Ticker

6/recent/ticker-posts

Auren Gargajiya A Garin Kwatarkwashi (6)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Auren Gargajiya A Garin Kwatarkwashi (6)

NA

NURA SANI KOTORKOSHI

 

Kayan aure

BABI NA BIYAR

5.0 JAWABIN KAMMALAWA

Kamar yadda na bayyana a baya cewa garin Kwatarwkashi yana cikin ƙaramar hukumar mulki ta Bunguɗu a jihar Zamfara. Haka kuma mutanen da ke ainihin maƙasudin kafa wannan gari sun taho ne daga ƙasar Katsina.

 

Mutumin da ke musabbabin kafa wannan gari na Kwatarkwashi wani mutum ne mai suna Kwatashi. Hasali ma daga wannan suna ne aka samo ainihin sunan da ake kiran wannan gari da shi wato Kwatarkwashi. A lokacin da Kwatashi ya iso wannan gari ya zauna a wurare daban-daban wanda a ƙarshe ya kafa garin Kwatarkwashi gab da gindin wani dutsi da ake kira dukura. Wato inda Kwatarkwashi take yanzu.

 

Kwatashi shi ne mutum na farko da ya fara sarautar wannan gari na Kwatarkawashi. Tun daga ainihin kafuwar wannan gari har ya zuwa yau an samu kimanin sarki ashirin da tawkas (28). Alhaji Amadu Sarki na yanzu shi ne Sarki na ashirin da takwas, ya kuma samu kimanin shekaru kusan hamsin da takwas a bisa karagar mulki.

 

Aure dai wajibi ne a kowace al’umma a aiwatar da shi. Don haka, na ga yadda mutanen Kwatarkwashi suke gudanar da aurensu ta bin dokokin addininsu na gargajiya a wancan lokaci. Duk da yake, waɗannan al’adu na gargajiya sun saɓawa ka’idoji da kuma dokokin addinin Musulunci, yana da kyau a fito dasu a fili domin a samu kauracewa waɗanda basu da kyau daga cikinsu. Haka kuma irin abubuwan da suka faru tun daga ainihin kafuwarsa zai ba mutane dama su gane ko kuma su fahimci irin ci-gaban da wannan gari ya samu tun daga farkon kafuwarsa har zuwa wannan lokaci.

 

Bincike akan irin waɗannan al’adu na gargajiya yana taimakawa wajen baiwa matasa tarihin rayuwar magabata da abin da suka taɓuka da hikimominsu yadda su ma matasa za su sami abin alfahari da tinƙaho da shi game da tarihin ƙasarsu.

 

Haka kuma fito da waɗannan al’adu fili yana da muhimmanci, domin yana faɗakar da mutane dangane da yadda za su kare kansu daga miyagun ayyuka da kuma yadda za su yi hulɗa da cuɗanya da jama’a.

 

5.1 KAMMALAWA

Kamar yadda aka bayyana. Take wannan kudin shi ne; “Auren Gargajiya a Garin Kwatarkwashi” Kamar dai yadda aka gani tun farko wannan bincike, an raba shi zuwa babi-babi har babi biyar kamar haka:

 

A babi na farko, wato share fage, an yi tsokaci a kan gabatarwa da dalilin gudanar da bincike da manufar bincike da farfajiyar bincike da hanyoyin gudanar da bincike da kuma muhimmancin bincike.

Sai babi na biyu, inda aka yi bitar ayyukan magabata da suka jiɓinci aikin nawa. Ayyukan da aka duba sun haɗa da kundayen bincike da bugaggun littattafai da kuma mujallu da maƙalu.

 

Babi na uku inda aka yi nazarin taƙaitaccen tarihin masarautar Kwatarkwashi, inda nayi tsokaci a kan ma’anar Kalmar Kwatarkwashi da kafuwar garin da addinin gargajiya da sana’o’in da zanen suna da kuma kaciya.

 

A babi na huɗu kuwa, wato gundarin aikin, an kalli ma’anar aure da ire-iren aure da auren gargajiya kwatarkwashi da zaman lalle daurin aure da al’adun aure kafin gudanar da buki da al’adun aure lokaci da bayan mutwarsa a tsakanin Kwatarkwasawa.

 

Babi na biyar kuma na ƙarshe wato naɗewa. An kawo jawabin kammalawa da kammalawa da shawarwari da kuma manazarta.

 

5.2 SHAWARWARI

Shawara muhimmiyar abu ce, Hausawa ma na cewa “Mai shawara aikinsa ba ya ɓaci” tabbas wannan Karin magana haka yake. Duk da kasancewar ni ɗalibi ne mai nazarin harshen Hausawa ba zan rasa shawarar da za ni baiwa malamai da ‘yan uwana ɗalibai ba. Shawara ta farko ita ce ga masu aikin gudanar da bincike kamar ni, idan za ayi nazari ko bin cike kan wani abu ya kamata a tsaya a natsu tare da bin ingantattun hanyoyi domin gudanar da bincike. Tare da yin amfani da kalmomi masu sauƙi yadda aikin zai yi alfanu da nagarta.

 

Shawarata ta biyu kuwa ina kira ga ɗaliban da suke wannan makaranta da ma sauran makarantu da a riƙa yawaita bincike a ɗakunan karatu musamman idan an ba da aikin jinga domin zai taimaka ƙwarai wajen samun bayanai ba tare da an wahala ba.

 

Haka kuma, ina baiwa malamanmu shawara, musamman na wannan sashe mai albarka, wato sashen Hausa da su matsa ƙaimi domin su riƙa nazari ɓangaren al’ada, domin yana ɗaya daga cikin tubalin ginin al’umma musamman fitattun al’adu irin na mutanen ƙasar kwatarkwashi.

Bugu da ƙari, ina bai wa ɗalibai shawara da su yi amfani da wannan aiki nawa, su karanta shi domin na tabbata zai zamar musu jagora idan buƙata ta taso.

Su ma mutanen ƙasar Kwatarkwashi ba mu bar su a baya ba, ina basu shawara da su tashi tsaye wajen ganin sun inganta al’adunsu tare da ganin sun bunƙasa su ta hanyar sauya su da zamani da kuma aƙidar addinin Musulunci

Shawara ta ƙarshe ita ce zuwa ga gwamnati da ta daure ta riƙa ɗaukar nauyin wasu ɗalibbai tana tura su jami’o’i daban-daban domin yin nazari a harshen Hausa. Wannan zai ba wa mutane sha’awar yin nazari a kan wannan fanni.

MANAZARTA

Tuntuɓi Amsoshi.

Post a Comment

0 Comments