Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Sallamar Sallah A Zuci (A Boye)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum malam mene ne hukuncin yin sallamar sallah a zuci (a boye)? Wasu sun ce wai zai bayyana sallama ta farko ta biyu kuma ta zama ba ta kai ta farko bayyana ba?

HUKUNCIN YIN SALLAMAR SALLAH A ZUCI (A ƁOYE)

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Dangane da Sallamar sallah mustahabbine liman ya bayyana sallama tafarko sama da yanda zai bayyana ta biyu, ya zo a cikin Almugny na Ibn Qudama, ruwaya da aka Ahmad Allah ya jikansa da rahama (zai bayyana sallama ta farko tabiyu kuma tazama ba takai tafarko bayyana ba) yana nufin ahakkin limami.

Amma mamu anaso yabayyana tafarkone kawai yanda zai jiyarda kansa dawanda yake gefensa, sallama ta biyu zai ɓoyetane, ya zo a cikin Taju wal'ikleel Mamu zai bayyana sallamar farkone kawai, ibnu wahab yaruwaito daka malik, " mamu zai bayyana sallamar farkone yajiyar da kansa dawanda yake gefensa, Anruwaito daka Aliyu: zai ɓoye sallama ta biyu.

Ya zo A cikin Mawahibul jaleel sharhin muktasarul khaleel Mamu Abun da ake nema ahakkinsa shi ne bayyana sallamar farko kawai, amma inba sallamar farko bace abun da akeso shi ne ya ɓoyeta.

Daka cikin Malamai akwai wadanda suka haɗa mutum daya da mamu awannan mas'alar kamar yanda ya zo a cikin Sharhin muktasarul khaleel na malikiyyah

Yana daka cikin sunnoni mai sallah mamune ko limami yabayyana sallamar farko danya sanar da fitarsa daka sallah, dan kada wani ya zo yabishi sallah,

Dan Haka dai kus-kurene mutum yaboye sallamarsa tafarko asallah sunnah shi ne yabayyana sallamar sa tafarko, tabiyu kuma ya ɓoyeta. Amma in yai tafarkon aɓoye sallarsa ta yi sai dai tasamu tawaya wajan cika da kamalar sallar tasa.

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments