Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Zina Da Kanin Miji

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Aassalamu alaikum Mallam na samu matsala ne a rayuwata ina zaune da mijina shekaranmu 7 da aure akwai kaninsa da yake bibiya ta malam tun bana kulashi har ya kai yanzu muna wasa da shi. Na yi-na yi ya bari yaki bari. Har ya saba in ya shigo ya danne ni ya yi zina da ni har sai ya biya bukatansa a kaina kuma ba na iya ce masa komai. Malam a taimaka mun da addu’oi da shawarwari.

HUKUNCIN ZINA DA ƘANIN MIJI

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam. Hakika kin aikata kuskure babba. Domin kuwa bayan shirka babu wani zunubi mafi girma awajen Allah kamar zina.

Ya zama wajibi kiji tsoron Allah ki dena domin kuwa wannan laifin zai iya janyo miki bala’i da tozarta da wulakanta dake da danginki da iyayenki tun daga nan duniya. Aranar lahira kuma Farjin naki da kike zinar da shi, da kuma sauran gabobin jikinki sune zasu tona asirinki agaban Zatin Allah, ga dukkan halittu suna kallonki.

Za ta yiwu ki samu ciki ta dalilin wannan Zinar, kuma ki shigo ma mijinki da wannan cikin (Ma’ana ba zai gane cewa cikin ba nasa bane). Alhali Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “DUK MATAR DA TA SHIGO MA WASU MUTANE ƊAN WANI WANDA BA CIKINSU YAKE BA, TO ITA BA KOMAI BACE AWAJEN ALLAH. KUMA (ALLAH) BA ZAI SHIGAR DA ITA ALJANNARSA BA… “ (Nisa’iy hadisi na 3481, Abu Dawud Hadisi na 2263).

Shi kuwa wannan Ƙanin Mijin naki yaci amanar Allah da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam) Kuma yaci amanar Ɗan'uwansa (wato mijinki). Kuma yana daga cikin mutanen da Allah yake yin tsinuwa agaresu. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya gaya ma Sahabbansa cewa “WALLAHI MUTUM YA YI ZINA DA MATAYE GUDA GOMA, SHI YAFI SAUKI AGARESHI (WATO SAUKIN AZABA AKANSA) FIYE DA YA YI ZINA DA MATAR MAKOBCINSA”. (Imamu Ahmad da Tabaraniy ne suka ruwaitoshi). A cikin riwayar Ibnu Abid dunya kuma daga Sayyiduna Abdullahi ‘dan Umar (ra) : “WANDA YA YI ZINA DA HALAL ƊIN MAKOBCINSA (WATO MATAR MAKOBCIN KO KUYANGARSA) ALLAH BA ZAI DUBESHI A ARANAR ALƘIYAMAH (WATO BA ZAI MASA KALLON RAHAMA BA) KUMA BA ZAI TSARKAKESHI BA. KUMA ZAI CE MASA “SHIGA WUTA TARE DA MASU SHIGARTA)”.

To in dai haka lamarin yake akan matar Makobci, to yaya kuma matar Ɗan'uwa? Saboda guje ma faruwar irin wannan Fasadin shi yasa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce : “KADA WANI MUTUM YA KEƁANCE TARE DA WATA MACE, FACHE SAI TARE DA MUHARRAMINTA”. Sai wani ya ce “Ya Rasulallahi shin Makusancin Miji fa?” Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce “MAKUSANCI AI SHI NE MUTUWA” (Wato shi ne yafi ɓarna kenan).

Abinda Za kiyi Shi ne: Da farko ki tuba zuwa ga Allah ki janye jiki daga wannan kwarton fasikin dake zuwa miki. Ki hanashi shigowa amma idan bai hanu ba, Ki sanar ma mijinki cewa lallai ya hana wannan Ƙanin nasa shigowa inda kike. Ki rika tuna lahirarki da kuma tsayuwarki agaban zatin Allah. Da kuma kusancin Allah gareki akoyaushe. Ki sani cewa Biyan bukatar Sha’awar Minti biyar za ta iya janyo miki Wulakantar duniya da lahira. Ki tuna rayuwar yaranki da kuma tarbiyyarsu. Kuma ki dubi amanar Mijinki da kike ci, Ki Yawaita Istighfari da Azumin nafilah domin samun tsarkaka daga wannan alfashar.

Idan Mijinki ba mazauni bane, gara ki matsa ki bishi wajen da yake aiki ku zauna achan domin samun tsira da Imaninki da mutuncinki. Ki rika yin wannan addu’ar domin nisanta kanki daga alfasha

اللَّهُمَّ جَنِّبْنِي مُنْكَرَاتِ الْأَخْلَاقِ، وَالْأَهْوَاءِ، وَالْأَعْمَالِ وَالْأَدْوَاءِ

Allah ya sawwake ya gafarta miki ya shiryeki ya tsamoki daga kowanne laifi, tare damu bakiɗaya.

WALLAHU A’ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments