da sili zagaye da babban lauje | 5020105 | |||
215. | Ƙasashen da jaɓa da gafiya da kusu ke wandaƙa | Ƙas ashen da ake satar dukiyar al’umma | |||
216. | Takardun ƙwadago | Takardun ɗaukar aiki | |||
217. | Ƙwadagon hana baƙin haure shige da fice | Immigration | |||
218. | Tagadaz | Agadaz | |||
219. | Jihar Ɗakin kara | Jihar Katsina | |||
220. | Masu hawa sa | Hausawa | |||
221. | Yaren Makaranta | Hausa | |||
222. | Masu zama bisa buzu | Malaman tsibbu | |||
223. | Gidan malam Tunau | Makaranta | |||
224. | Gwamnan Dabawa | Gwamnan Kano | |||
225. | Garin da ake sa dara | Kano | |||
226. | Angwance | Aure | |||
227. | Gidan gaskiya | Hanya | |||
228. | Wa-zai-zo-ya-biya | Wazobiya | |||
229. | Sumul | Ƙalau | |||
230. | Ƙaramin lauje da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya | 24 | |||
231. | ‘Yan mai tako’ina | Masu hali | |||
232. | Adon gari | Mata | |||
233. | Ta ido | Kunya | |||
234. | Halin amale | Handama | |||
235. | Gobara | Lantarki | |||
236. | In da masu yaen hau-hau wurin hawan sa suke zaune | Mazaunin Hausawa | |||
237. | Wuri sili | Wuri ɗaya | |||
238. | Elin-zubar | Elizabeth | |||
239. | Farcen susa | Babu dama | |||
240. | Masu ƙasƙantar da kai wajen gagara misali | Masu ibada | |||
241. | Ta jiki | Shawara | |||
242. | Sintirtir | Sintiri | |||
243. | Rana ta ƙaramin lauje da manuniyar ƙasa ga watan mayun shekara ta dubu ƙaramin lauje da sili da ƙaramin lauje da sili da ƙaramin lauje | 29 ga watan Mayun 2012 | |||
244. | Hauro tiren taliya madambaci da gashin balama sili da zagaye da zagaye | Kuɗi tiriliyon takwas da biliyan ɗari | |||
245. | Tunar kilshi | Harakokin duniya | |||
246. | Gaisuwa irin ta masu addinin Ɗan Amina | Sallama | |||
247. | Baba manga | Bamanga | |||
248. | Tada kan adda | Ta’addanci | |||
249. | Jami’an asusun ilimi | Shugabannin Ƙungiyar ASUU | |||
250. | Kamfanin dumdumdurundum | Kamfanin bayar da wutar lantarki | |||
251. | Batu na ingarmar ƙarfe | Gaskiya | |||
252. | Ranar ‘yancin rani | Ranar tunawa da samun ‘yanci | |||
253. | Baba Ojo | Obasanjo | |||
254. | Shugaba ‘Yar bishiya | Shugaba ‘Yar adua | |||
255. | Zaman-takewa | Cutarwa | |||
256. | Watan Noman-baba | Watan Nuwamba | |||
257. | Doguwar dabba | Raƙumi | |||
258. | Watan-dashen-baba | Watan Disemba | |||
259. | Turken rayuwa | Aure | |||
260. | Cefanar | Sayar | |||
261. | Masanin sisi-da-sisi | Gwamnan babban bankin Nijeriya | |||
262. | Zari-ruga | Satar kuɗin gwamnati a ɓoye | |||
263. | Ma’aikatar kula da sufurin tsuntsayen sama | Ma’aikat kula da jiragen sama | |||
264. | Mai gonaki otawa | Obasanjo | |||
265. | Mace da zane | Ministar kuɗi Ngozi Iweala | |||
266. | Lalita | Asusun ajiya (Accaunt) | |||
267. | Tayar-ladan, Malalen-suya, Indon-isiya | Thailand, Maleysia, Indonisia | |||
268. | Niyar-jari, Zaman-gidan-buwai | Niger, Zimbabwe | |||
269. | Damisoshin Asiya | Ƙasashen Asia | |||
270. | Zaɓi-sonka | Zaɓe | |||
271. | Dama-dama-da-kurɗa-kurɗar wasan Samson-siya-siya | Siyasa | |||
272. | Samartakar kusu | Satar dukiyar gwamnati | |||
273. | Uban-mama | Obama | |||
274. | Amari-kowa | Amurika | |||
275. | Dalilin-taronsu | Jaridar Daily Trust | |||
276. | Faffale-dalili | Jaridar Peoples Daily | |||
277. | Balon-faranti | Jaridar Blue Print | |||
278. | Gadin-yana | Jaridar Guardian | |||
279. | Banda-da-gadi | Jaridar Vanguard | |||
280. | Shugaba mai Gudun-loko | Shugaba Goodluck | |||
281. | Uwargida Damo-haƙuri | Uwargida Patient | |||
282. | Jami’an tsoratarwa | Jami’an tsaro na haɗin gwiwa | |||
289. | Raɓaɓas | Rivers | |||
300. | Mai ɗan taku da kulki | Ɗan sanda | |||
301. | Tonon-Anini | Tony Anini | |||
Matanin Wasu Labaran Shafin Makaranta
A wannan ɓangare zan kawo wasu labarai da na tsakuro daga wasu shafukan ‘Makaranta Dodorido’ da ke cikin jaridar Aminiya domin ganin yadda sigar Hausar shafin take.
‘Yar makaranta ki riƙa ɗumama ɗumame da ɗumi-ɗumi
ɓayan gaisuwa da fatar alheri ga babban direban alli na wannan makaranta da sauran ɗalibai, zan taya abokiyar watsattsakewa da buɗa wagegen littafi a wannan makaranta, wacce ta angwance da yaron Giz-baba da fatan Allah ya ba su zaman lumana, kuma muna so ki nuna masa irin horon da kika samu a hannun malam wajen ɗunɗuma ɗumame da ɗumi-ɗumi da kuma dafa taliyar indon-mami da ‘ya’yan kaji waɗan da ba a ƙyanƙyashe ba’. Aminiya 2012, Febrairu, shafi na 14.
Hausam-fa ko Gwarawan-fa?
‘A shekara ta dubu ƙaramin lauje da kwanciyar magirbi kamfanin buga Amintattun jaridu ƙasar Haurobiya ya yi ƙaura daga unguwar Mawanawasa kan layin zaratan Zambiya zuwa garin Tako-tako, inda aka gina mana ɗakin katako, mu kuwa muke laluben na koko a ciki. Tun daga waccan shekarar zuwa yau nike ta neman inda Hausam-fa take, domin na san a Harubja da akwai rukunin matsugunnin al’umma mai laƙabin ‘Gwarawan-fa’. Don haka nike ta neman ina Hausawam-fa take, ko kuma rukunin matsugunnin al’umma da aka gina a wannan katafaren birnin inda masu magana da yaren Hau-Hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa suke bararraje’. Aminiya, 2012, Satumba, shafi 14.
Kada a rungumi ƙadandoniya
‘Assalamu alaikum ɗaliban wannan makaranta ta mu mai albarka ta Dodorido da ke farfajiyar jarida, sanin kowa ne a rayuwa karɓar abu mai kyau ko maras kyau shi aka fi so ga mutum mai kallon alƙibla, amma a wannan lokaci jama’a sun shiga ruɗani na rayuwa da kallon abin duniya da yin tunanin gizo da ƙoƙi, yawancin mutane zuciyar su ta ƙoƙe kamar ƙoƙiya maza da mata suna tafiya ba kai ba gindi a harkar zamantakewa, kasuwanci da ma sauran al’amurran yau da kullum dab a a faye ɗaukar ƙaddara ba. Kaico duniya rawar ‘yanmata na gaba ya koma baya. Hattara al’umma mu riƙa ɗaukar kaddara idan mun ƙi kuwa mu rungumi ƙadandoniya’.
Daga: Ɗalibar makarantar Tumbin giwa Jamila Ishak (Atinen Ziko) ta garinsu Munyi-jibir, kurtun mangana: zagaye da kwanciyar magirbi da zagaye da manuniyar sama da kwanciyar magirbi da manuniyar ƙasa da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya da kwanciyar magirbi da manuniyar ƙasa da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya da tsayuwa bisa ƙafa ɗaya’. Aminiya, 2013, Afrilu, shafi 14.
1.6 Kammalawa
Wannan maƙala mai taken ‘Karin Harshe na Rukuni: Nazarin Hausar Shafin Makaranta Na Jaridar Aminiya’ ta yi nazari a kan Hausar shafin Makaranta na jaridar Aminiya a matsayin wani nau’in karin harshe na rukuni a Hausa, wanda ya danganci wasu rukunin al’umma da suka haɗu a sigar makaranta, wadda ke da malami da ɗalibai. Shafin kamar yadda muka bayyana a baya ya kan fito ne, ku san kowane mako a jaridar Hausa ta Aminiya kuma ya kan tattauna al’amurran yau da kullum da suke faruwa a cikin al’umma a ƙasar nan cikin nau’in wata Hausa ta daban.
Wannan Hausar kamar yadda misalan da muka bayar suka gabata, Hausa ce ta daban wadda ta keɓanta ga malami da ɗaliban makarantar kawai kuma tana tafiya ne ta sigar Hausantar da kalmomi da fassara wasu tare da amfani da ayyukan wasu mutane ko takensu maimaikon sunayensu. Bugu da ƙari ana kuma ƙirƙiro wasu jumloli da sassan jumlolin Hausa. Shafin musamman yana da tsarin da yake bi wajen bayyana lambobi, wanda sai ƙwararre a irin wannan Hausar ne zai iya fahmitarsu. A tunani na, wannan Hausa idan aka ƙara zurfafa bincike a kanta da wasu makamantanta za ta taimaka wajen samar da nau’in wani harshe na daban wanda zai iya taimakawa wajen sadarwa a keɓaɓɓun wurare, musamman wajen inganta sadarwa ta wasu ma’aikata na musamman ko kuma wurin ayyukan jami’an tsaro a ƙasar nan. Haka ma Hausar tana iya haifar da wani karin harshe babba, wanda za a iya faɗaɗa bincike a kansa.
Akwai buƙatar a yi amfani da basira da ƙwarewar mutane masu irin wannan baiwar ƙirƙira a harshe domin haɓaka harshen da duban yadda za su bayar da gudummuwa ga ci gaban al’umma da ƙasa baki ɗaya. Wannan bincike ya nuna muna cewa harshen Hausa yana iya bunƙasa ta irin wannan hanya har a kai ya haifar da wani harshe a cikin al’umma, idan aka baiwa irin waɗannan mutane masu baiwa ta harshe goyon baya da taimakon da ya dace.
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.