𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum mallam miji ne kullum in dare ya yi sai dai ya ɗauki waya har wajen sha-biyu ba ruwansa da matarsa kuma babu fada haka kawai har ya kai sun yi wata huɗu yana kallonta ita ma haka in ta matso kusa da shi ya yi ta fadamata maganganu har sai ta yi kuka ya ce shi zai iya shekara babu mace kuma iyayensa sun masa fada ya ki ya daina Dan Allah mallam a ba mu shawara
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Bai halatta ace haka
kawai miji ya kauracewa matar sa wajen a kwanciya ba, in dai ba wai laifi ta yi
yake son ladabtar da ita wannan hanyar ba, idan laifi ta yi yake son ladabtar
da ita da nufin kaurace mata domin ta gyara halin ta toh wannan ya halatta, nan
ma shi wannan hukuncin iya saduwa ne kuma kada ya ɗauki lokacin da zai
iya cutar da rayuwar ta.
sa'annan haramun ne
ya ce ba zai ba ta kulawa ta magana da murmushi ko wasu abubuwa sama da kwana
uku kamar yadda hadisi ingantacce ya haramta mutum Musulmi ya kauracewa ɗan'uwan sa sama da
kwana uku.
Sabida haka in dai
domin ladabtarwa ne ya kaurace mata, toh ba haramun bane mutum ya kauracewa
iyalin sa a wajan saduwa na kwanakin da ya ɗauka mata sai dai ba'a son kwanakin su yi
yawa kamar misalin ace a ɗauke watanni ba ruwan
sa da ita, wannan kuskure ne, sabida haka ba wai sai lokacin da ya ga dama zai
dawo gare ta ba, domin abubuwa guda biyu.
1. Wajibi ne ga miji
ya tausasawa matar sa ya yi mata rangwame ya dunga saduwa da ita gwargwardon
bukatar ta gwargwadon ikon sa. An tambayi Shaikul Islam ibnu taimiyyah
Alharrany Rahimahullah cewa, dangane da miji idan zai iya hakuri da saduwa da
iyalin sa wata guda ko wata biyu, shin yana da laifi ko ba shi da laifi? shin
miji zai iya neman hakan? Sai ya amsa: Wajibi ne ga miji ya sadu da matar sa da
kyautatawa, saduwa yana cikin mafi girman hakkin ta a kansa, yafi hakkin ciyar
da ita da ke kansa karfi, Saduwa wajibi ce, wasu suka ce wajibi ne duk wata huɗu ya sadu da ita sau ɗaya, wasu suka ce a'a
gwargwadon bukatar ta da kuma ikon sa, kamar yadda zai ciyar da ita gwargwadon
halin sa da ikon sa, wannan kuma shi ne mafi ingancin zantuka guda biyun.
Majmu'u Fatawa (32/271).
2. Duk wanda ya ki
saduwa da matar sa, ba saboda kangarewa umarnin sa da ta ke yi ba, ba kuma wani
hakkin sa ne ba ta ba shi ba na tsawon wata huɗu, zai kasance a cikin hukuncin bawa, za
a umarce shi ya sadu da ita ko kuma ya Sake ta, idan ya ki Sakin ta sai a je
gaban Alkali masanin Shari'ar Musulunci sai ya sake ta.
Malaman majalisar
koli ta Addinin Musulunci na kasa mai tsarki suka ce, duk wanda ya kauracewa
saduwa da iyalin sa sama da watanni uku, idan sabida saɓon ta ne ta hana shi
wani hakki nasa da ke kanta, ta ci gaba da hana shi bayan ya yi mata wa'azi ya
tsoratar da ita akan hukuncin Allah Madaukakin Sarki, da tunatar da ita hakkin
mijin ta a kanta, duk ta ki ji, toh ya halatta ya kaurace mata adadin tsawon
lokacin da yake so, domin ya ladabtar da ita har sai ta dawo tana ba shi hakkin
sa abisa son ranta, ba wai abisa tilas ba.
Hakika Annabi
(Sallallahu Alaihi wasallam ) Ya kauracewa matan Sa tsawon wata guda, sabida
haka idan Namiji ya yi hakan daidai ne, amma wajen yin zance da su ko kula su
wannan haramun ne ya kaurace mata sama da kwana uku.
Amma idan haka kawai
miji ya kauracewa matar sa domin ya cutar da ita ba tare da cewa tana tauye
masa hakkin sa ba, haka kawai don son zuciyar sa da mugunta ya sa bai son
saduwa da ita sai matan banza a waje, toh za a deba masa kwanakin ILA'I, idan
wata huɗu suka wuce bai dawo
ya sadu da matar sa ta farji ba, kuma yana da ikon saduwa da ita ɗin sai ya ki, kuma ba
ta cikin jinin biki ko haila kuma lafiyar ta ƙlau, haka kawai yake
kin saduwa da ita babu gaira ba dalili ba hujja sa'annan ba Jinnu bane a jikin
sa, ko a jikin ta da yake hana shi yin Jima'i da ita ba, toh za a umarce shi da
ya Sake ta, idan ya ki dawowa gare ta kuma ya ki Sakin ta, toh sai a je gaban
Alkali masanin Shari'ar Musulunci sai Alkali ya Sake ta, ko kuma a ba ta auren
nasu idan matar ta nemi hakan, Lajnatul da'imah (20/261-263).
