Ticker

6/recent/ticker-posts

Maza Ma Suna Fama Da Jinnul Ashiq?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum Shin maza ma suna fama da matsalar Jinnul Ashiƙ kuwa malam?

MAZA MA SUNA FAMA DA JINNUL ASHIƘ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Kwarai kuwa, tunda aljanu ba iya jikin mata suke iya shiga ba. Saboda haka maza suna iya fama da matsalar Jinnul Ashiƙ (الجن العاشق). Shi namijin ne Ashiƙ (العاشق), ita kuma macen ana ce mata Ashiƙa (العاشقة). Ma’anar Ashiƙ ita ce namiji mai tsananin so, yayin da Ashiƙa take nufin mace mai tsananin so. Kowanne mutum da irin yadda suke zuwa masa, kuma ba kowacce matsala bace za a dinga danganta ta ga matsalar aljani. Dole akwai bukatar bincike, kuma mu Musulmai ne, akwai ƙaddara da Allah ya tsara wa bawansa. Amma a takaice ga wasu alamomi guda 15 na Jinnul Ashiƙ.

1. Rashin sha’awar aure duk yawan shekarun mutum, rashin son kwanciyar aure sam-sam.

2. Ƙin mikewar gaba sanda kayi nufin kwanciyar aure.

3. Ƙin fitowar ruwa yayin kwanciyar aure, domin aljanin yana iya zama a cikin marainan mutum.

4. Saurin gajiya yayin kwanciyar aure.

5. Jin motsi kamar tafiyar wani abu a gaɓoɓin haihuwa yayin kwanciyar aure.

6. Rashin biyan bukata a shimfiɗa.

7. In ka yi nufin yin kwanciyar aure sai bacci ya ɗauke ka.

8. Da ka yi niyyar yin jima'i kawai sai ka ji ka kawo tun kafin ka fara.

9. Komawar gaba da maraina su shige ciki.

10. Yawan ciwon kai, ɓacin rai mara dalili, faɗuwa gaba, da dai sauran su.

11. Haka kawai sai ka ji ka tsani matar ka ko budurwrka.

12. Yawan mafarki kana saduwa da wata mata.

13. Yawan samun matsaloli a duk inda ka je neman aure, sai maganar ta lalace.

14. Za ka dinga mafarkin wata tana wasa da kai.

15. Matsananciyar sha'awa da tsoron mata.

Wannan shi ne a takaice. Don Neman shawarwari ko magunguna a tuntubi wannan number: 09030633961

Allah ya tsaremu.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments