𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, malam Allah ya ƙara daukaka, ya gafartama mahaifa, malam tambayata a nan shi ne, yaya sharia ta yi tanadi wurin tsaftace tufafi, don na ji ana cewa se anfara dauraye tufafi, kafin asa musu sabulu, wasu ma se su ce, za a wanke sau ukku kafin a saka sabulu
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salamu
warahamatullah,
Shari'a ba ta ɗora wa mutum wani
tsari na dole wajen wanke tufafi ba, kamar ɗaurayewa kafin sabulu ko wankewa sau uku
kafin a sa sabulu. Ba a samu hadisi ingantacce ko wata magana daga magaba ta da
ta tabba tar da wannan tsari ba. Abin da shari'a ta tsara shi ne tsaftace
najasa idan tufafi sun ƙazantu da ita, kuma a nan ne ake magana kan yawan
wankewa.
Idan tufafin ba su ɗauki najasa ba, kawai
datti ne na gumi ko ƙura, to ana wankewa ta duk hanyar da ta dace, da sabulu
ko ba tare da shi ba, da ɗaurayewa kafin sabulu
ko bayansa, komai ya halatta. Tufafin dake da datti kawai ba najasa bane, don
haka tsarkinsu ya tabba ta, kuma sallah da su ta inganta, sai dai an fi so
mutum ya yi sallah cikin tsafta. Allah ya ce
وَثِيَابَكَ
فَطَهِّرۡ
"Kuma tufafinka,
ka tsarkake su" (Muddaththir: 4).
Malamai sun fassara
wannan da tsarkake su daga najasa da kuma tsaftace su. Idan najasa ce ta taɓa tufafin, to sai a
cire ainihin najasar dake jikinsu, ko ta wace hanya, da ruwa ko sabulu ko wani
abu mai cirewa. Bukhari da Muslim sun ruwaito a hadisin Asma'u da na yi bayani
akai a amsan da ya gaba ta, inda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce a
goge jinin, a murje shi da ruwa, a wanke shi. Ba a ambaci sabulu ba, kuma ba a
ambaci adadin wanke wa ba. Kuma Hana fiyya, Malikiyya da Shafi'iyya sun ce idan
najasar ta tafi ta hanyar wankewa sau ɗaya, ta wadatu, sai dai wasu sun fi son a yi
sau uku don kwanciyar rai. Hanabila kuma a wata riwaya suna ganin sau bakwai, amma
hujjar wannan tafi ƙarfi ne kawai a kan najasar kare (Muslim 279), wato
lokacin da kare ya lasa kwano. Sauran najasa kuwa, ana duba ne ko ta tafi ko
a'a, ba adadi ba.
Don haka, wanda yaji
ana cewa dole sai an ɗauraye kafin sabulu
ko sau uku, wannan bashi da tushe a shari'a, ra'ayi ne ko al'ada ce ta wasu
mutane. Idan mutum yana son yin haka don ya tsaftace tufafinsa, ba laifi, amma
kada ya mayar da shi abin wajibi ko sharaɗin sallah. Allah ya sa mu dace.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.