Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Cin Nasara 10: Ba Wa Ƙwaƙwalwa Damar Aiki

Da yawa mutane masu himma sun sami abin da suke buri. Wani zai gaya maka shi babban soja ne, kuma wallahi tun yana ƙarami bai da buri sai aikin sojan. Wani zai ce maka likita ne shi. Tun yana ƙarami burinsa ke nan. Wasu lamuran Allah kan dubi zuciyoyimmu ne ya...

Hanyoyin Cin Nasara 10: Ba Wa Ƙwaƙwalwa Damar Aiki

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Mutane sun karkasu zuwa gidaje daban-daban, akwai masu ƙoƙari  waɗanda kullum cikin tunanin bunƙasa ayyukansu suke yi, in dan kasuwa ne wanda yake sayar da gwanjo, yakan fara tunanin cewa nan gaba fa zai iya tsallake wannan sana'ar zuwa wace ta fi ta, kamar sayar da sabbin kaya  waɗanda aka yiwo odarsu daga ƙasashen waje, in mai sayar da takalma ne a bakin titi yana bin motoci da gudu, zai fara tunanin cewa nan gaba fa jarinsa zai yi yawa zai kama shago, zai zama babban dan kasuwa har a mutane zu riƙa zuwa suna sarin kaya a wurinsa.
.
In kuma malamin makaranta ne zai fara tunanin zai zama babba har ya yi fice a fagen ilimi, zai gina makaranta tasa mai cin gashin kanta, in karen mota ne yana tunanin zai zama direba zai sami mota tasa ta kansa, zai zo ya sayi motoci nan gaba ya dauki direbobi yana biyansu,  waɗannan abubuwa ba su rabuwa da zuciyoyin gwarazan mutane,  waɗanda duk abin da za su yi suna tunanin gaba, kamar mutum mai ƙaunar ibada kullum a masallaci, har ya fara burin a ce shi ne ladanin masallacin, yau da gobe ya zama na'ibin limamin, ko a ba shi limanci a wani masallacin, da yawa in mutum zai kama haya saboda zai yi aure za ka ga ya fara tunanin inda yaransa za su riƙa kwana da tarbiyar da za su samu a matattarar, bayan ko auren ba a daura ba, tsari ke nan.
.
Da yawa mutane masu himma sun sami abin da suke buri. Wani zai gaya maka shi babban soja ne, kuma wallahi tun yana ƙarami bai da buri sai aikin sojan. Wani zai ce maka likita ne shi. Tun yana ƙarami burinsa ke nan. Wasu lamuran Allah kan dubi zuciyoyimmu ne ya biya mana buƙatummu. Dubi dai waƙa da ake ganin abar banza ce, na dubi Hauwa Kululu wace Mamman Shata ya yi wa waƙa, tana cewa tun tana yarinya ba ta aikuwa sai in mutum zai yi mata waƙar Shata, asali ita yariya ce ƙarama, ba ita ce mai sayar da tuwon ba babarta ce.
.
Lamarinta ya riƙa ba masu sayen tuwon babarta al'ajabi, kwatsam sai ga Mamman Shata din wata rana ya sauka wurin babarta, aka ba shi labari kuma aka nemi ya yi mata waƙa, Shata ya zauna ya waƙe ta fes, burinta ya cika, amma fa ba arha ta sami wannan daukakar ba, sai da ta tsaya kan burinta har ta kai ga gaci, sauran lamura da kake gani a rayuwa duk haka suke, ba yadda za a yi mutum ya kai ga biyan buƙata ba tare da ya tsaya ƙyam kan abin da yake so ba, kullum tunaninsa shi ne ya zan kai ga wannan ƙudurin nawa?
.
Burina a ce na zama malami, na fara koyarwa ne a makarantar Islamiyya ta dare, a hankali har na dawo ta safe, na koma furamare, na fara karantarwa a sakandare da ta manyan mutane, na karantar a kwaleji kafin yanzu na komo jami'a, tafiyar ba mai sauƙi ce ba kamar yadda na karanto haka, akwai jarabowoyi a tsakiya kala daban-daban, wasu har ba ka son ka tuna su, ba ka ƙaunar ka ga wanda ya san su, burin mutum a zuciya kawai ya isa wurin da yake hari, kuma zai isa din amma sai da taimakon Allah SW, ke nan tun farko shi ne mutum zai fara kamawa, in ya amince maka dole a baka, duk abin da za ka yi kar ka manta da mahaliccinka.
.
A cikin mutane akwai  waɗanda suke son ci-gaban, kuma suna ganinsa tare da wani, amma ba sa ƙaunar su motsa, ba sa iya yin tunanin cewa za su zama wani abu nan gaba, wanda yake yankar farce dole ya saka cewa zai zama wani abu yadda nan gaba shi ma za a zo a yanke masa, bunƙasa sana'a dole ne in ba haka ba nan gaba za a rasa mai yi, amma ci-gaba ma wajibi ne, ba yadda za a yi ka ce kaza na gada kansa zan mutu, bai zama dole sai ka canja sana'a ba, amma ka yi tunanin ya za ka bunƙasa shi har mutane birjik su ƙaru da kai?
.
Ba yadda za ka bunƙasa gadon mahaifinka sai ka yi tunanin kawo na'urorin da za su sauƙaƙa aiki su inganta shi ta yadda za a riƙa yi da yawa, ko a canja salo, duk abin da ka sani a duniyannan za a iya inganta shi, na san wani yaro da ya taso a gaban mahaifinsa tela, yanzu ya zama babban tela ya kawo manyan kekuna masu yi wa kaya ado, da haka ya mallaki gida na kansa da ma'aikata masu yawa, sana'ar dinkin ce dai ba a canja ba, amma an ƙawata ta, an habbaka ta, an inganta ta, wannan ya sa aka ƙara samun dafifin jama'a dake burin ganin an yi musu dinki a shagon.
.
Duk wani babban mutum da kake gani wanda ya ci nasara a rayuwarsa ta hada-hada, ko cinikayya, ko wani fanni na aiki ko sana'a in zai gaya maka hanyoyin da ya bi don ganin ya cimma burinsa za ka taras sai da ya ci baƙar wahala, anan akwai abubuwa guda biyu:-

1) Ya sa abin a ransa don ganin ya cimma burinsa, ya yi ta bin hanyoyi daban-daban don ganin hakan ya wakana, ko dai karatu, ko mutanen da yake ganin za su taimake shi, ko bibiyar shawarwarin da za su isar da shi.

2) Aiki tuƙuru kan jiki kan ƙarfi, yin amfani da kuɗi wajen sayen kayan aikin da in ba a samo su ba aikin ba zai yuwu ba.

Post a Comment

0 Comments