Ticker

6/recent/ticker-posts

Maƙarƙashiya



Waƙar ƙwar biyar ce, babban amsa amonta “ya”. Yawan baitocinta hamsin (50). An kammala ta ranar Lahadi 25/05/2014 daga Masar zuwa Katsina, an haɗa ta a Kano, Mumbayya House, BUK, ɗaki na 10. Ga dukkanin alamu kashe-kashe da zubar da jini da ta’addancin da ake son a liƙa wa musulmin Arewacin Nijeriya, maƙarƙashiya ce. Tilas, a sake zama a nazarci matsalolin da idon adalci a ɗebe bambancin addini da aƙida da siyasa da yanki da ɓangaranci. Zancen Boko Haram wata sabara ce da ake fakewa da ita a harbi barewar da ake son a kashe. Idan haka ne kuwa, ya zama dole a sake lale ‘yan dara, a hura wuta kowa ya ga rabonsa, komi taka zama ta zama.
---------------------------
-------------------------------
1.       Allah na kiraye ka,
          Salati nikai wa manzonKa,
Ga Sayyidina ma’aikinKa,
Muhammadu mai gari Makka,
          Aminu mazan nagarta.

2.       Bayani nai nufin saƙa,
Cikin lafazi na mai waƙa,
Saboda kuranye gaggaƙa,
Wuyanmu da an ka sa sarƙa,
          A kan tsananin mugunta.

3.       A yau mu ɗai ake dako,
          Da mui zance a sa tarko,
A hau bisa kanmu ba tsaiko,
A sa muna tarnaƙin iko,
          Gabanmu da baya cuta.

4.       Musiba babba nah hanga,
Aboki tsaya ka ɗan waiga,
Ƙasarmu tana cikin sabga,
Na ruɗani da damaga,
          Da babu irinsa wauta.

5.       Ga tarihi na tarayya,
          Zama aka yi na soyayya,
Idan aka fara jayayya,
Gabaci za a ba hanya,
          A tabbata an tuƙe ta.

6.       A bar fitina ta gawurta,
Ana kallo ta ƙasaita,
A jefa ƙasa ga ragaita,
Ɗiyanta a sa su tozarta,
          Saboda ɗiyan maƙwabta.


7.       A kan tsabar munafucci,
Da makircin ƙabilanci,
A ware ƙasa da ɓangarci,
A sa mu cikin agolanci,
          Da yin hijirar barin ta.

8.       Muna kallo a ƙware mu,
A yo gayya a yaƙe mu,
Ana ta kashe matasanmu,
A watse dukan biranenmu,
          A sa mu cikin asuta.

9.       Musiba duk a ce mu ne,
Idan aka hango mun gane,
A gayyato masu jan kunne,
A ce musu ga su can su ne,
          Su buɗe wuta da hauka.

10.     Ƙasa duka an ka wa miki,
Mutan ciki na da jan aiki,
A tilasta su yin raki,
A kwana a tashi ba girki,
          Ƙasa tilas barin ta.

11.     Buƙatar masu yaƙanmu,
Gaban a raba su ƙware mu,
A karkashe masu ƙazonmu,
A tarwatsa arziki namu,
          Su tura ɗiyanmu bauta.

12.     Takaici na gidan soja,
Mazajen rungumar danja,
Muƙami sai ɗiyan Neja,
Ɗiyanmu a ba su masinja,
          Waɗansu su zan kurata.



13.     Tsaro da shirin ƙasa tamu,
Suna hannun magabtanmu,
Muna kallo a ƙware mu,
Mu kasa tsayi da ƙarfinmu,
          Mu tabbata an kwatanta.

14.     Ina aka kai mu ‘yan boko,
Sarakai masu jin iko,
Da ‘yan ɗamarar dakon ciko,
Birai su mayar da mu soko,
          Ƙashi ya kashe mahauta.

15.     A bi mu ana ta mammara,
Mu faɗi ana ta shusshura,
Mu kama shiɓa da bankaura,
A ɗauko Igwa mu ɗau gora,
          A kanmu ake daka ta.

16.     Irin rigimar da ke Delta,
Ta ƙare babu algaita,
A ba su kuɗi su sai mota,
Tukuici han na ragaita,
          Su zub da jinin maƙwabta.

17.     A ce musu ‘yan biɗan ‘yanci,
A ba su dukan muhimmanci,
Da albashi na sagarci
Su ƙasura sui ta shashanci,
          Batunsu ake mutunta.

18.     Arewa batunmu ƙarya ne,
Da mui magana a ce mu ne,
Jininmu zubansa daidai ne,
Batun diyyarmu shirme ne,
          Wa ka biyan ƙazanta?


19.     Mafarin yin fa’addanci,
Ƙasa ta halasta zalunci,
A dinga mutunta cin hanci,
A ja ɗamarar ƙabilanci,
          Bala’i ya rufe ta.

20.     Idan aka fara ha’inci,
          Hana wa ɗiyan ƙasa ‘yanci,
Da ɓangarci da bambanci,
Da gardancin aƙidanci,
          Ƙasa tuni an kashe ta.

21.     Matasa an ka wa fanho,
Su zabura ce kakai shaho,
Suna kuwa suna eho!
Su jikkita babu mai hoho,
          Kisan kai an halasta.

22.     Abinda ka ba ni mamaki,
          A ofis can wajen aiki,
Kujera ta zamo gunki,
A kan ta a ɗora yin raki,
          Na kare martaabarta.