Idan kuma ta ce za ta
iya zama da shi a hakan ba tare da saɓawa Allah gurin yin Zina, ko aikata wani abu
na biyan bukatar ta gurin ta gamsar da kanta har ta cire Sha'awar ta da kanta
ba, toh shikenan sai a bar ta ci gaba da zama da shi a hakan tunda hakan take
so, idan kuma tana cutuwa ba ta son zama da shi kuma a gaba hakan zai sa ta
koma yin zina ko kallon batsa tana biyawa kanta bukata ko ta koma yin madigo,
toh Matakin kenan da za ki dauka wato a je domin a Sake ki, kada ma ki yi
lissafin wai ai Yaran ku 10 ne ya za kiyi da su idan kun rabu, ko kuma ke za
kiyi zaman Yaran ki, toh Yaran ki sune suke Auren ki ne? idan kin faɗi cewa wai ya za kiyi
da Yaran ki kamar kin manta da cewa akwai Allah kenan.
Sa'annan masu cewa
idan Namiji ya ki saduwa da matar sa na watanni ko shekara wai ai Auren su ya
mutu, ku sani cewa kuskure ne wannan ba ku ji fatawar da aka ba ku dakyau ba,
ai ko shekara nawa ne Mijin ki ya yi bai yi Jima'i da ke ba, toh Auren ki da
shi yana nan har abada daram dam, sai dai idan kin je gaba Alkali kika yi masa
bayani Alkali ya umarce shi da ya Sake ki sai ya ki, toh idan Alkali masanin
Shari'ar Musulunci ya Sake ki shikenan sakin ya yi, ko kuma shi Mijin naki ne
ya ce ya Sake ki, toh shi ne fa Auren ki yake mutuwa amma wai don Mijin ki ya
yi shekara ko watanni bai yi Jima'i da ke ba hakan bai nufin cewa Auren ki ya
mutu wai kina iya tafiya gidan ku ki je a sake yin sabon Aure, idan kin yi irin
wannan kuskuren toh kin yi Auri wani kin daura Aure akan Auren mijin ki ne
domin rashin Jima'i da ke bai ɗaukar hukuncin Saki. Allah Ya shirya.
Idan mace mijin ta ya
yi tafiya kuma matar sa ba ta yarda da barin sa gida ba sama da wata shida bai
dawo ba, toh za ta iya yin kara wajen alkali domin ya aikawa mijin ta sakon
wajabta masa dawowa zuwa gare ta, idan ya ki dawowa sai Alkali ya yanke hukunci
akan abun da yake ganin shi ne yafi Saki ko kuma ya ba ta Auren gaba ɗaya. Tafiyar ta sa ta
uzuri ce? kamar fatauci saboda bukatar dukiya ko rashin samun aiki a garin sa,
ko kuma ta rashin uzuri ce ma gaba ɗaya, alhalin uzuri ba wajibi bane ya dawo
kuma ba shi da laifi idan bai dawo ba.
Sabida haka matan da
Mazajen su suke tafiya su fi watanni 6 ko 8 wani ma shekara bai da lokacin
dawowa, ko irin sako me kyau ga Matar bai yi, bai yin chatting da ita ko nuna mata
kulawa alhalin kullum yana online amma ba ruwan sa da ita, bai tura musu kuɗi ko kayan abinci
kullum suna kukan yinwa, bai nuna kulawar sa ko damuwar sa akan iyalan sa da
Yaran sa, toh kina da zaɓin ki na zuwa gurin
Alkali masanin Shari'ar Musulunci kiyi masa bayanin komai idan kina da hujjojin
ki a wayar ki sai ki nuna masa, toh dole ne Alkali ya nemo shi ya dawo ko kuma
ya Sake ki ko kuma ya sa dole ya gyara halin sa, idan ko ya ki yin ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da
Alkali zai gaya masa, toh Alkali ya san hukuncin da zai yi a kansa.
Sabida haka kuskure
ne ke ana cutar da ke, ana tauye haƙƙin ki amma ki ce wai
ke kina zaman Yaran ki ne ko kuma wai za ki koma ne gidan sa ne don Yaran ki,
wannan kalmar ta yi muni sosai wallahi shiyasa dole ne mata ku rika shan
wahala, ba sauki a rayuwar ku domin irin kalmomin da kuke furtawa ba su dace ba
Allah.
Don haka wannan
matakin shi ne yakamata mata su bi domin kaucewa faɗawa cikin halaka na
Zina da biyawa kanki bukatar ki ko shiga madigo, sa'annan ko shekara nawa mijin
ki ya yi bai yi Jima'i da ke ba, toh har gobe Auren ku na nan kada wasu su rude
ki a gaya miki abun da ba da ba shi ba cewa ai Auren ku ya mutu, bai mutu ba
wallahi yana nan, sa'annan waɗannan sune matakan da za ki bi domin samun gyara ko
rabuwa da mijin ki, ko ta gurin manyan sa idan shi mai jin maganar manyan ne,
ko kuma hukumar Musulunci ko Alkali wannan shi ne. Allah Ya tsare Ya sharya.
WALLAHU A'ALAMU
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.