Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mijin Da Ya Sadu Da Matarsa Tana Cikin Idda

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum Malam miji ne ya saki matarsa saki ɗaya, amma sai ya ce ta zauna a gidansa ta yi iddah, to tana iddar kuma ya je mata (ya sadu da ita) kamar sau uku sai daga baya ya ga ta yi jini uku sai ya ce wai iddarta ta kare za ta iya tafiya gida. to ya ya wannan mu'amalar da ya yi da ita akwai aure ko ya lalace sai an sake sabon daurin aure?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Idan mutum ya saki matarsa, kuma wannan sakin ya kasance shi ne na farko ko na biyu to ba ta fita daga idda ba, idan ya so zai iya maido ta da furuci, misali ya ce na maidoki ko na cigaba da rikonki. Ko ya maidata ta hanyar wani aiki da yake nufin mayarwa, kamar ya kusanceta da niyyar mayarwa to mayarwar ta yi.

Iddar macen datake haila shi ne: Al'ada uku (jini uku) idan ta samu tsarki daga wannan jini ukun ta yi wanka, to tagama iddarta.bIddar macen da ba ta haila saboda yarinta ko ta daina hailar, wata uku ne za ta yi tagama iddarta. Iddar mai ciki kuwa shi ne ta haife abin da ke cikinta, abin da ya gudana na jima'i bayan wannan aikin haramun ne.

Wajibine Wannan mijin yatuba zuwaga Allah maɗaukakin sarki a kan afkawa jima'in da ya yi tareda ke, bisa rashin kudurce komai na dawo dake ba, kuma ya zama wajibi Ku sake daura wani auren da Sharuddansa na waliyyi da shedu da siga da sadaƙi idan kowannenku ya na kwadayin hakan.

Ba ya halatta a gareshi ya sake kusantar ki, harsai ansake ɗaura muku aure sabo.

Saboda haka wannan kusantarki daya yi ba tareda ƙudurce ya maidake ta sigogin da malamai suka tattauna wanda suke nuna mutum yadawo da matarsa ba, haramun ne yanzu agareshi ya sake yi miki duk wani abu da ya halatta tsakanin miji da matarsa harsai an ɗaura muku sabon Aure da sadaki da shaidu da waliyyi.

WALLAHU A'ALAMU

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments