Ticker

6/recent/ticker-posts

Dangantakar Harshen Hausa Da Nufanci: Nazarin Tasirin Hausa A Kan Harshen Nufanci (3)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com
NA
KUDU MUHAMMAD SALIHU

BABI NA UKU


DANGANTAKAR HAUSAWA DA NUFAWA


3.0 Shimfid’a


A wannan babi na uku za a duba dangantakar Hausawa da Nufawa yadda suka yi tasiri a kan juna da ma’anar dagantaka da fuskokin dangantaka irin na addini kamar almajirci ko neman ilimi da malanta da jihadi (wato tutar sarautar Shehu) da dangantaka ta fuskar fatauci da tarihin zuwan Turawa da yak’insu a Nijeriya da dangantaka ta wasu al’adu irin su kayan k’walamar Bahaushe  na gargajiya kamar tuya k’osai da guguru da dak’uwa har ma da gyad’a. Akwai kuma sana’ar d’inki da nomad a kamun kifi da sabulun salo da daddawa da k’ira  na bak’i da farin k’arfe da auratayya kamar bikin aure da kuma bikin haihuwa a k’arshe kuma a nad’e babin kamar yadda aka yi wa sauran babuka.

3.1 Dangantakar Hausawa da Nufawa


A duk lokacin da aka yi maganar dangantaka tsakanin al’umma biyu ko k’abilu guda biyu to kuwa ana nufin tsarin zaman wad’annan al’umma kamar abin day a shafi tasiri ta hanyoyi daban-daban. Tarihi da hasashen masana da marubuta sun nuna mana cewa akwai dangantaka ta tasiri tsakanin wad’annan al’umma (wato Nufawa da Hausawa musamman abin da ya shafi yak’i da kasuwanci da sana’o’i iri daban-daban kamar su noma da d’inki da tuya k’osai da guguru da dak’uwa da gyad’a da kamun kifi da sabulun salo da k’ira har ma da auratayya da dai makamantansu.

Haka kuma lamain dangantaka tsakanin Hausawa da Nufawa ba ta tsaya kawai a kan wad’annan abubuwa da muka ambata a sama, ya ta’allak’a da wasu al’adu iri daban-daban da kuma yanayin sanya tufafi da kayan abinci irin na gargajiya da nad’in sarauta da makamantansu. A game da abin da ya shafi abincin Hausawa irin na gargajiya kuwa, ya sami tasiri a kan Nufawa irin su zogalai da tafasa da yakuwa da waina ko masa da sauran kayan abinci makamantan wad’annan.

Bugu da k’ari, akwai kuma dangantaka ta fagen sarautan gargajiya inda a kan yawancin sunayen masu sarauta sun samo asali ne daga al’ummar Hausawa wanda a kan yi wa wasu kwaskwarima don su dace da harshen amfani, akwai kuma wasu da ake d’aukowa kai-tsaye daga harshen Hausa zuwa harshen Nufe. Misalin wad’anda aka d’auko kai-tsaye cikin harshen Nufe kamar Waziri da makama, da marafa da Galadima da Jarma da makamantansu. Wad’anda aka yi wa kwaskwarima kuwa sun had’a da mayak’i a maimakon mai yak’i da dai makamantansu da yawa.

 

 

3.2 Ma’anar Dangantaka


Dangantaka na nufin kwatanta wani abu da wani abu domin a ga kamanninsu. Kowane al’umma su na da al’ada wanda ya dogara da shi kuma yake alfahari da shi, haka kuma suna da hanyoyi daban-daban da suke bi wajen aiwatar da su da kuma irin sunaye da suke k’iran wani abu cikin al’adunsu.

Dangantaka dai yana aukuwa ne tsakanin al’ummomi guda biyu a sanadiyyar wurin zama inda wani kan sami tasiri a kan wani ta hanyar harsunan da suke amfani da shi da halayya ko al’ada ko huld’a ta kasuwanci ko fatauci da dai wasu abubuwa da su ka yi kama da wad’annan na abin da ya shafi al’amuran yau da kullum da ke faruwa tsakaninsu har ma da banbancin ra’ayi da makamantansu.

3.3 Fuskokin Dangantaka


Dangantaka kamar yadda muka sani, ya na faruwa ne tsakanin al’umma biyu ko k’abilu guda biyu yayin da d’ayan k’abilan zai sami tasiri a kan d’aya. Ta haka ne muke so mu duba wannan dangantaka tsakanin Hausawa da Nufawa yadda suka yi tasiri a kan juna a fuskoki daban-daban. Daga cikin fuskokin dangantaka da za mu yi la’akari da su, inda wad’annan al’umma suka yi tasiri a kan juna sun had’a da addini da fatauci da almajirci ko neman ilimi da malanta da jihadi irin sarautar tutar Shehu da zuwan Turawan mulkin mallaka da yak’in Turawa da kuma wasu al’adu irin na gargajiya daban-daban da suka had’a da kayan k’walamar Bahaushe irin na gargajiya irin su tuya k’osai, da guguru da dak’uwa da gyad’a da d’inki da noma, da kamun kifi da sabulun salo da daddawa da k’ira da auratayya irin su bikin aure da kuma bikin haihuwa da makamantansu.

3.3.1 Dangantaka ta Fuskar Addini


Addini wata hanya ce ta bauta inda mutane ke bi wajen ganawa da ubangijinsu. Dangantaka ta addini tsakanin Nufawa da Hausawa ya faru ne a sanadiyyar wurin zama, sannu a hankali su ka fara ko soma kallon yadda kowannensu ke gudanar da addini, ta hanyar bauta da yanayin bauta da kuma wanda ake yi wa bauta.

A sanadiyyar wannan hali ne Hausawa suka sami tasiri a kan Nufawa domin kuwa yanayin addini da hanyar bautarsu, sun zo iri d’aya wanda idan bak’o ya shiga cikinsu, zai kasa ganewa da al’ummu guda biyu ne suke sai dai a dalilin jin harsunan da suke amfani da shi da dai makamantansu.

  1. Almajirci/Neman Ilimi


Lamarin almjirci ko neman ilimi abu ne mai yalwa tsakanin Hausawa da Nufawa domin a cikin tsawon lokaci da suka wuce, Nufawa da yawa sun sami kansu a hannun Hausawa wajen neman ilimi. Kodayake, akwai malamai a k’asar Nufe wad’anda suka yi tashe a hark’ar ilimin addinin musulunci musamman abin da ya shafi fik’hu sai dai Nufawa sun aikata wani abu irin abin da Hausawa ke fad’a a cikin karorin maganganunsu kamar haka: “ciniki nake ban san na gida ba”.

Malam Lawal wani malamin zaure ne wanda na yi zama da shi a ranar Talata 14 ga watan Maris, 2017 ya ba ni haske a kan dangantakar Hausawa da Nufawa ta fuskar addini, inda ya ce, wannan dangantaka ya faru ne tun shekaru aru-aru da suka wuce tsakanin wad’annan al’umma domin shi karan kansa ya sami wannan tasiri na Hausa a kan harshen nan nasa (wato Nufe). Abin nufi a nan kuwa shi ne, ya sami ilimin addini ne daga garin Zariya  wanda ya ambaci wasu malamai da yawa kamar su Malam Al-Hassan Babanna da Malam Umar da kuma Malam Minin duk sun yi karatu ne a k’ark’ashin malaman Hausa inda wannan harshe na Hausa ya sami tasiri a kansu domin wajen koyar da karatunsu, sukan yi ne da harshen Hausa.

Haka kuma, a cewarsa, akwai wani malami mai suna Sheik Abdulk’adir Zariya wanda ya bayyana da cewa wannan malami Banufe ne daga garin Agaie k’aramar hukuma ne a jihar Neja ya yi karantunsa ne a garin Zariya kuma ya ci gaba da zamansa a can wanda har zuwa gobe zuri’arsa suna nan a Zariya wanda idan ba a san asalinsu ba, sai a d’auka cewa Hausawa ne su amma a hak’ik’anin gaske ba Hausawa ba ne dan haka, irin wannan zama da karatun da suka yi a wancan lokacin ne ya sa harshen Hausa ya sami tasiri a kan Nufawa da dai makamantansu.

 

  1. Malanta


Malanta kamar dai yadda muka sani, za a iya bada bayani a kanta game da yin duba ko kallon hark’ar malanta ta fuskoki guda biyu kuma wad’annan fuskokin sananne ne ga kowane mutum da ke yin rayuwa cikin wad’annan al’umma guda biyu wato Hausawa da Nufawa.

Idan aka ce malam, nufin kowane mutum ne masani walau a fagen Islama ne ko kuma a gefen boko. Amma kuma ga Bahaushen fahimta, akwai malami mai koyar da karatun Alk’ur’ani akwai kuma malamin duba ko tsibbu dukkan su kuma suna amsa sunan malam.

Don haka, idan muka wad’annan malamai sunansu malam a bayyane amma akwai banbanci tsakaninsu domin kuwa babu inda mutum zai amsa sunan malam kuma yana had’a malanta da k’ulle-k’ulle na k’arya wanda ya sa’bawa karantarwa irin na malamai ko kuma abubuwanda Allah mad’aukakin Sarki bai yarda da su ba. (Lawal 14/03/2017).

A k’arshen bayaninsa cewa, ya rage ga mai neman gaskiya ya zad’i d’aya daga cikin wad’annan malaman don ya sami dogarowa a kansa saboda tsirar duniya da kuma lahira.

 

iii. Jihadi (Sarautar Tutar Shehu)

A wannan yanayi, idan aka yi maganar jihadi, mutane sukan d’auka cewa yak’i ne ake magana a kai. Jihadi a wannan hali, shi ne jaddada addinin musulunci da Shehu Usman ‘DANFODIYO ya yi tare da muk’arrabansa a duk yankunan k’asar Hausa da Nufe har zuwa Ilori. A wannan lokacin, ya sami taimakon Abdullahi Fodiyo da kuma d’an nasa Muhammadu Bello wad’anda sune suka jagoranci Sakkwato da Gwandu wato Abdullahi ne ya d’au tutar Gwandu inda Bello kuma ya d’au tutar Sakkwato Shehu kuma ya ci gaba da koyarwa da fad’akarwa a Sakkwato har lokacin mutuwarsa a shekarar 1817. Bayan an tabbatar da cikakken iko a jihar arewa, sai Fulani suka soma fad’ad’a jihadi zuwa sauran yankunan k’asar nan inda a lokacin ne yak’i ya ‘barke tsakanin sarakunan Nufe, kwatsam Malam Dendo ya shigo da tutar jihadin Shehu kuma ya shawo kansu. (John Hatch 1971).

Dendo ya sami labarin Abdulrahman Bajichi Banufe ne kuma malamin addini inda yake gudanar da wa’azi cikin al’umman Nufe, wannan ya nuna akwai musulunci a k’asar Nufe gabanin jihadin Shehu amma kuma mutanen Nufe suna gwama addinin da maguzanci wanda aka nuna cewa Abdulrahman ya sami goyon baya Dendo wajen jaddada addinin musulunci a k’asar Nufe.

Sannu a hankali, bayan Dendo ya sami cimma burinsa. Da malam Dendo ya koma ga Allah, babban d’ansa ya mayar da masarautar daga inda yake a garin Raba zuwa garin Bida kuma shi ne Sarki na farko a k’asar Nufe k’ark’ashin sarautar tutar Shehu. Daga nan kuma sai sarki Abubakar Masaba wanda Turawa suka sha gwagwarmaya da shi har zuwa lokacin da ya fita a garin irin fitar kusu (Awwal).

Maishanu (2006) a k’aulinsa cewa Abdulrahman Malami ne  cikin al’umman Nufawa ya sami taimakon Dendo yayin da yake k’ok’arin fad’akar da su kan abin da ya shafi addinin musulunci.

3.3.2 Dangantaka ta Fuskar Fatauci


Fatauci hanya ce ta amfani da dabbobi irin su rak’uma da dawakai da jakuna wajen taafiye-tafiye daga wani wuri zuwa wani wuri don neman abinci. Mafi akasari, Hausawa suna amfani ne da rak’uma. A irin wannan yanayi, a kan yi amfani da su wajen d’ora musu kayan sayarwa zuwa k’asashe ko garuruwa inda za su sayar da kayan. A kan yi amfani da wad’annan dabbobi wajen kwasan kayayyakin gona wa manoma inda motoci ba za su iya zuwa ba. Kodayake a wannan lokaci babu maganar motoci dabbaobi ake amfani da su a k’asar Hausa tamkar abin hawa kuma fatake sukan yi dogon tafiya daga k’asa zuwa k’asa ko gari zuwa gari.

Har zuwa wannan lokaci, akwai fatake da suke shigo k’asar Nufe da kewaye don gudanar da hark’ar fataucinsu. Daga irin kayan gona da wad’annan fataken suke d’orawa bisa rak’uma sun had’a da shinkafa da dawa da gero da dankali da rogo da dai sauran kayan gona da ake nomawa.

Kenan, dangantaka ta fatauci tsakanin al’ummar Nufe da kuma al’ummar Hausa sun fara ne tun lokaci mai tsawo, kuma ya taimaka ainun wajen tabbatar da huld’a da kuma wanzar da zaman lafiya tsakanin al’ummun.

3.3.3 Dangantaka ta Tarihin Zuwan Turawa


Abin sha’awa ne k’warai ga mutumin Nijeriya ta arewa a yanzu ya sami karanta tarihin halin da Turawa suka zo suka sami k’asan nan shekaru aru-aru da suka wuce.

Wannan zai jawo hankalinmu mu karanta wasu littattafai kamar zuwan Turawa Nijeriya ta arewa kan irin halin da aka sami wasu shugabanni wad’anda suka zo bayan Shehu Usmanu ‘DANFODIYO da almajiransa a kai, game da yadda suke tafiyar da al’amarin mulki wanda Shehu da Muhammadu Bello suka shirya musu, wanda kusan za a iya ce a dalilin kaucewan nan tasu Allah kuma ya dubi rashin kwanciyar hankalin jama’a a k’asar nan ya turo Turawa domin jama’a su sami zaman lafiya da kwanciyar hankali. Don kuwa, tun kafin a san komai game da zuwan Turawa a k’asar Hausa, Mujaddadi Shehu Usman ‘DANFODIYO ya fad’a a cikin wasiyoyin da ya yi wa jama’ar k’asan nan cewa, zuwa akwai wasu mutane da za su zo.

Mani, (1956: 38-45) ya ce, Turawan da aka turo binciken yanayin k’asar Hausa kowannensu ya yi iyakacin k’ok’arinsa ya kuwa kawo cikakken bayanin wad’ansu sun kawo nasu k’arshen watan Yuli, wad’ansu kuma a farkon watan Agusta 1900. Daga ainihin irin abin da mutanen nan suka samo ne gwamna ya gane lallai ba zai yiwu gareshi ya kafa hedkwata a k’asashen da ke can gaba k’warai na k’asan nan ba. Domin duk kogunan da suka tashi daga kwara sai ka tarar  ba su nufi can wajen ba, ko kuma sun nufa sai ka ga ba tare da wani abin amfani ba. Kogin gurara dai aka ga zai bada wahala ainun, domin kuwa bai yiwuwa a shige shi da jirage, saboda duwatsun da ke warwatse cikinsa ko ina, tun ma ba a wani wuri na nan ba, kamar mil talatin daga kogin kwara. Wannan wuri da duwatsu ya ke, bargaja! Kuma idan ruwa ya zo, igiyar ruwan gurara ta cika k’arfi k’warai har ma ba zai yiwu jirgin ruwa ya yi tafiya a ciki ba. In kuma aka bari sai da rani, to, a lokacin ba ruwa duk ya janye.

Ganin haka, sai Gwamna Lugga ya ce watak’ila wajen wushishi d’in nan, shi ne zai fi dacewa da yin sabuwar hedkwata. Saboda haka, da ya ga ruwa ya samu cikin watan Yuli, sai ya sa aka kwashi gidajen katakon da aka kawo, aka bi ta ruwa da su, aka sauk’e su a wushishi. A wannan lokaci, Gwamna Lugga ba shi da kwanciyar hankali domin duk lokacin da aka tashi kai wad’ansu keya daga Lokwaja zuwa wushishi ta cikin ruwa, in dai har Bida da Kwantagora za su sami labari, to sai su tarya su wazgi rabonsu a ciki.

Hasali ma, ganin yadda Kwantagora da Bida ke yi, Turawa suka gane lallai ba a yi maganar kafa sabuwar hedkwata ba, in ba an daidaita da su ba. Da aka gano kwashe kayan nan sarai, sai Gwamna Lugga da wani Bature mai suna Likita Langley, wanda ya ke shi ne shugaban likitocin Nijeriya ta arewa a lokacin da shugaba Fidaburdi, Mista Taglasome, da Baturen Safiyo Mista Scott da Kaftin Abadie, suka taso daga Lakwaja ran 19 ga watan Janairu 1901, suka d’unguma sai wushishi. Da suka bi kogin suna tafe suna dubawa, a lokacin nan ne suka gane ashe dai kogin cikin wani k’aton kwari yake. Gashi kuma cike da duwatsu mulmulallu. Can gaba da wushishi kamar kilomita goma abin yafi wuya ainun, tun ma ba wajen jimu ba. Saboda haka sai Turawa biyu Mista Taglesome da Mista Scott suka ratsa daji suka tasamma wushishi daga wannan wurin mai wuya, domin su gani ko abin zai fi sauk’i ta can.

Bayan sun ratsa wurin nan, Turawan nan suka shaida wa Gwamna Lugga suka ce, ko da yake wurin nan mai wuyar al’amari ne duk da haka ana iya samun wurin da za a iya shimfid’a hanyar jirgi. Nisan wurin kuwa, kamar kilomita arba’in (40) kuma ana iya gama aikin a k’alla a shekara cif. Kai abu dai ya zama babu yadda za a yi a sami tashi a koma sabuwar hedkwatar da ake son yi, tilas sai an kai bazara ta 1903. Sa’annan kuma Turawa suka ga lallai ko an yi hanyan nan, to tilas kuwa kowace shekara sai ruwa ya yi mata ‘barna, koma ya tun’buke ta d’ungum. Don haka, wajen kula da ita zai yi ta sa a kashe kud’i masu yawa kowace shekara. Su kuma kayan da aka kwaso aka kawo wushishi za su lalace kenan, domin ko a lokacin ma wad’ansu har sun fara lalacewar kafin a somi kawo su sabon wurin nan. Ga shi kuma ba shi yiwuwa a kwaso su tilas sai an yi hanyar jirgi. Kafin kace kwabo, shugaban aikin nan na Fidaburdi ya fara aiki. Shi kuma Gwamna Lugga ya tashi ya bi ta Bida. Domin ma ran 19 ga watan Maris duk al’amarin za’ben sabon wurin nan an gama shi sarai.

A game da sha’anin mulki kuma, duk shekaran nan ta farko an yi ta ne a kan shirye-shirye. Hasali dai, k’asashen da Turawa suka aza hannuwansu a kansu lokacin nan kamar su fara ne. daga cikin taron nan har da Ilorin da Kaba da tsakiyar k’asar Neja da k’asashen kudu da Biniwai da k’asashen arewa da Biniwai da k’asar Nufe da Bargu da Kwantagora sa’an nan kuma da k’asar Zariya. Kuma wad’anda ake sa ran za su shiga hannu ba da dad’ewa ba, sune kamar su Basa da Muri domin sun ga alama su ma za su yi wa Turawa maraba. Daga nan kuma sai Bauchi da Yola.

Musamman abin da ya sa Turawa ke ta alla-alla su sami sanin yadda k’asashen nan da ke gabas suke, saboda zaton watak’ila duwatsun nan na su, za su sa a sami ma’adanai da yawa a can kuma wuraren suna da alamun lafiya idan an zauna.

Ganin irin wannan hali da mutanen k’asan nan har ma da wad’ansu da ke zuwa daga kudu ke ciki, shi ya sa Gwamna Lugga ya ce ba abin da ke warkad da cuta, sai an sami Turawan mulki wad’anda suka fahimci jama’ar k’asar nan sosai. Watau irin Turawan nan wad’anda kowane irin dungu aka yi musu zasu gane shi nan da nan musamman idan sun fahimci harshen mutanen. Wanda duk ya fahimci harshen jama’a ya zama d’an uwansu kenan kuma suna iya yarda da shi fiye da duk yadda ake zato.

A cikin shekaran nan guda ta farko zuwan Gwamna Lugga, watau daga 1900 zuwa 1901, Baturen da ke kula da k’asashen Binuwai na arewa, Mista Hewby ya bada labarin irin k’ok’arin da ya yi, ya sa aka kafa kotu a kusan kowane babban gari da ke k’ark’ashinsa. Ya ce koyaushe ana sama da shi irin shari’o’in da aka yanke kusan dukansu kuwa babu son rai a ciki sai an tabbatar ds gaskiyar magana sa’annan a yanke hukunci.

Mataimakin Razdan na dori ya ce, ai kasuwar bayi ta mutu, ta zama abin tarihi. A wajen shari’a kuma, ana ci gaba da yadda ake bin hanyar gaskiya da adalci a sabon d’akin shari’ar da aka kafa, saboda garin sojoji sun kau da jiki a fagen fama da yawan tashe-tashen hankula a wannan k’asa, kuma duk da haka, zaman lafiya ya k’aru hankalin jama’a yana ta k’ara kwanciya fiye da da.

  1. Yak’in Turawa


Mani, (1956) cewa ya yi, a karo na farko, Turawa sun fara da Bida yayin da suka dankwafar da su, bayan d’an lokaci k’ank’ani sai Gwamna Lugga ya sami labarin Kwantagora da Bida suna had’a kansu har ma da sauran k’asashen fulani wai zasu aukawa Turawa da yak’i. Da jin haka, sai suka shiga gyaran d’amara, har suka sami karo da mayak’an nan. Yankin k’asar da ya kama tun daga wushishi har zuwa kamar kilomita ashirin duk ya zama yana hannun Turawa. Ana nan cikin wannan hali, sai Gwamna Lugga ya umarci jama’arsa  da su gyara masa hanya ta ruwa cikin kogin Kaduna. Wajen gudanar da wannan aikin ma, mayak’an Kwantagora da Bida suka ta da tarzoma inda Turawa suka sami nasara a kansu, suka kore su fatafata har gida. Baturen sojan da ya kori mayak’an Bida ya yi k’wazo k’warai domin daga shi sai mataimakansa mutum talatin rak suka yi k’oran nan. Kad’an ya rage Baturen nan ya kama Sarkin Bida da hannunsa. Amma saboda mummunan raunin da suka yi wa Baturen ne ya sa bai sami damar kama sarki ba.

Jim kad’an sai sojojin da suka tafi kai gudunmawa k’asar Gwanju suka dawo, Gwamna Lugga ya ce musu bismilla ga wani aiki ya taso inda ya ce da su ya na so su ci Kwantagora suka yi harama suka ‘bullawa garin Kwantagora ta fuskar arewa, sun yi haka ne wai kada sarkin ya bi ta Sakkwato ya gudu. Kafin k’iftawa sai sarki ya guda sojojin kuma suka bi shi ya bar bayi da fadawa a baya, su Turawan suka tsayar da sojoji a nan dan gudun masu tada k’ayar baya su kuwa suka wuce zuwa Kaduna. A kan hanyar tafiya Kaduna ko ina suka kai sai mutane su rinka yi musu maraba suna gud’a da raye-raye wai an raba su da Nagwamatse kusan galibin k’auyuka na kusa kwantagora duk sun zama kufai a lokacin saboda yawan hare-hare da kamun bayi.

Bayan Turawa sun koro shi, daga baya sai suka biyo shi, likita Miller ya ce suna isowa Zariya daga Kano inda aka koro su, sai suka gane lallai sun fad’a cikin babban tarko domin su na isowa, sai suka iske sarkin Sudan ya kewaye Birnin Zariya da mayak’ansa ya kuwa nemi izini daga kawunsa sarkin musulmi da kuma sarkin Kano ya dai yi haramar fad’a wa garin da yak’i don ya ci shi. Mayak’an da ke tare da sarkin Sudan duk k’asar Hausa kowa ya san da zamansu. Saboda tsananin jaruntaka tasu zarumai ne ainun. Da likita Miller ya ga haka, sai ya yi hanzari ya yi ya je wurin sarkin Zazzau shi kuma sarkin a lokacin ya aikawa Gwamna Lugga da takarda ya na neman a taimake shi, da zaman likita, ya cewa sarki kada ya ji komai tun da ya riga ya aika wa Gwamna Lugga, ya tabbata Lugga ba zai ta da alk’awari ba muddin dai ya d’auki alk’awarin taimaka ma shi, zai kuwa taimaka iyakacin k’ok’arinsa.

Yadda Turawa suka sama sarkin Sudan da hannunsu kuwa, abu ne mai ban takaici k’warai domin kuwa lokacin da ‘yan Turawan nan su kad’an suka tinkaro inda sarkin Sudan ya ke, watau a sansaninsa su da kansu sai da suka tsaya cik suka tambayi junansu suka ce shin kuwa za su iya yin kome da dubban mutanen nan da ke tare da sarki? Ko kasan halin soja abin jan hankali ne gare su. Nan da nan Mista Abadie da wani Bature mai suna Mister Peter suka za’bo gargannun sojojinsu ‘yan kad’an suka rufo idanunsu ba su zame ko tsaya ko’ina ba sai daf da wata k’atuwar rumfa inda suka tabbatar ita ce rumfar sarkin Sudan suka mamaye shi suka buga masa ankwa kafin dubban mutanen nan su kai ga zaburowa, sai Turawa suka sa wani Bahaushen soja daga cikinsu ya yi shela ya shaida wa mutane su fa ba fad’a ne ya kawo su ba, wanda dai suke neman kamawa ga shi sun kama shi fak’at.

Kano da Sakkwato da Zariya sun bi Turawa lokacin da Gwamna Lugga ya gama da Kano da Sakkwato, da ya dawo Zariya, da yardar mashawarta sai aka tabbatar da Aliyu D’ansidi ya zama sarkin Zazzau.

Ku tuna fa jama’a, a lokacin nan k’asan nan babu wanda ke zama lafiya domin lokaci ne na kama karya, wanda ya fi k’arfi kuwa shi ne wanda zai kama mara k’arfi ya karya shi. Don haka, Turawa suka sami maraba daga wajen marasa k’arfi a k’asan nan ta Hausa har ma su Turawa suna ganin kamar dai duk ‘yan yak’e-yak’en da suke yi suna yin su ne da wad’anda suke ‘bata k’asa ne kurum. Kusan kowace k’asa ka je kuwa, sa ka tarar da mutane suna kuka game da irin mungun abu da masu mulkinsu ke yi musu.

Ya sake jaddada (Mani) da cewa, wani muhimmin abu kuma shi ne karin maganan nan da Hausawa ke yi inda suke cewa, “da d’an gari a kan ci gari”. Wannan gaskiya ne domin duk sojojin da suka yak’i k’asar Hausa, Hausawa ne zalla, daga mutumin Kano sai na Sakkwato sai na Katsina da dai makamantansu. Turawa suka rik’a koyawa sojoji dabaru iri daban-daban daga ciki, sukan ce musu duk garin da suka je kada su kuskura su sha ruwan rijiyarsu wadda ba su ga suna amfani da ita ba. Wato don gudun kada su zuba musu guba a ciki wanda idan su ka sha za su mutu.

Turawa ma da kansu sun za ta lallai yak’in da za su yi a Kano, zai fi na kowa ne gari wuya, don haka suka fara tara babbar runduna inda suka sami sojoji fiye da dubu. Ranar 29 ga watan Janairi, 1903 ne kanar Morland ya shugabanci wad’anda za su yak’in Kano. Duk irin sojojin da aka yi wa rauni sai a kai shi k’aura a nan aka sa Bature guda mai kula da su sauran sojojin kuma suka tasamma Sakkwato, ita ma a lokacin ta na tsaye a kan shirye-shiryen fad’a da Turawa. A cikin ranar Juma’a 7 ga watan Maris suka bar Kano suka tasam ma Sakkwato tare da Kaftin Abadie a lokacin nan ne ya bar Likita Cargill ya zama razdan na Kano, tafiyar da sojoji suka yi daga Kano zuwa Sakkwato sun sha d’ari domin lokacin hunturu ne tun ma ba da dare ba, sai suka yi ta fama da rashin lafiya musamman ciwon hak’ark’ari wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji hamsin da biyu (52).

3.4 Dangantaka ta Fuskar Wasu Al’adu


Kamar yadda muka sani a game da al’adun Bahaushe yadda yake yin tasiri a kan wasu al’ummu daban-daban na k’asan nan, al’ummar Nufawa ma suna da irin wad’annan al’adu. Idan aka duba dangantakar dake tsakanin wad’annan al’umma ta fuskar wasu al’adunsu, za a ga cewa akwai kamanceceniya dake tattare cikin al’adun, haka kuma akwai wasu al’adu da suka ke’banta ga Nufawa kad’ai wanda a sanadiyyar tasiri suka koma kamar na Hausawa ne.

Don haka, babu abin da zai fayyace mana tsakanin al’adun wad’annan al’umma face tarihi daga bakin masana tarihi ko kuma wad’anda suka yi rayuwa na tsawon lokaci kuma suka san yanayi da sigogin al’adun wad’annan al’umma guda biyu.

Akwai buk’atar nuna wad’annan al’adu da za a yi magana a kansu na abin da ya shafi ma’anoninsu da kuma dabarun aiwatar da su har ma da amfanoninsu. Wad’annan al’adu kuwa sun had’a da kayan k’walamar Bahaushe na gargajiya irin su k’osai da guguru da dak’uwa da gyad’a. Haka kuma akwai irin su d’inki da noma da kamun kifi da sabulun salo da daddawa da k’ira na bak’i da farin k’arfe har ma da sana’ar karau (glass work) da makamantansu.

3.4.1 Sana’ar Kayan K’walamar Bahaushe na Gargajiya


A cikin tsawon lokaci da ‘yan adam ke rayuwa a doron k’asa, an ci karo da sana’o’i da al’adu iri daban-daban wad’anda a hak’ik’anin gaskiya, kowane d’an Adan yakan yi sha’awar d’aya daga cikin wad’annan abubuwa musamman al’ummar Hausawa.

Tarihi ya nuna cewa, wad’annan abubuwa suna da matuk’ar amfani cikin al’ummar Nufawa da kuma Hausawa har ma sauran al’ummar k’asar nan. An sami hasken bayanin ne daga wata mata mai suna Hajiya Ladidi a anguwar fogun k’aramar hukumar Bida ta Jihar Neja a ranar Lahadi 25 ga watan Yuni, 2017, a cewarta, kayan k’walamar Bahaushe na gargajiya a asali ma, wad’annan kayan k’walamar, an san su ne wajen Nufawa domin kuwa sune ke sarrafa su kuma su sayar. Kashi tamanin cikin d’ari na masu wad’annan sana’a Nufawa.

