Ticker

6/recent/ticker-posts

Noma: Igiya Maɗaurar Kaya In An Yi Ba Da Kai Ba Su Watse

Takardar da ake gabatar a taron k’ungiyar Manoma ta tarayya, reshen Jihar Sakkwato (AFAN) a makarantar Ilmukan K’ur’ani ta Sarkin Musulmi Muhammadu Maccid’o Abubakar III ranar Lahadi 31-05-2014 a bukin k’addamar da kalandar manoma da karrama fitattun manoma da masu agaza wa aikin noma
 

Daga

Aliyu Muhammadu Bunza

Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya

Jami’ar Umaru Musa Yar’adua

Katsina Nijeriya

Gabatarwa:


Halittun da suka mamaye duniyar matane guda biyar ne :

Mutane da dabbobi da tsutsaye da kwari da tsirrai. Mutane tsuntsaye da dabbobi da k’wari da tsirrai ne abincinsu. Tsuntsaye a kan su suke shawagin bid’an abinci su. Dabbobi da k’wari da tsuntsaye da tsirrai suke kalaci. Tsuntsaye a kan su suke shawagin bid’an abincinsu. Tsirrai da toroson Mutane da dabbobi da tsuntsaye da k’wari (da nasu) ke rayar da su. Wanda ya jahilci wannan ya yi wa duniya zuwan kare ga aboki. Wanda ya hak’ik’ance su bai zuwan sunge duniya ba. Sarrafa rayuwar wad’annan gabad’ayansu, su amfani mazauna duniya, yana ga hannun manoma. Ashe idan aka ce ga k’ungiyar manoma kowa na cikin ko bai zo ya yi rejista ba murhun gidansa wata babbar hujjar zama d’an k’ungiyar AFAN ne. Don haka nake ganin ba sai an wasa wannan k’ungiya ba, domin masu hikima ce wa suka yi annurin fuska kaurin hanji.

Mak’asudi:


Mak’asudin taronmu a yau shi ne, k’addamar da kalandar masu hankali, ‘yan kishin k’asa, ma’arzitan duniya. Masana al’ada sun ce hankali cikin gona yake yawo da ya yi ‘batan hanya hauka za ta zo, da an koma gona santi da sai’bi za su farfad’o da shi. Babu d’an kishin k’asan da ya kai manomi, domin k’asar da duk babu shi komai k’arfin arzikinta dole ta ragaice. Da noma aka fara girka arzikin duniya. Duk tattalin arzikin da babu noma ciki yunwa na wargaje shi. Tabbata burinmu na karrama noma da manoma da masu agaza wa noma da manoma wani sabon alk’awali ne na ceton al’ummar jaharmu da k’asarmu baki d’aya. Hak’ik’a, ma’aikatar  kula da al’amuran noma ta jahar sakkwato ta cancanci yabo ga kowane irin manomi na jaha. Irin k’wazon ma’aikatanta na ganin kayan tallafa wa manoma sun sadu ga manoma shi ya sa muka shirya wannan taro na godiya ga gwannatin Jihar Sakkwato da ita kanta ma’aikatar da ma’aikatanta da masu agaza mata. Allah Ya yi muka jagora ya k’ara k’arfafa ku. Goyon bayan da kuke ba mu, ya k’arfafa mu muka ba yauwa tsoro ta yi hijirar da babu ranar yada zango k’asarmu

 Gurbin Manoma

A tunaninmu kowa manomi ne, da mai rik’a kwasa da mai rik’a kuyafa da mai rik’a cokali. K’arfafa sana’armu na rage ta’addanci a k’asa. Inganta ta na kawar da rikice-rikice k’abilanci. Mutunta ta na kawar da rikicin addini. Ba ta cikakken goyon baya na yayyafa wa rikicin siyasa ruwa. Ba ta goyon baya na hana wa matasa ragaita. Kula da ita makamin yak’ar ‘bata gari da zauna gari bunza ne. A ba mu dama a gani, mu yanke wa yunwa hukuncin kisa, mu rataye ta, in ana sake jin ‘bular cutar zawo da amai da maci-d’an-wawa da gyambon ciki da juwa da hauhawan jinin da babu dalili. Na yarda da tunanin Garba Gwandu da ke cewa:

Noma jigon gari shi zan bai watse ba,

Noma gand’on k’asa ta zan ba ta yoye ba,

Gari duka in babu noma ba zai zauna ba,

Barden duniya a ko’ina ba d’wad’i ba,

Kai ka tashi mu yo girgiza gaba d’aya ga manoma.

A kirarin Ak’ilu Aliyu cewa ya yi:

Noma kashe bashi d’an Sabtau,

Wawwargaza yunwa d’an k’artau,

Mai dad’d’aga martabar Nomau,

Madalla abin kirari nau

Kai ba dodorido ne ba.

A ra’ayin Sani ‘Dambold’o noma layun tsari ne.

Jagora:        Kun san layun tsari gare ni

:         Dunk’ullan dawo gami da noma

:         Kowas sha su ba ya jin kasala,

:         In ko an yi gardama a dama

Gindi: Rabbana Allah ka taimake mu

Mu Samu bitar kai cikin tukunya.

Burinmu, a zabura zuwa gona, kamar yadda Aikau Jikan Tayawa ke yi (in ji makad’i Amali). Yin haka, zai sa a kauce wa tarkon ‘Dan’anace (a wak’ar Mijin Danjimma). Ai sai damina ta yi kyawo su Hantsi Hore ke nuna buwaya (in ji Gambo Mijin Kulu).

Yaba kyanta tukunici:


          Tsananin ba noma da manoma muhinmanci ya sa mai girma Gwannan Jihar Sakkwato Alhaji (Dr) Aliyu Magartakarda Wamakko (Sarkin Yamman Sakkwato) ya ba k’ungiyarmu mota. Babu shakka, a ko’ina ake taron manoma, manoman sakkwato na daban ne domin ba mu ta’ba jiran mai kai mu ba, sai dai mu nemo direba. Haka kuma, a fagen huld’a da manoma mai girma kwamishinan ma’aikatar gona da babban sakatarensa da daraktocinsu da sauran ma’aikatansu sun share muna hawaye. Ba su ta’ba yi wa manomi kallon wa ya aiko ka ba. Ba mu ta’ba kai buk’ata ta barkace ba. Ba mu ta’ba neman agaji suka yi kasala muka koka ba. Duk da haka muna rok’on:

  1. A k’ara tallafa wa manoma ga sayen kayan da suka noma domin su k’ara k’arfin guiwa.

  2. A k’ara fito muna da iraruwan shuka da ke yi wa sauyin yanayinmu barazana.



  • A cece mu a bud’a kamfunan hukuma na sarrafa abincinmu domin jahar Sakkwato ta sake jagorancin jihadin noma a Nijeriya.



  1. A rik’a kula da wak’ilcinmu a kwamitocin jaha da na tarayya domin mu ke ba da agajin farko gabanai a kur’ba nagaske (Shayi).

  2. A fito da wani shirin da zai taimaka wa matasan da suka kammala karatu na noman rani da damina.


Nad’ewa


          Da k’ara yawaita ma’aikatau tsaro da fad’ad’a asusun tsaron k’asa, da sayen makamai, gara a fito da wani salon kashe rabin kud’in ga noma. A iya tunaninmu, k’abu k’asar da ke sayar da abincinta ta saye makamai. K’asashen da ke sayar da makamai abinci suke saya wa jama’arsu. Idan ba a shafa ba, an yi lokacin da dukkanin d’awainiyar wannan k’asar a wuyan Arewacin k’asar nan yake da ya ginu a kan noma. Mak’iya sun lura da cewa, abincin da muke da shi wani makami ne da ba ya yak’uwa. Don haka ake son a tarwatsa muna manoma da makiyayya a karkashe su, su gaji k’asar afafa. K’ungiyar AFAN na tabbata wa mai girma Gwannan jihar Sakkwato Alhaji (Dr) Aliyu Magatakarda Wamakko (Sarkin Yamma Sakkwato) cewa, tana baya ga k’udurinsa na k’wato wa Arewa hak’k’inta. Muna tare da kai sai an kar’be goriba ga hannun kuturu. Ka da ka ja da baya, sai an hura wuta kowa ya ga rabonsa. Mun ji an ce, wai, mai d’aki ya san gefen da yake tarara. Mu ko za mu tabbata mai d’akin cewa, mai baibaya ya san wurin da ya toshe makwararar ruwa. Masu cewa, cikin kashi babu wanda ya fi wani wari. Yaran makad’a Narambad’a sun k’aryata su ga fad’arsu:

Jagora:        Da Mai hashin wuta da mai kashin wuta

:         Da mai rabon fad’a da mai had’in fad’a

:         Su duk hud’u sun taru game

:         Ba mu samu guda wanda yaf fi ba.

Yara:          Narambad’a koma ga gaskiya

Mai kashin wuta ya fi mai hashi

:         Mai rabon fad’a ya fi mai gami

:         Ni kan ga irin wadda nag gani

:         Ka san jimina ta fi zar’bi babban guru ko tai masassara.

Gindi :         Ta tabbata gwarzon uban gida namijin jiya ka tsere ‘yan’uwa.

 www.amsoshi.com

Post a Comment

4 Comments

Post your comment or ask a question.