23.     Saboda a nan ake sata,
A tara kuɗi a ƙasaita,
A jefa ƙasa ga ragaita,
Talauci duk shi dame ta,
          Ta nakkasa gun maƙwabta.

24.     A sa marashi da mai samu,
Suna kwana cikin gammu,
Matasa har da mai gemu,
Su takura ba wurin kamu,
          Ƙasa duka an fusata.


25.     Matasa an ka cuce su,
Ga ilmi an ka ƙware su,
Ga aiki babu mai ba su,
Siyasa taf farauto su,
          A dole su je kiran ta.

26.     Da nan aka sa su ‘yab banga,
A ba su giya su sha daga,
Su gigice da damaga,
Fasadi ga shi an shirga,
          Ƙasa sama har ƙasanta.

27.     Ganin an rena ƙurarmu,
A banzantar da wayonmu,
A ta da faɗa ƙasashenmu,
Saboda a karya ƙarfinmu,
          Da ganganci da cuta.

28.     A ofis an ci ƙarfinmu,
Siyasa an galale mu,
Yawan jama’a a cuce mu,
Muƙamai an ka kore mum,
          Kujerin an ka ƙwata.

29.     Muna kallo mu zan leɓo,
Tufanmu kaɗai ka yin raɓo,
A kwashe zuma mu ɗan soɓo,
Da an gamu sai a ce, Jaɓɓo,
          Ina Mudi da Auta?

30.     A nai muna izgilin raini,
Ganin an samu zamani,
Siyasa mai baƙin muni,
Da mai gemu da mai huni,
          A tabbata an talauta.


31.     A yau mabiya ga alƙibla,
Musulmi masu yin salla,
Ake ta yi wa kisan gilla,
Saboda muna faɗin Allah,
          Ka tsari mai nagarta.

32.     Siyasa ce gidan tasku,
Zaman ciki babu dottaku,
Da mai rawani da mai diku,
Kwaɗai ya rufe ƙwaƙwalwarku,
          Ku zan manyan macuta.

33.     Ku jefa ƙasa a Basasa,
Tsaro ya zamo barafasa,
Ta’addanci ya bunƙasa,
Dukan tsarinta an rusa,
          Musiba ta rufe ta.

34.     Haba jama’a mu hankalta,
Ƙasa ta ƙare muzanta,
Zaman tuni an ga wallenta,
Mutane sun galabaita,
          Suna ta shirin barin ta.

35.     Ku dubi irin halin maiki,
Da yag gamu shi da gauraki,
Wurin taɗi da hankaki,
Gaban jimina yana raki,
Sanin ya ɓarka cuta.

36.     Biri in yai kuren reshe,
Dabaru nasa sun rushe,
Irin tsololuwar baushe,
Da ya faɗo yana mushe,
          Su angulu za su zabta.


37.     Musulmi wanda yad dace,
Shahada langaɓunai ce,
Ya sha romo ya ɗau kwalce,
Da likkafaninsa zai zarce,
          Cikin murnan zuwan ta.

38.     Kisa bai ƙare Imani,
Zaman rai na da zamani,
Akwai shi a kowane ƙarni,
Da shi aka maganin raini,
          Shiga Aljanna kyauta.

39.     Ganin mu za a rinjaya,
Ake yin martanin gayya,
Na ƙone yara har manya,
Da rodubulo a kan hanya,
          A firgita masu bin ta.

40.     A turbuɗe bom ƙasashenmu,
Ya karkashe ‘yan uwan namu,
A bi mu ana ta kamo mum,
Da hujjoji na zarginmu,
          Da an ka shira na cuta.

41.     Mutum da gidansa an bi shi,
Ya yunƙurto a harbe shi,
Ya miƙa wuya a ɗaure shi,
A runtuma gun iyalanshi,
          Da yin fyaɗe da ɓata.

42.     Gabanka a harbe tsohonka,
Walau a kashe iyalanka,
A sa ‘ya’yanka yin shirka,
A sa ka rutsi na cin fuska,
          Da tun tuni an hukunta.


43.     Muna ji Borno ta watse,
Gaba ɗaya Yobe ta motse,
Na Bauchi gabansu ya katse,
Ƙasar Adamawa ta gintse,
          Filato an kashe ta.

44.     Kano ta sha harin girshi,
Kaduna karen ka wa habshi,
Jahar Nasarawa sai nishi,
Abuja kwatsam yake tashi,
          A kama gudu a kwalta.

45.     Gusau a wajen manomanta,
Kaza sashen makyayanta,
Bala’in ya malale ta,
Rahotannin musibunta,
          Abin sai an taƙaita.

46.     Ƙasar Katsinanmu an yi hari,
Da gawakki gudan tari,
Abin ya kasance labari,
Hukuma ba ta inkari,
          Da tunkarar macuta.

47.     A Sakkwato an yi mai muni,
Awon ya furce mizani,
Zuma sun harbi mai gani,
Kare ya shuri ƙur’ani,
          Ruwa su kashe masunta.

48.     Ina kuka zacci zai tsere?
Ƙasa can da tana kore,
Hamada ta bi ta share,
Ina wani wanda zia more,
          Zama ya ci gajiyarta?


49.     Maƙarƙashiya shirin manyan,
A tunkuɗa yara jayayya,
Da son a ga masu rinjaya,
A ba kowa makamayya,
          Su karkashe kai da wauta.

50.     Tammat kun ji ƙarshen ta,
Maƙarƙashiya ga sunanta,
Alu ɗan Bunza yay yi ta,
Masar aka nome ƙwazonta,
          Kano aka kai tuƙinta.

Post a Comment

0 Comments