  1. Sana’ar Tuya K’osai


K’osai sana’a ce ta sarrafa wake don samun abin lasawa (wato ciyarwa). Ana kuma samun abin buk’atu na yau da kullum. Tun da dad’ewa al’ummar Nufawa ke sana’ar k’osai amma ta hanyar gargajiya kenan tun kafin zuwan Turawa. Hanyar gargajiya a nan shi ne amfani da dutse wajen nik’a domin bayan zuwan Turawa aka samu hanya ta zamani wato injin nik’a.

Dan haka, dabarun da aka bi wajen sarrafa wake domin a mayar da shi k’osai guda biyu ne kamar yadda bayani ya nuna a sama, na d’aya shi ne hanyar gargajiya wato yin nik’a da dutse. Abin da ke faruwa a nan shi ne, idan aka zuba wake cikin turmi sai a zuba ruwa sannan a rink’a daka shi da ta’barya har ‘bawonsu ya fita idan alama ya nuna na fitar ‘bawon waken, abu na gaba sai a wanke shi tsab daga nan kuma sai a fara nik’a shi da dutsen nan na nik’a har ta nuk’u.

Hanya ta biyu kuwa ita ce hanya ta zamani wato amfani da inji wanda aka samu a sanadiyyar zuwan Turawa. Ana surfa waken da inji kafin a jik’a cikin ruwa a wanke, ana kuma zuba cikin turmi a daka domin a fitar da ‘bawon kamar yadda bayani ya gabata bayan an wanke sai kuma a nik’a ta.

Bayan an gama da wad’annan d’awainiya, sai a sami tukunyan tuya k’osai da murhu da icce da kuma man gyad’a. Bayan an hura wutar, sai a aza tukunya a zuba mai a ciki idan ya yi zafi sai a nemi lauciya na nik’a tuwo a murd’a nik’ak’k’en waken ana amfani da gishiri da albasa da ruwa sannan a samo cokali ko ludayi a fara d’ibawa ana sakawa cikin tukunya don soyawa. Idan ya d’an jima kad’an sai a juya ta da sanda ko majuya daga baya sai a kwashe (Ladidi, 2017).

 

 

  1. Guguru


Guguru na daga cikin kayan k’walamar Bahaushe na gargajiya wanda ake sarrafawa. Guguru shi ne sarrafawar masara bayan an gyara ta, a kan yi amfani da tukunya tamkar irin tukunyar nan da ake amfani da shi wajen tuya k’osai. Dabarun aiwatar da wannan sana’a kuwa shi ne, da farko dai a kan nemi masara bayan an gyara ta, sai a nemi babbar tukunya da murhu da icce, idan an hura wuta, sai a aza tukunyar bayan da an ga alama ta yi zafi, sai a zuba masaran a dinga kai da komowa cikin tukunya ana jujjuyawa har sai sun farfaso sun kumbura sannan a kwashe su. Daga nan kuma, za a samo wata tukunya a zuba ruwa da sikari, idan sikarin ya narke, sai a zuba cikin sarrafaffen masara don a ji dad’inta. Wannan ita ce hanya ta gargajiya. Akwai wata hanya ta na’uran inji wanda aka samo a sanadiyan zuwan Turawa wanda bayan an gyara masaran sai a zuba cikin wannan inji ana jujjuyawa har ta soyu sosai kana a kwashe a zuba sikari kamar yadda dai bayani ya  gabata.

Wannan sana’a ta guguru sana’a ce ta Nufawa wanda kuma dad’ad’d’ar sana’a ce a yankin kuma suna samun amfani masu d’imbin yawa. Sannu a hankali, huld’ar al’ummar da kuma wata al’umma wato Hausawa suka sami tasiri a kansu wadda a yau ana samun Hausawa da suke sarrafa sana’ar guguru.

Bugu da k’ari, yadda bayani ya gabata a baya, an sami ci gaba ta zamani wajen yin amfani da na’uran inji wanda Turawa suka kawo wanda hanyar amfani da shi ya sa’bawa hanyan nan na gargajiya da aka san al’umman Nufawa da shi tun tsawon lokaci da suka wuce.

A k’arshe, sana’ar guguru tana da amfani matuk’a domin yana samar da aikin yi ga al’umman Nufawa kuma yana taimaka musu wajen sauk’ak’e al’amuran yau da kullum. (Ladidi, 2017).

iii. Dakkuwa

Ita ma dakkuwa tana daga cikin kayan k’walaman Bahaushe na gargajiya wanda asalinsa ta samu daga al’ummar Nufawa. Al’adar wannan sana’a, dad’ad’d’ar al’ada ce a yankin wanda kuma tasirin huld’a da zamantakewa irin ta kasuwanci tsakanin Hausawa da Nufawa ya sa aka d’auko al’adar ake hayyanawa (wato Hausawa). Amma kuma dabarun sarrafa dakkuwa na al’ummar Nufawa ta sha banban da na Hausawa.

Dabarun sarrafa dakkuwa a al’ummar Nufe, shi ne kamar haka: ana amfani da abubuwa guda uku wad’anda suka had’a da gyad’a da masara da kuma sukari. Bayan an sami wad’annan abubuwa guda uku, sai a gyara su, sannan a had’e su gaba d’aya a kai nik’a idan an nik’a ta, sai a zuba cikin turmi a rinka daka da ta’barya har ta daku sosai kamar za ta fito da mai, idan aka gama hakan, sai kuma a kwashe daga cikin turmi ana d’ibawa kad’an kad’an ana matsewa bayan an gama gaba d’aya, sai a rink’a zuba su kad’an-kad’an cikin kwano ana kai da komowa har su kai kamar za su fito da mai. Ana samun amfani sarai domin ana samun abin sauk’e larura ko buk’atun yau da kullum (Ladidi, 2017).

i’b. Gyad’a

Gyad’a tana daga cikin kayan k’walamar Hausawa na gargajiya. Al’adar gyad’a wato soya gyad’a dad’ad’d’an al’ada ce a k’asar Nufe kamar yadda bayani ya gabata kan sauran kayan k’walamar Bahaushe na gargajiya.

Dabarun aiwatar da sana’ar gyad’a ba wahala gare ta ba, abin da ke faruwa anan shi ne, idan aka sami gyad’a, bayan an gyra ta aka fitar da ru’ba’b’bu a cikinta, sai a samo ruwan zafi a jik’a gyad’an da gishiri, bayan wasu lokuta sai a zubar da ruwan sannan a baza gyad’an dan ya sha iska daga nan kuma sai a nemo tukunya da murhu da icce, idan an lura wutan, sai a aza tukunya kana a samo yashi ko k’asa a zuba daga nan kuma sai a zuba gyad’an ana kai da komowa har ta soyu sosai.

Akwai amfani masu d’imbin yawa cikin wannan sana’a dan kuwa ana samun abin rufa asiri kuma ana samun wanda za a ci da dai makamantan haka.

Abin da ya shafi dangantaka tsakanin al’ummun nan biyu kuwa (wato Nufawa da Hausawa) abu ne dake d’auke da dogon tarihi wanda a sanadiyyar haka, ya jawo kusantar Nufawa da Hausawa har ya kai inda harshen Hausa ya sami tasiri a kan harshen Nufe dan kuwa ana samun wasu mutane daga wurare daban-daban na k’asar Hausa wad’anda suke gudanar da wannan sana’a. (Ladidi, 2017).

3.4.2 Sana’ar D’inki


Sana’ar d’inki dad’ad’d’ar sana’a ce a rayuwar al’umma daban-daban daga lokaci zuwa lokaci domin kuwa tun shekaru aru-aru mutane suna saka tufafi don amfanin jiki da kare tsiraici. Da zamani ya yi zamani, sai aka sami kayan d’inki iri daban-daban saboda yawan al’ummar da suke amfani da shi.

Idan muka tuntu’bi tarihi lokacin da ‘yan adam suka fara rayuwa a doron k’asa, za mu gane cewa babu irin tufafin da muke amfani da su a halin yanzu sai dai abin da ya sauwak’a a lokacin su ne, ganye da kuma fatun dabbobi.

Da tafiya ta yi tafiya, lokacin da Turawa suka fara shigowa ne aka samu masak’a inda ake sak’a zannuwa iri daban-daban har aka fara shigowa da mashinan d’inki ko kekunan d’inki don kuwa sun fara shigowa ne a matsayin yawon kasuwanci had’e da lek’en asiri daga baya suka juya suka zamo ‘yan mulkin mallaka a shekara (1906) suke ta tafiyar da al’amuran yau da kullum domin sun samu gindin zama wanda sune wuk’a sune nama. (Yahaya, 1992).

Ya sake da cewa (Yahaya) a wannan lokaci ne ake harsashen sun shigo da keken d’inka tufafi kasancewar al’ummar masu hikima suka fara koyon d’inki na zamani wad’anda ke banbanta kayan maza da mata. D’inki suna ce ta gaba d’aya da aka baiwa sana’ar, amma kuma akwai mad’inka daban-daban da suke d’inka tufafi irin su malun-malun da aska biyu da kaftani da makamantansu.

A tak’aice dai, idan aka yi maganar d’inki, mutane sukan mayar da hankulansu wajen d’inkin tela dan kuwa shi ne tamkar madugu uban tafiya. Don haka, sana’ar d’inkin tela, sana’a ce wadda zamani ya zo da shi wanda kafin wancan lokaci, al’umma suna sak’a tufafi ne kawai ba tare da gwaje-gwaje da yanke-yanke ba har ta kai ga d’inki. Wannan sana’a ta bada gudunmawa sarai wajen samar da sababbin kalmomi ga al’umman harsunan guda biyun nan (wato Hausawa da Nufawa). Ga kad’an daga cikin misalin tufafi da suka samar wa al’ummar Hausa da Nufe kalmomi kamar haka:

__________________________________________________________________

          Kalma                                                          Ma’ana

__________________________________________________________________

Tazarce                                                            wasu irin riguna ne dogaye na maza daga

sama zuwa k’asa masu jan k’asa.

 

Tiri Kwata                                                       wani nau’in wando ne guntu na ‘yan gayu

wanda ake yi k’asa da k’wabri kad’an.

 

Sho mi yo back                                               wani irin nau’in riga ce ta mata da ake

bud’ewa da fad’i duk kafad’a a waje.

 

Bambalasta                                                      wani nau’in tufafi ne mai walk’iya wadda

maza da mata suke amfani da shi.

 

Shuwagaba                                                      nau’in wando ne na mata wanda ake d’inka

shi a matse.

 

Farmala                                                           wani nau’in riga ce da ake sanyawa a saman

k’aramar riga.

 

Fensir                                                              nau’in wando ne na maza wadda ake

d’inkawa a matse.

 

Fitet                                                                 wani nau’in riga ce ta maza da mata marasa

fad’i wato ana d’inka shi ne a matse.

 

K’ube                                                              wani nau’in hula ce mai tsada musamman a

wajen mutanen Maiduguri da kewaye.

 

Hijab                                                               wani nau’in mayafi ne  babba irin na

mutanen Makka wato Larabawa.

 

Shadda miro                                                    nau’in shadda ce mai walk’iro sosai wadda

maza da mata ne suke amfani da su.

                                                                                                                                                           

3.4.3 Sana’ar Noma

Lamarin noma a duniya, babban muhimmin abu ne wanda da taimakon manomanne muke samun kayan abinci iri-iri. Hausawa da Nufawa al’ummu ne da suke da dogon tarihi a duniya kuma akwai danantaka tsakaninsu iri daban-daban, wadda noma ma na daga cikinsu don kuwa sun sami huld’a na tsawon lokaci inda kuma muka wayi gari Hausa ya yi tasiri a kan Nufe a wurare daban-daban.

Noma shi ne tonon k’asa a fitar da amfanin ta ta hanyar shuke-shuke a bayanta ka ji kirarin da ake wa noma, “Na duk’e tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya tarar tajirin rani bawan damina”. Ta nan ne ake samun tsirai iri-iri na ci da na tsotsa da na yin tufafi.

Noma wata sana’a ce dad’ad’d’iya wadda mutane ke yin ta shekaru aru-aru da kuma ko da taimakon da dabbobi ko na’urori saboda tsare rayuwarsu da kyautata. (Ahmad, 2005).

K’asar Nufe ya na daga cikin k’asashen da ya dogara ga noma a wannan k’asa ya tanad’e a kan ruwan sama da dalili kuwa, a kan sami sauk’i a cikin watan Mayu har k’arshen watan Oktoba, lokacin damina kenan a k’asar Nufe, ko da yake babu banbancin damina tsakanin k’asar Hausa da na Nufe, amma wani lokaci ya kan fara sauk’a a Nufe kafin Hausa.

Manoma sukan fara kai taki gona kafin ruwan sama su fara sauk’a kuma su yi sassabe. Idan taurarin damina sun kama, sai a yi fize, in kuma ruwa aka samu, to sai shuka. Bayan shuke-shuken sun fito, cikin mako biyu kuma ta sami biko, sai kawai a fara tur’be ko ban huri. Can bayan shuka ta baje ta hau kaza, sai a shiga mai-mai kuma daga k’arshe sai a yo sassarya da cirar kuduji cikin gona. Ana shuka kuma ana roreta ne a fard’e ko tsige ko a ta’be.

Bayan noman damina, akwai kuma noman rani wato noma ne da ake yi a fadama ko kuma madatsan ruwa inda ake yin lambu a yi ta ba da ruwa. Ana nan ruwa da jigo (kutara) ne ko famfo mai ba fangallai ruwa ta hanyoyi daban-daban, a kan shuka abubuwa da yawa ko kuma a dasa su kad’an daga ciki amfanin gonar da ake nomawa sune kamar dawa, da gero da rid’i, da shimkafa da gyad’a, da wake da masara, da barkono da sauran tsire-tsire a lambu kamar su rake da albasa da gwaiba, da lemu da ayaba da mangoro da gwanda da karas da makamantansu da yawa.

 

3.4.4 Sana’ar Su (Kamun Kifi)


Al’adun kamun kifi al’ada ce dad’ad’d’a a cikin al’ummar Nufe da Hausa. Al’ummun suna amfani da ruwa ne wajen kamun kifi kuma suna da dabaru daban-daban na shigan ruwan wato irin dabarun da suke yi don samo kifaye iri daban-daban da kuma wasu abubuwa da suke rayuwa cikin ruwa. K’amusun Hausa (2006: p. 82) ya ba da ma’anar dabara kamar haka:

“Dabara ko dabaru kyakkyawan shiri ko wayo ko hikima ko tsari”.

Kenan dabarun kamun kifi ya danganci wayon mutum ko hikimar mutum ko tsarin mutum ko shiri  ko kuma hanyar da masinci zai bi ko amfani da shi wajen shiga ruwa don kamun kifi. Akwai dabaru daban-daban da ake bi wajen kamun kifi ga dai kad’an daga ciki kamar haka:

  1. Kwalle

  2. Lalabe



  • Darzaje


Ma’anar kifi, kamar yadda k’amusun Hausa (2006: p. 243) ya ce:

“kifate ko kifi wata halitta ce a ruwa mai k’arni wadda ake ci, akwai su iri kamar su tarwad’a, ko tsage, ko lulu, ko karfasa, ko musko, ko ragon-ruwa, ko sawayya, ko k’araya, ko minjirya ko barya ko bargi, ko madde ko halullu’ba da makamantansu”

 

D’an Iya (2006: p. 129) ya na cewa, su ko kamun kifi yana d’aya daga cikin sana’o’in Hausawa na gargajiya da ya ji’banci neman naman ruwa. Wato ma’ana sana’a ce dad’ad’d’iya a k’asar Hausa da ta ji’banci farauto naman da ke cikin ruwa musamman kifi da sauran nau’o in dabbobin ruwa kamar irin su kada da ayu da kwad’i da dorinar ruwa da makamantansu. Wannan sana’a a matsayin ta na dad’ad’d’iyar ko tsohuwar sana’a, na da irin nata kirare-kirare da kuma abokan wasanta kamar yadda Bahaushiyar al’ada ta tanada ga sana’o’in Hausawa na gargajiya.

“Sumtau bawan Allah

Mai yin ko ba ya fatara

Sai dai ya ji k’uyar yi”

Wannan na d’aya daga cikin nau’o’in kirare-kirare da ake yi ma wannan sana’a. wato wannan sana’a ce ta bayin Allah masu tak’awa da tawali’u da juriyar hak’urin zaman duniya wanda duk mai yin wannan sana’a ba zai yi fatara ba sai dai idan ya ji kunyar yin ta. Idan har shi mutum baya jin nauyin jikinsa, inda duk ya watsa fatsarsa zai sami d’an abin kalaci.

Haka kuma masunta da ke zaune a birane na k’asar Hausa na wannan zamani, suna yi wa wannan sana’a tasu kirari kamar haka:

“Su – sara, sassak’a kwarami

Sak’a, tsince-tsincen takalma

Susuta aiki magajin samu”

Manufar wannan kirari shi ne, akasarin wuraren da ake gudanar da wannan sana’a a birane (wato sana’ar su) za a tarar cewa ruwan a tare yake wuri guda. Wato ba mai gudana ba ne. saboda haka, za ka iske ciyayi masu d’an tsawo, haka kuma a wasu zaka tarar da kainuwa da bado da sauran hakukuwa sun wanzu bajaja a bisan ruwan, haka kuma za a tarar cewa akwai kwaramkwace baja-baja a ciki wanda akasarinsu shara ce ta gidajen al’ummar dake zaune kusa da wurin, sharar kuma kan k’unshi abubuwa iri daban-daban kamar irin su gwangwamaye da tsofaffin takalma da ledoji da k’arafa da kwalabe da sauran nau’o’in tarkace-tarkace, bisa wannan cinkoso ne da akan samu a wuraren da ake gudanar da wannan sana’a ta su musamman a birane ya sa ake yi wa wannan sana’a irin wannan kirari da ya gabata. Haka kuma, idan ka iske masunci na gudanar da sana’ar tasa, sai ka d’auka a susance kawai yake yi, amma sana’ar ta gaji samu. Bisa wannan dalili ne ya sanya ake yi wa wannan sana’ar kirari da cewa “Su sara sassak’a, kwarami, sak’a tsince-tsincen takalma susuta aiki magajin samu”.

Kamar sauran sana’o’in Hausawa na gargajiya da kowannensu ya ke da kayayyaki na musamman domin gudanar da sana’o’in. Haka ita ma sana’ar su, akwai kayayyaki iri daban-daban da ake amfani da su wajen gudanar da ita wannan sana’a. Ire-iren kayayyakin sun had’a da:

Brigi                                        Hura

K’ugiya                                   Wula

Taru                                         Fatsa

Koma                                      Dumba

Ara                                          Mashi

Sankiya                                   Kalli

Nau’o’in halittu da masunta kan yi muwafak’ar kamawa a cikin manya da k’ananan rafuka sun had’a da:

Tarwad’a                                 K’arfashe                     Tsage                           Gartsa

Gawo                                      Minjirya                       Halba                           Faya

Kufingu                                   K’ursa                         K’awara                      Ramfai

Mirgi                                       Ragon-Ruwa   ‘Barya                         Gamboshi

Dumno                                    Gaiwa              Wayya             Zawo

Bana                                        Yaka                            Saro                             Fanbami

Tatir                                         Gala                             Tako                            da makamantansu.

A k’asar Hausa, akwai nau’o’in masunta daban-daban wajen yin dabarar kamun kifi, haka kuma a k’asar Nufe babu banbancin irin wad’annan abubuwa da kuma mutanen ta yadda suke gudanar da al’adunsu na kamun kifi. Ga kashe-kashen masuntan nan kamar haka:

‘Yan Taru

‘Yan Mari-Mari

‘Yan Lalube

‘Yan Ago

Kamar sauran sana’o’in al’ummun nan guda biyu, na gargajiya da suke da wasu al’adu na ban al’ajabi. Haka ma masunta suna da nasu al’adu irin na tsa-tsiba da kuma al’ajabi. Wad’annan al’adun sun had’a da:

D’aure ruwa

Mayar da gungumemen itace kifi

Tsere na link’aya ko nutso na lokaci mai tsawo da ya sa’ba al’ada irin ta yau da kullum.

Kad’an kenan daga cikin ire-iren al’adun tsatsibe-tsatsibe na masunta a cikin al’ummar Hausawa da Nufawa.

Haka zalika, akwai wasu hanyoyi da masunta suke bi wajen sarrafa halittun abubuwa da suka kamo a ruwa musamman kifi, ga hanyoyin kamar haka:

Shanyar rana

Banda

Soyayye

Dafaffe

Gasashshe

3.4.5 Sana’ar Sabulun Salo


Sana’a ce dad’ad’d’iya a k’asar Nufe kuma ya na daga cikin albarkatun da al’ummar suka dogara a kai, dan kuwa ana samun amfani masu d’imbin yawa a cikin gida da waje.

Ma’anar Sabulun salo, cikin ganawa da na yi da Hajiya Habiba a garin Ndagbachi a k’aramar hukumar Abako ta Jihar Neja a ranar Asabar 01 ga watan Yuni, 2017 cewa:

“sabulun salo sarrafawa ce ta amfani da ruwan toka mai tsami had’e da man kad’e ko alayadi a had’ e tare da dafawa har ta kai ga abin da ake so”. (Habiba, 2017).

A al’adar Nufawa, akwai abubuwa da ake amfani da su wajen aiwatar da sabulun salo, wanda ya had’a da:

Ruwan toka

Man kad’e

Man alayadi

Dabarun aiwatar da sabulun salo, ya danganci neman ruwan toka mai tsami kamar bokiti guda ko kuma sama da haka gwargwadon yawan sabulun da ake nufin had’awa cikin tukunya bisa wuta za a hura mata wuta sosai har ta dafu. Idan ya rage kad’an bayan ya ci wuta sosai, sannan a samo man kad’e ko man alayadi a zuba cikinta a ci gaba da dafawa har zuwa lokacin da za a ga alama ta koma bak’i k’irin sai a jujuya da dogon sanda daga nan kuma za a nemi k’ananan kwanduna ko gwangwamaye ko robobi ana d’ibawa da cokali ana zubawa cikin wad’annan kwanduna gwargwadon girman da ake buk’ata. Idan kuma ta sha iska, sai a cire su kana a fara yin amfani da su ko kuma sayar da su.

Al’adar sabulun salo ya na d’aukan lokaci mai tsawo kafin a had’a shi domin irin matakan da ake bi wajen aiwatar da shi. Haka kuma abin da ya shafi dangantaka a gefen wannan al’ada tsakanin Nufawa da Hausawa, abu ne da ke d’auke da dogon tarihi kamar yadda hasken al’amarin ya bayyana ta bakin Malama Habiba wadda ta ke da tsawon kimanin shekaru saba’in da biyu a duniya inda ta nuna cewa, ta sami hasken labarin daga mahaifiyarta mai suna Kaka Legbo (Marigaye) a garin Ndagbachi inda ta ke cewa, al’adar amfani da sabulun salo, babu wani banbanci tsakanin Hausawa da Nufawa domin a kan yi amfani da shi wajen wanke sabon jariri ko dai a ce ya na daga cikin kayan da iyaye mata suke tanadawa d’iyansu masu juna biyu kafin ya kai ga lokacin haihuwa a al’adar al’umman nan guda biyu. Haka kuma ana amfani da wajen wanke gawa. Ta ganin irin d’imbin alfanu da wannan sabulu ke da shi ne Hausawa suka fara huld’a ta kasuwanci aka kuma sami wad’ansu Hausawa da suka kwaikwayi wannan sana’a wato yadda ake aiwatar da shi wanda ana iya samun Hausawa jefi-jefi cikin wannan sana’a ta sabulun salo. (Habiba, 2017).

 

 

3.4.6 Sana’ar Daddawa


Sana’a ce dad’ad’d’iya a k’asar Nufe kuma ta na da amfani ga masu sana’ar da masu girki da dai sauran al’umma da suke amfani da daddawa. Wannan sana’a ta shahara a k’asar Nufe cikin karkara da birane saboda irin amfani da yake d’auke da shi.

K’amusun Hausa (2006: p. 84) ya ba da ma’anar daddawa kamar haka:

“Wata bak’ar abu da ake yi da kalwa ana sawa a miya don k’arin zak’i, amma tana da wari”

Ita kuma Malama Gogo haifaffiyar wani gari mai suna Emi Tsara a k’aramar hukumar Gbako ta Jihar Neja a ganawar da akai da ita a ranar Talata 25 ga watan Mayu, 2017 ta ba da ma’anar daddawa kamar haka:

“Sarrafawa ne na kalwan d’orawa ta bin hanyoyi ko matakai daban-daban har a kai ga yadda ake sonta”.

(Gogo, 2017)

Amfani da kalwan d’orawa don a mayar da shi abin da ake sa miya ko k’arawa miya dad’i wato daddawa ya na buk’atar dogon tafiya kafin a kai ga wurin sauk’a. Abin nufi a nan shi ne, akwai matakai da ake bi wajen sarrafa kalwan d’orawa don ya zamo daddawa. A bayaninta ta na cewa, idan an samo kalwan sai kuma a gyara ta daga nan kuma a zuba cikin tukunya a dafa kamar dai mai dafa shinkafa ko wake, amma kuma a kan fara dafa kalwan ne tun da safe har zuwa maraice ko kuma daga maraice zuwa safiya. Idan ya dafu sosai, sai a sauk’e sannan a zuba cikin babban k’warya ko kwando a rufe da kyau amma kafin a rufe shi, akwai wani bak’in abu kamar gari mu kan k’ira shi da harshen Nufe ‘Eda Kula’ a rufe daga maraice zuwa safiya daga nan kuma a fara mulmula dai-dai yadda ake buk’atarsa. A cewarta, wannan bak’in abun da aka zuwa wato bak’in garin nan shi ke taimaka wajen samun sauk’in mulmule shi.

Haka kuma, ta sake cewa a zamanin kaka da kakani, al’umma ba su san wani abu  da sunan maggi ba kamar yadda zamani ya zo mana da su yanzu, abin da muka sani a wancan lokaci kuwa shi ne daddawa wadda ke sa girki ko miya ta yi armashi ko dad’i ko zak’i domin duk sa’ad da aka sa shi cikin miya, ya kan fitowa da d’and’anonsa yadda ya kamata. Ganin irin amfanin daddawa a doron k’asa ne ya ba wasu Hausawa damar yin huld’ar kasuwanci inda ake zuwan saye daddawa daga k’asar Nufe zuwa k’asar Hausa. Haka kuma, ta ce a sanadiyar wannan huld’a na kasuwanci, ana iya samun wasu Hausawa da su iya sarrafa daddawa wadda hakan ya yi tasiri k’warai a tsakanin al’umma.

3.4.7 Sana’ar K’ira


Sana’ar k’ira dad’ad’d’iyar sana’a ce a ban k’asa wanda ya k’unshi bak’i da farin k’arfe da kuma k’arau (wato sarrafa kwalabe) kuma wannan sana’a ta shahara a garin Bida ta Jihar Neja.

Tarihi ya nuna cewa babu isashshen bayani da zai nuna lokacin da wad’annan mak’eran suka shigo garin Bida ko kuma k’asar Nufe, amma kuma ana iya yin hasashe zuwa shekara 1859 – 1860 inda aka sami wasu matasa suka yi k’aura zuwa k’asar Nufe.

K’ira sana’a ce ta sarrafa k’arfe a mayar da shi makami ko ma’aikaci da dai makamantansu. Ana sarrafa k’arfe ko tama ko saho lama ko gaci ko azurfa ko zinari da wuta a mayar da su wani abin amfani. Zugazugai kayan k’ira ne da uwar mak’era da guduma da masabi da saketa da awartaki da makamantansu.

An dad’e ana k’ira tun shekara da shekaru kuma tun daga wancan lokaci har zuwa wannan lokaci, k’ira ta yi ayyuka da dama inda aka sami cikakken kayan fad’a, mak’era sun taka rawar gani lokacin yak’e-yak’e a k’asar Nufe don kuwa su kansu sun shigo Nufe ne a sanadiyar sarakuna kamar yadda na sami hasken daga wani mutum mai suna Abdullahi maigida a anguwar dokadza ta garin Bida ta Jihar Neja a ranar litinin 24/04/2017 inda ya ke cewa duk inda sarakuna suke, za a tarar da mak’era suna tare da su saboda k’ere-k’eren da suke yi wa sarakuna na kayan yak’i da kuma kayan adon dawakai da dai makamantansu. Haka kuma, har zuwa wannan lokaci suna taimakawa don suke k’era abubuwan amfani na yau da kullum.

  1. K’iran Bak’in K’arfe


Mak’eran bak’in k’arfe, mutane ne da suka shahara wajen sarrafa k’arafai su mayar da su kayan amfani iri daban-daban. Kamar yadda bayani ya gabata kan n lokacin da mak’eran suka shigo k’asar Nufe da kuma inda suka yi k’aura zuwa inda suke a yau.

  1. Baba (1978) ya sanar da mu cewa, mak’eran bak’in k’arfe sune tamkar jagoran sauran mak’era a asali don kuwa an nuna sun shigo Bida na k’asar Nufe ne tun daga lokacin da ake k’iran garin da suna ‘Banin’ kuma suna da shugaba wanda aka yi sarauta da suna ‘Majin Tswata’ su wad’annan mak’era suna a k’ark’ashin masarautar Umaru kuma tarihi ya nuna suna tare da sarakunan Nufe tun lokacin da babbar masarautar Raba kafin a mayar da ita garin Bisda, sanadiyar wannan ya sa aka yi nad’in wani sarauta na mak’era mai suna ‘Dokodza’ wanda kuma shi ne shugaban mak’era a duk k’asar Nufe.


Bisa ga al’ada, mak’eran suna samar da k’arfe su fara k’ere-k’erensu bayan da suka yi shirin zuwa inda suke hak’o tama, za a zo ne a tare tubalan tamar wuri guda, sannan a d’auko zugazugai kamar guda hud’u zuwa biyar a d’a’irce tamar za a zuba gawayin itacen k’irya a yi ta hurawa ko rura wutar kimanin sa’a biyar zuwa takwas. Daga nan, za a bar tamar a kan garwashin har zuwa safiya. Da gari ya waye za a tarar kumfa ta rufe ainihin tamar, sai a sa hannu a ‘ban’bare wannan kumfa, za a tarar ta zama k’arfe. To wannan k’arfen ne ake sarrafa shi domin gudanar da sana’ar k’ira.

 

 

  1. Mak’eran Farin K’arfe


Mak’eran farin k’arfe suma sun dad’e a k’asar Nufe wajen gudanar da sana’ar su na k’ira, kuma sune kashi na biyu daga cikin mak’era guda uku da ake da su a k’asar. Don kuwa wad’annan mak’eran sune ke k’era kayayyaki iri-iri kamar murjani da ciko da mundaye da kayan adon doki irin su sirdi, kambu da kuma likkafa. Irin wad’annan mutane wato mak’eran farin k’arfe ana samun su ne a anguwanni guda uku a garin Bida wad’anda suka had’a da ‘Tswata muku’ da Gbongbofu’ da kuma ‘Tswatako’. (M. Baba, 1987).

K’iran farin k’arfe sana’a ce da ake sarrafa kayan amfani iri-iri kamar na adon mata da suka had’a da ciko, da murjani da kuma mundaye. Haka kuma akwai kayan adon doki irin su kambu da likkafa da kuma sirdi akwai kuma irin su ludayi da cokali da dai makamantansu.

Babu cikakken tarihi a kan asalin mak’eran farin k’arfe, amma akwai dai hasashen da ke yin nuni da cewa, aikin sana’ar k’iran farin k’arfe ya sami asali daga wasu mutane  da suka taso daga Afirka ta arewa a zamanin sarkin Nufe Abubakar (Etsu Abubakar) a misalin shekara (1859), wanda kuma a lokacin Turawa suka taso wa yankin ta (Royal Niger Company). Idan wannan hasashen ya na k’unshe da gaskiya, to mun sami tabbacin cewa a wannan lokaci ne sana’ar k’irar farin k’arfe ya sami gindin zama a k’asar Nufe. (M. Baba, 1987).

iii. Sana’ar Karau

karau sana’a ce ta k’ira kuma ta shahara a k’asar Nufe shekara da shekaru wadda tarihi ya nuna cewa al’ummun da suka ke’banta ga yin wannan aiki ko sana’a, sun taso ne daga k’asar Masar (Egypt), suke ta yawo daga wuri zuwa wuri don neman abin rufin asiri da neman abinci. A wani k’aulin kuma, wai dalilin annoba da yak’e-yak’e ya sa suka bar k’asarsu zuwa wurare daban-daban har suka sami gindin zama a inda suke a halin yanzu wato masaga a garin Bida ta jihar Neja.

Haka kuma, bayan dogon zama da suka yi tsakaninsu da juna, akwai wasu mutane guda goma sha takwas wad’anda tarihi ya nuna su ne suka yi k’udurin barin k’asarsu, cikinsu akwai maza goma da mata takwas, ga sunayensu kamar haka:

  1. Jafaru

  2. Abdullahi

  3. Ayuba

  4. Junaidu

  5. Iliyasu

  6. Isma’ila

  7. Muhammadu

  8. Yahaya

  9. Ibrahim

  10. Dauda

  11. Zainabu

  12. Habibatu

  13. Hauwa’u

  14. Ruk’ayyatu

  15. Asma’u

  16. Atikatu

  17. Hadijatu

  18. Aishatu


Tarihi ya nuna cewa jikokin wad’annan mutane sha takwas, yawancin su ne suka yada zango a inda ake k’ira anguwar masaga a garin Bida ta Jihar Neja wanda sune ke gudanar da wannan sana’a ta karau (glass work). Kuma ta d’auki kimanin shekara talatin da uku kafin su iso k’asar Nufe.

Karau sana’a ce ta sarrafa kwalabe don mayar da su kayan amfani musamman na adon mata. Haka kuma masu sarautun gargajiya ma na amfani da su kamar sarakunan Yarabawa (wato Oba) da kuma na Inyamurai (wato Igwe) da sauran manya-manyansu masu rik’e da sarautun gargajiya. Turawa suna amfani da su wajen tarihi.

Haka kuma, wasu abubuwa ne ake amfani da su wajen gudanar da wannan sana’a jiya wato kafin zuwan Turawa, wanda a sabilin zuwansu ne muka sami kwalabai da ake amfani da su a halin yanzu. Kafin wannan lokaci, mak’eran wannan sana’a ta k’arau suna da k’arancin kayan aiki amma da Turawa suka shigo, sai aka fara samin kwalabai da gilasai wajen samar da kayan adon mata masu d’imbin yawa.

Wad’annan al’umma sun fara yin k’aura ne daga k’asarsu ta asali tun wajen shekara (1821) inda suka fara yada zango a k’asar Libiya tsawon shekaru biyu, sai kuma wani gari mai suna Adabara a shekara (1823) sun kuwa yi zama a wannan gari na Adabara tsawon shekara shida domin sun sami cin kasuwa sarai, sun kuma bar garin a shekara (1829) suka haurawa garin Zalinge inda suka yi shekara goma sha d’aya, daga nan sai garin Atiya sun yi shekara bakwai a can wato daga 1840 zuwa 1847 daga Atiya kuma sai Yerwa inda suka yi shekara hud’u 1852 kafin su yi k’aura zuwa Zariya a cikin wannan shekara 1852 suka yi zama kimanin shekara d’aya da rabi a Zariya 1852 ½ sai kuma garin Nahuche. Yayin da suke zama a wannan gari na Nahuche ne suka ji labarin Dendo a k’asar Nufe wanda Nufawa suka yi wa lak’abi da ‘Manko’ a shekarar 1854 a garin Raba, da suka yi ido biyu da shi, sai suka gaisa kuma suka fad’a masa cewa Larabawa ne su daga Cairo kuma musulmai, Dendo ya ba su masauk’i suka yi murna suka ce babu inda za su je yanzu za su ci gaba da zama tare da Dendo. Duk hakan ya faru ne lokacin shekaru hud’u wato daga 1854 zuwa 1857 lokacin da Dendo ya koma garin Lade don yad’a addinin musulunci. Bayan shekara biyar kuma, wato shekara 1862 Dendo ya sake komawa garin Abara don ci gaba da yad’a addinin musulunci duk suna tare kafin su koma wurin zama na din din din wato inda suke da zama yanzu a garin Bida cikin shekara 1867 zamanin sarki Abubakar (Etsu Abubakar Masaba), suka kai gaisuwar ban girma fadar sarki sai ya ba su masauk’i wato anguwar Masaga kusa da wani rafi wai shi Landzum saboda yanayin sana’arsu ba zai gudana kamar yadda ya kamata ba face da ruwa.

Da wad’annan mutane suka samu gindin zama a garin, sai suka za’bi rana na kai wa sarki gaisuwar ban girma tare da yi wa sarki abubuwan k’ere-k’erensu iri daba-daban har guda goma. Sarki ya yabe su, ya kuma yi musu godiya daga baya, ya nema da su zo da mutum guda da suka yarda zai shugabance su don a ba shi sarauta, tun wannan lokacin ne aka fara samun sarautar Masaga Nufe, yayin da kuma gaisuwarsa shi ne ‘Turawa’.

K’ira dai kamar sauran sana’o’i, yana buk’atar kayayyakin gudanar da sana’ar wad’anda suka had’a da:

  1. Uwar mak’era Magagari

  2. Guduma Kalamba

  3. Masaba Gizago

  4. Masko Gawayi

  5. Hantsaki/awartaki Zigazigi

  6. Kurfi Turu na Mak’era

  7. Matsoni Mak’a/mak’ata

  8. Turmi k’. Tubalin mak’era/Tubalin Bakin Wuta

  9. Madoshi                                  Iccen Bakin Tubali


Sana’ar k’ira tana da matuk’ar muhimmanci matuk’a, domin ta haka ne ake samun mak’era ko ina birni da k’auye. Idan za a gabatar da sana’ar k’ira, dole ne a samu muhallin yinta da kuma kayayyakin amfani wajen yinta kamar yadda na ambata su dage sama, haka kuma abubuwan da ake k’era wa irin kayan alatu na mata irin su mundaye da murjani da ciko da kayan amfani cikin gida irin su cokali da ludaye da kayan adon doki irin su kambu da sirdi da likkafa da linzami da wasu kayan musamman irin na aikin gona da na cikin gida irin su garma da fatanya da gatari da dagi da mashi da takobi da wuk’a da zarto da mari da adda da lauje da manjagara da dai sauran makamantansu.

3.5 Dangantaka ta Fuskar Auratayya


Dangantakar auratayya tsakanin Hausawa da Nufawa abu ne da ya faru tun shekaru aru-aru inda kuma ake samun Hausawa cikin gidan Nufawa su kuma Nufawa cikin gidansu. Wannan dangantaka ta k’ulla gagarumin zumunci tsakanin al’ummun inda ake samun fuskokin aure tsakaninsu wanda ya had’a da auren sadaka, da na zumuncin da na gata da dai makamantansu.

Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da al’amarin aure, daga cikin su akwai:

Habib A. ga abin da ya ke cewa:

“Aure alak’a ce ta halaccin zaman tare tsakanin mace da namiji. Ana yin sa ne saboda abin da aka haifa ya sami asali, da mutunci, da d’aukaka da kiwon iyaye kuma shi ne maganin zina ga ‘ya ‘ya marasa iyaye”.

 

Shi kuma Gusau da wasu ga abin da suke cewa:

“Aure wata hanya ce ta k’ulla zaman tare tsakanin namiji da mace ba tare da iyakancewa ba sai in mutuwa ta raba wanda ake iya tabbatarwa ta amincewar ma’auratan da waliyansu da ka shaidu”

 

Saulawa I. A a na shi ra’ayi:

“Aure wani abu ne wanda ake yi tsakanin mace da namiji bisa ga amincewa da junansu a had’a su tare ta hanyar shimfid’ad’d’un k’a’idoji na wannan al’umma”.

 

Idan muka yi la’akari da ma’anonin wad’annan masana a game da aure, sun yi amfani da wasu za’ba’b’bun kalmomi da suka zamanto dole a yi kula da su cikin auratayyarmu na Hausawa saboda irin mutunci da d’aukaka da Bahaushe ya gada tun kaka da kakani; za a iya kallon wad’annan kalmomin da suka had’a da asali, da mutunci da d’aukaka da maganin zina da amincewar juna da waliyai da kafa shaidu wajen tabbatar da shimfid’ad’d’un k’a’idoji da makamantansu.

Akwai alak’a makusanciya tsakanin auren Hausawa da Nufawa wanda duk sharud’an da ake cika kafin a wanzar da aure, kusan iri guda ne wanda babu banbanci a ciki.

3.5.1 Bikin Aure


Kamar yadda al’ada ta nuna, can da iyaye ne ke bid’ar wa ‘ya ‘yansu maza da mata wanda zasu aura kuma ba lalle su tafi wurin tad’i ba wani lokaci ma sai dai ma’auratan su sami sanin juna bayan an gama bikin auren. A k’asar Hausa, akwai wakilin uban yaron da ake neman ma aure wato a kan nemi dattijo ne wanda ake aikawa gidan yarinya tun daga lokacin nema har lokacin auren.

Kafin ranar d’aura auren ya shigo, a kan buk’aci yaron da ake neman wa yarinya, ya tafi gidan iyayenta don ya yi musu gaisuwa da dangin uwa da uba duk sai an kai musu gaisuwa. Da farko dai, bayan an ga yarinya kuma uban yarinya ya ga yaron da ake neman ma kuma suka amince, sai a buk’aci kawo goro na d’aya da na biyu, daga nan kuma a fara shirya dukiyar da za a kai gidansu yarinya na aure wato kud’in neman aure da na rabawa dangi. Bayan gaishe-gaishen da yaron zai yi kamat yadda aka ambata a sama, sai a sa ranar d’aura aure kuma a nan ne ake gabatar da sadaki, bayan an d’aura aure da lokaci kad’an sai a fara shirye-shiryen kai ta d’akinta idan wuri mai nisa za a je, idan kuma cikin gari ne za a kai ta, a kan jira zuwa maraice kuma iyayen ango ne ke ba da lokacin d’aura aure da kuma lokacin da za a kai amarya d’akinta. (Bello M. da Sa’idu M. Gusau, 1970).

Amma kuma idan aka duba al’adar aure a wannan lokaci ya banbanta da na wancan lokaci domin akwai tasirin zamananci inda ake samun rashin jituwa tsakanin ma’arauta musamman idan iyaye ne suka k’ulla musu soyayya tsakaninsu, yaran sukan sami matsala sai dai suma su nemi juna kuma su amince da soyayya tsakaninsu. Akwai al’adu iri daban-daban da ake gudanarwa cikin aure wanda tasirin addinin musulunci ya kau da yawancin al’adu sai dai ba a iya rasa wasu al’adu a wasu yankunan k’asarmu cikin cikin al’ummar Hausawa da Nufawa. A kan kai kayan lefe ta amfani da sakar kaba da manyan kwanoni da fantimoti da kuma kwallaye, wad’annan sune inda ake zuba kaya a wancan lokaci a kai gidan amarya, amma zamani ya sauya wad’annan abubuwa sai ake amfani da akwatuna msu taya wajen zuba kaya zuwa gidan amarya.

A zamanin kaka da kakani a kan yi amfani da tsohuwa ne wajen yi wa amarya da ango wanka ko kuma sa lalle, a yayin da ake sa wa amarya lalle, ‘yan uwa da abokai sukan taru, suna tafe suna rera wak’ok’i iri-iri shi kuwa ango, a yayin yi masa wankan ango a kan nemo makad’a su rink’a kad’a ganga tun farawar wankan har gamawarsa bayan haka sai ya kaiwa iyaye gaisuwa wasu ke’ba’b’bun mata sukan rera wak’a da yin gud’a da makamantansu. Daga cikin irin wak’ok’in da ake rera wa amare, akwai irin:

Ayye mamaye iye

Ayee mama labo-labo

Mama ye iye

Turmin mama turmin dakan tama

Mama ye iye

In kin ji dad’i zauna

Mama ye iye

In ko babu dad’i tsere

Mama ye iye

A kan kuma rera irin wannan wak’a lokacin da ake kai amarya d’akinta. Wata al’ada kuma wanda har zuwa wannan zamani ana yin sa, al’adar kuwa ita ce inda mata sukan taru cikin rana ta biyu da aka kawo amarya ko kuma ranar farko inda a kan k’ira ‘yan uwa da abokai maza da mata k’anana da manyan don tarawa amarya kud’i wai kud’in d’auke musu kunya wanda a harshen Nufanci ake k’ira (yawo zunyali). A kan yi abinci iri daban-daban da yanke-yanke da kuma shaye-shayen kayan dad’i na zamani da makamantansu.

Al’adar bikin aure a al’ummar Nufawa d’aya yake da na al’ummar Hausawa dan kuwa, duk matakan da ake bi wajen neman mata ko neman miji d’aya ne babu wani banbanci don haka, akwai dangantaka makusanciya tsakanin wad’annan al’ummun guda biyu wato Hausawa da Nufawa.

3.5.2 Bikin Haihuwa


“Haihuwa maganin mutuwa, ba dan ke ba, da iri ya k’are”. Da jin kirarin da Hausawa ke yi wa haihuwa kuma sun k’ara da cewa, kyawun gida da magaji”

Ahmad (2005) ya ba da ma’anar haihuwa kamar haka:

“Haihuwa ita ce, yayin da miji da mata suka k’aru da samun  d’a ko ‘ya”.

      Masu hidimar haihuwa suna cewa, lokacin da mace ta sami juna biyu, wato sa’ad da ta sami ciki bayan an tabbatar da igiyar aure tsakaninta da minjinta. K’arshen haihuwa kuma shi ne, yayin da jariri ya fito daga cikin uwarsa ta hanyar al’ada, tin daga wannan lokaci ne iyaye za su soma tattalin abin da suka samu har sai ya girma ya kai minzilin mutum wato sai ya kama kansa.

Da zarar mace ta sami juna biyu, sai iyayenta ko wasu masu kula da ita su suk’ufa wajen neman taimako don ta sauk’a lafiya. A kan kafa mata dokoki da za ta kiyaye kanta da shi irin cin abinci ko shan abin sha masu zak’i kamar zuma da sukari, ko rake ko mazark’waila ko alawa sabosa sauk’in nayin fitowar abin haihuwa wanda yake faruwa da ciwon zak’i. Kuma a kan umarce ta da ta rik’a shan magani kamar sabara da bauri.

Idan haihuwa ta farko ne yarinya takan je goyon ciki wato zuwa gidan iyayenta don ta haihu a can domin ta samu cikakken kula sosai don gudun  had’ari da barkwanci wajen haihuwa da rashin iya yin wankan bik’i kamar yadda ya dace a al’adance. Idan mace ta shiga nak’uda, alama kenan haihuwa ta kusa, daga nan sai a shiga tattalin maganin sauk’in gwuiwa kamar shan rubutu da jik’e-jik’e sai a aika a k’irawo wata mace wato ‘yar biki ko ungozoma don ta kula da mai haihuwa, kuma in ta sauk’a lafiya, ta wanke abin da aka haifa kuma ta yanke cibi ta binne mahaifar, sai bayan fad’uwarta, ungozoma ta kan ce “Alhamdulillahi, barka da arziki” da dai sauran addu’o’i da a kan yi bayan haihuwa ta fadi. A kan yi gud’a sau uku idan namiji aka samu, idan kuma mace ce a kan yi gud’a sau hud’u, wannan gud’a tamkar shela ce cewa ga irin abin da aka haifa. Daga nan kuma, sai a fara yin lugude don a sanar da mak’wabta cewa an sauk’a lafiya, na nesa kuma a aika musu manzo. Lugude daka ne da a kan yi cikin raha, ana yi ana gud’a ana kad’a turmi da k’warya da makamantansu. Haka kuma a kan taru a yi gayya wajen dakan luguden.

Bakin sanarwa, ana kuma maganar ‘boye ta hanyar lugude, masu lugude suna iya yi wa mak’wabta ba’a  ko zambo, ko wani abu makamancin haka, su kuma idan sun gane, sai su girka nasu luguden domin su mayar da martani.

A cewarsa (Ahmad) ana yi wa wadda ta haihu wak’ar bik’i, wannan wani wanka ne na tilas da yarinyar ta ke yi ko ake yi mata da cewa ta sauk’a lafiya da tafashshshen ruwan zafin gaske tare da ganyen runhu ko sabara ko toka ko ma dalbejiya saboda maganin ciwon sanyin haihuwa wanda ya kan sukurkuce yarinya, wani lokaci ya kan aukar da ‘barna fiye da haka. Takan yi wankan ne sau biyu a rana safe da maraice tun daga ranar haihuwa har ta yi arba’in, sannan ta mayar da wankan sau d’aya a rana ko dai sa safe ko kuma da maraice kurum don kuwa wannan wanka yana taimakawa k’warai da gaske, ta haka ne ake yi mata kirari ana cewa:

“Wank’an bik’i maganin sum’buta, yarinya daure ki yi shi ki huta, in kun kuskura sai bugunki”.

Da cewa matar mutum ta haihu, sai mijin ya yi sayayyar kayan barka da haihuwa ko kayan bik’i kamar itace da kayan yaji da gishiri da buhun gero da na dawa har da shinkafa da garwar kananzir da fitilar kwai da zannuwan goyo da kayan jariri da makamantansu. Idan namiji ne aka haifa, bayan kwana uku ake shan magani ko shan kimba idan ko mace ce sai an kwana hud’u. Ranar shan kimba, angon k’auri na sayen kauri wato kan sa da k’afafuwansa, wani lokaci har da rago a aikawa matar mai haihuwa. Wannan shi ne dalilin da ya sa idan an yi wa mutum haihuwa aka ce masa angon k’auri.

Bayan haihuwa da kwana shida, iyayen mata suna aikawa miji da walima wato su yi masa (waina) da alkaki da ‘yan kud’i, shi ko zai sayi rago don rad’awa abin da aka haifa suna da goro don rabawa a wurin rad’in sunan. A ranar suna, wani kan yanka raguna biyu wani ko rago  d’aya da sa. Idan kuwa haihuwar ta biyu ce ko fiye, rago d’aya ne ake saye a yanka, wani ko biyu daidai da k’arfin kowa. Jama’a sukan taru a rana ta bakwai don rad’awa yaron da aka haifa suna, dangin uba sune ke rad’awa abin da aka haifa suna bayan sun za’bi sunan. Haka kuma mata na taruwa gidan suna don haka wanda aka yi wa haihuwa, yana sayen kayan shaye-shaye irin su koka kola da fanta da minti da biskit da goro da sabulun wankan ‘yan biki da makamantansu, ya aikawa ‘yan biki su watse zuwa gidajen mijinsu biki ya k’are kenan sai an sake wata haihuwa. Asalin wannan taro, don a yi wa jariri aski a taru ana kad’e-kad’e ana ba marok’a da wanzamai samu don kuwa a taya mahaifan jariri ko jaririya murna da farin ciki (Bello da Sa’idu M. Gusau, 1970).

3.6 Nad’ewa


Wannan babi na uku ya yi bayani ne tare da gabatar da shimfid’a sannan kuma dangantakar Hausawa da Nufawa, da ma’anar dangantaka, da fuskokin dangantaka irin ta addini da suka had’a da almajirci ko neman ilimi da malanta, da jihadin Shehu da dangantakar fatauci, da zuwan Turawa da yak’e-yak’ensu da dangantakar wasu al’adu irin su kayan k’walamar Bahaushe kamar k’osai, da guguru, da dakkuwa da gyad’a da sana’ar d’inki da noma da kamun kifi da sabulum salo da daddawa da k’ira na fari da na bak’in k’arfe da k’arau da dangantakar auratayya irin su bikin aure da kuma bikin suna.

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

Post a Comment

0 Comments