𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin ko ya halatta ga mijin yatsotsi gaban matarsa ko ita mace tatsotsi gaban mijinta ko kokuma tasha maniyinsa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Asali dai a
Shari'ance Ya halatta Mace da Miji su yi abin da ake ƙira da suna
(Al-Istimta'u) wato Jindaɗī tsakanin Ma'aurata,
danhaka Ya halatta suji daɗi da junansu yadda sukaga dama, Sai dai abin da Shari'a
ta keɓance ta yi hani
akansa, kamar ace Miji yasadu da Matarsa alokacin da take cikin Jinin al-ada ko
jinin Bīƙi, kokuma Miji yasadu da Matarsa ta duburarta ko
Saduwa da'ita lokacin da take yin Azumin-Farilla, danhaka ke nan idan Miji yatsõtsi
Farjin-Matarsa ko ita Mace tatsõtsi
azza karin Mijinta Malamai sukace duk Ya halatta, saboda hakan zai
iya shigane cikin Ƙarƙashin hukuncin (Al-Istimta'u) wato Jindaɗī tsakanin Ma'aurata,
Saboda Faɗin Aʟʟaн(ﷻ) cewa
نِسَاؤُكُمْ
حَرْثٌ لَّكُمْ فَأْتُوا حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ
Matanku Gõnakanku ne,
danhaka kuzõwa Gõnakanku ta inda duk kukaga dama: (Suratul Bakara Aya ta 223)
A cikin wata ayar
kuma Aʟʟaн(ﷻ) Ya ce
هُنَّ
لِبَاسٌ لَكُمْ وَأَنْتُمْ لِبَاسٌ للَهُنَ
(Matanku) tufafine
agareku, haka kūma (Mazajensu) tufafine agagaresu. (Suratul Bakara Aya ta 187)
Amma idan yakasance
ana da tabbas ko zatõ mafi rinjaye gameda cewa yin hakan zai'iya haifarwa wani
daga cikinsu wata cūta, kokuma yakasance babu wata cūta da hakan zai haifar sai
dai kawai ɗaya daga cikin
Ma'auratan bayason ayimasa hakan to Malamai sukace bai halatta su yi hakan ba
dan gudun kada acūtar da wanda bayaso ɗin, Sai dai wasu daga cikin Malamai suna
ganin duk dacewa yin hakan ba haramun bane to amma barinsa shiya fi alkhairi,
Amma dangane da magana a kan hukuncin cewa idan mace tana tsõtsar azza karin mijinta har ya kai ga yin inzali (fitar maniyyi) a cikin bakinta, shin ya halatta ta haɗiye wannan ruwan maniyyin ko bai halatta ba?
Alal-Haƙiƙa a nan Malamai
sun yi Saɓani akan wannan
Mas'ala, kuma Saɓanin nasu ya gina ne a kan mas'alar cewa Shin Maniyyi najasa ne ko ba najasa bane?
Malaman da suka tafi akan fahimtar cewa maniyyi najasa ne sukace haramunne mace ta sha, domin ba ya halatta ga mutum musulmi ya ci ko ya sha dukkan abin da ya kasance jinsi.
Sai dai Magana mafi
Inganci kamar yadda wasu daga cikin Malamai suka rinjayar ita ce, cewa Maniyyi
ba najasa bane, to amma Sai dai Malamai sukace duk da kasancewar Maniyyi abune
Mai-tsarki ba najasa ba, sukace bai kamata ace Mutum yasha Maniyyi ba, domin
yin hakan yana daga cikin ƙazanta, kamar yadda bai kamataba aga
Mutum yana shan Majina ba, duk dacewa Majina ba najasa bace
amma ko shakka babu cewa shanta ɗin ƙazantane.
ШΑʟʟΑНΥ-ТΑ'ΑʟΑ Α'Α'ΑʟΑМ
AMSAWA: Mυѕтαρнα
Uѕмαn. 08032531505
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.