Ticker

6/recent/ticker-posts

Shaye-Shaye A Garin Gusau (4)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Shaye-Shaye A Garin Gusau (4)

NA

BASHAR ISYAKA

Shaye-shaye 

BABI NA UKU

ILLOLIN SHAYE-SAYE

3.0 GABATARWA

Wannan babi zai tattauna ne a kan illolin shaye-shaye waɗanda suka haɗa da: Taɓarɓarewar taribiya, haifar da lalaci ga matasa, haifar da sace-sace a cikin al’umma, bangar siyasa, fyaɗe, fisgen wayoyi, da sauransu.

 

3.1 TAƁARƁAREWAR TARBIYA

Taɓarɓarewar tarbiya kan faru ga matasa ta hanyoyi da dama sakamakon samun kansu cikin wani yanayi na ƙunchin rayuwa. Wasu daga cikin waɗannan hanyoyi su ne kamar haka:

 

1. Jahilci: Jahili na ɗaya daga cikin abubuwan da ke kawo taɓarɓarewar tarbiyar matasa. Domin matashi wanda bai yi karatu ba, yana tashi cikin gurguwar rayuwa da rashin sanin ya kamata. Kuma akasari waɗannan matasa kan tashi da yawace-yawacen banza wanda kan jefa su cikin aikata abubuwan da ba su dace ba. Saboda haka, dole ne a ba yara ingantaccen ilimi domin a kyautata rayuwarsu.

 

2. Maraici: Maraici kan zama musabbabin tabarɓarewar rayuwar mutum musamman ƙananan yara. Wannan kan auku ne a sakamakon rashin samun kulawa ta fannonin rayuwa daban-daban, kamar wajen ɗaukar nauyin ilimi musamman a matakin farko, da ba yaro tarbiyya da kuma kula da irin mutanen da yake mu’amala da su a lokacin ƙurciyarsa. Saboda haka akwai buƙatar masu hannu da shuni da hukumomi da sauran ƙunyiyoyi su riƙa ba da tallafi na musamman domin kulawa da yaran da ke cikin irin wannan hali domin inganta rayuwarsu.

 

3. Talauchi: A wasu lokutan kuma talauci kan zama musabbabin samun matsala ga rayuwar mutane da dama domin kuwa sau da yawa iyaye kan yi watsi da al’amarin kulawa da ‘ya’yansu a lokacin da fafutukar neman abin masarufi ta ɗauke masu hankali. Wannan kan gurgunta karatun yara tun daga matakin farko, saboda rashin samun kulawar da ta kamata.

 

Haka kuma akan samu matsalar tallace-tallace da yara ke yi musamman ‘yan mata, wadda kan jawo taɓarɓarewar iliminsu da ma tarbiyyarsu baki ɗaya. Saboda haka, akwai buƙatar iyaye su yi taka tsan-tsan kuma su ba da cikakkiyar kulawa wajen tarbiyantar da ‘ya’yansu, ta fuskar ɗaukar nauyin karatunsu tun daga Firamare har zuwa Jami’a.

 

4. Rashin Kulawa daga Iyaye: Wasu iyaye kan nuna halin ko in kula wajen tarbiyantar da ‘ya’yansu. A yayin da wasu iyaye kuma kan nuna so mai tsanani ga ‘ya’yansu wanda a ƙarshe yake haifar da matsala. Irin waɗannan iyaye kan yi biris su ƙi tsawata ‘ya’yansu ko da sun yi ba dai-dai ba domin gudun bacin ransu. Wannan matsala ce mai haifar da kangarewar ‘ya’ya su zama masu kunnen ƙashi, kuma daga ƙarshe su fi ƙarfin iyayen. Don haka ya zama wajibi iyaye su kasance suna nuna wa ‘ya’yansu abin da ya kamata tun lokacin ƙurciyarsu, domin icce tun yana ɗanye ake lanƙwasa shi, idan ya bushe baya lanƙwasuwa sai ya kare.

 

5. Zaman kashe wando: Rashin aikin yin na iya zama dalilin gurɓacewar tarbiyya a mafi yawancin lokuta, domin kuwa idan mutum ya kasance ba ya da aikin yi yakan fara tunanin yadda zai yi ya samu abin yi ta hanyoyi daban-daban. Idan bai cimma burinsa ba to a ƙarshe yana iya fadawa cikin kowace irin sana’a wanda haka shi ke jefa matasa cikin waɗansu sana’o’i waɗanda bai halatta ba. Saboda haka ya kamata maga’isan yara da hukumomi na kowane mataki da sauran kungiyoyi su shiga a dama da su kuma su yi aiki tukuru domin ganin cewa an kauda wannan matsala ɗari bisa ɗari a zukatan ‘ya’yanmu.

 

3.2 HAIFAR DA LALACI GA MATASA

Lalaci shi ne zama ko-ma- baya a cikin al’umma tare da rashin iya biya wa kai buƙata domin cigaban rayuwarsa da kuma al’umma baki ɗaya. Ta sanadiyar shaye-shaye, matasa kan lalace tare da yin ko oho, da abubuwan cigaban rayuwa, da suka ƙunshi ilimi, girmama uwaye da maga isa, tare da zaman banza na rashin dogara da kai na wata sana’a ko aikin hannu.

 

Haka kuma shaye-shaye kan sa mai yin sa ya lalace ta fuskar ƙirar jikinsa, ya haifar masa da rashin lafiyar lalacewar huhu ko kuma ƙoda, ko hanta da sauransu.

 

3.3 HAIFAR DA SACE-SACE A CIKIN AL’UMMA.

Shaye-shaye yana da matuƙar illa ga mai yin sa da kuma al’umma baki ɗaya. Domin fitinar mashaya kan dami al’umma dangane da abin da ya shafi sace-sacen ababe daban-daban. Sata wata babbar musiba ce wadda ta zama ruwan dare ga al’umma musamman matasa masu tasowa. Yanzu kuma akasari wannan ɗabi’ar ta shaye-shaye ita ce ummul haba’isin wannan sata. Domin cikin kayan shaye-shaye akwai wanda da zarar aka sha shi, to zai nuna ma mashayi ba a ganin shi don haka komi yana iya yi har da sata.

 

Mashaya kan fantsama cikin al’umma domin samun kuɗi ko wasu ababe na biyan buƙatun rayuwa. Alhali kuma ba su ajiye ba, ba su bayar da ajiya ba, sai dai su sha kayan maye su ɗauki makamai su farwa mutane a cikin gidaje, ko masana’antu, ko gonakki, ko kan hanya da sauransu.

 

3.4 BANGAR SIYASA

Bangar siyasa ita ce inda matasa kan bi wani ɗan siyasa domin tallatashi da kuma ‘yan siyasa daban-daban, da ba su miyagun makamai; wanda kan haifar da ababe kamar haka:

 

a.      Sace – Sace: A fagen siyasa ne matasa kan sha kayan maye daban-daban idan za su fito wani taro kamar yekuwar neman zaɓe, inda sukan aikata laifukka kamar sace-sacen kuɗi, ko cin abinci ga mai sana’a, har sukan iya karɓar canji ba tare da sun bayar da kuɗi ba.

 

b.     Fyaɗe: A tafiya irin ta bangar siyasa wani lokaci akan samu cuɗanya tsakanin mata da maza. Matasa sukan sha kayan maye wanda yakan sa su fita hayyacinsu, har abin ya haifar da mummunar laifi na afka wa wasu daga cikin matan suna saduwa da su ba tare da yardarsu ba, wanda masana hakkin bil-adama kan kira da fyaɗe.

 

c.       Fisgen Wayoyi: A sanadiyar bangar siyasa ne matasa da dama masu ɗabi’ar shaye-shaye suka saba da riƙa kuɗaɗe ba tare da yin wata sana’a ba. Amma daga baya sai abun ya sauya sabon salo na fisgen wayoyi a unguwanni da wuraren taruwar jama’a da ban-daban, domin su sayar su samu kuɗaɗe na biyan buƙatunsu na yau da kullum. Haka kuma da sayen kayan maye da miyagun makamai da sauransu, domin aikata ta’addanci na fisgen wayoyin mutane.

 

3.5 KAMMALAWA

A cikin wannan babi na kawo bayani game da illolin shaye-shaye waɗanda suka haɗa da taɓarɓarewar tarbiyya, haifar da lalaci, haifar da sace-sace a cikin al’umma bangar siyasa, kamar su sace-sace, fyaɗe, fisgen wayoyi, da sane (yankan aljihu suna sace kuɗi).

Post a Comment

0 Comments