Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mace Ta Sanya Gyale Ko Mayafi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum. Malam ina da tambaya: yawancin mutane suna yawan kallon macen da taki sanya gyale ba ta da kamun kai ko kuma kamar yin hakan babu kyau. To shin mene ne hukuncinsa a addini?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullah.

Hakika kinyi tambaya mai muhimmanci musamman ma idan akayi la'akari da zamanin da muke ciki.

Shi dai tufafin mace musulma ba a kayyade kalarsa ko sunansa ba, amma akwai ƙa'idodin da wajibi ne tufafi (gyale ko maya fi ko riga) ya cikasu kafin ya zama halastacce ga mace musulma.

Misali

1. Wajibi ne tufafin ko gyalen ko hijab ko maya fin ya zamto ya rufe jikinta baki dayansa, kada ya zama dangalalle ko kuma kafafunta ko damatsunta suna bayyane.

2. Wajibi ne Tufafin kada ya zamto mai mutukar jan hankalin jama'a izuwa gareta. Misali kamar tufafi ko maya fi mai yawan kyalkyali, ko wanda aka yi wa ado da abubuwa masu tsada masu ɗaukar hankali kamar zinare, lu'u-lu'u, da sauransu. (waɗannan sai dai a gida ta sanya domin mijinta kaɗai).

3. Dole ne tufafin ko maya fin ko hijabin ya zamto an yishi ne da abu mai kauri ba mai shara-shara ba. Domin tufafi ko maya fi ko hijab mai shara-shara zai iya bayyanar da siffar halittar jikinta. Misali kamar irin gyalen nan na zamani mai shara-shara, shi ba ya rufe jikin mace yadda addini ya yi umurni, kuma yana bayyanar da siffar halittar jikinta. Shi yasa Malamai suke cewa haramun ne.

4. Wajibi ne hijab ko maya fin ya zamto ya ishi jikinta, kada ta sanya matsatsun tufafi ko dangalallen hijab ko maya fi... Haka nan ta guji sanya wando ko riga matsattsu ko da atsakanin muharramanta ne.

5. Haramun ne sanya tufafi irin wanda mazaje ne kaɗai suke sanyawa. Domin Annabi ﷺ ya tsine wa duk matar dake yin shigar maza, da kuma mazajen dake yin shigar mata.

6. Haramun ne mace ta shafa turare ko shafa mayuka masu tashin Ƙamshi. Domin wannan zai iya jan hankalin mazaje izuwa gareta. Za ta sanya turare ne kaɗai alokacin da take zaune agida daga ita sai mijinta ko muharramanta.

7. Wajibi ne mace ta gujewa duk wani tufafin da wasu mutanen banza kamar fasikai ko kafirai suka shahara da shi, saboda gudun kada mutane su munana zato gareta.

8. Haka nan wajibi ne ta guji sanya wani tufafi ko Hijab ki maya fi ko wata shiga wacce za ta sanyata ta fito dabam a cikin jama'a domin neman shuhura a bainar jama'a.

Domin samun Hujjoji game da waɗannan ka'idodin da bayanan, aduba cikin Alƙur'ani a cikin waɗannan ayoyin

1. Suratul Ahzab ayah ta 59, da ta 53.

2. Suratun Noor ayah ta 31.

3. Suratun Noor ayah ta 60.

Da kuma wadannan ingantattun hadisan

1. Abu Dawud hadisi na 4102.

2. Sahihul Bukhari hadisi na 146 da na 5,149.

3. Sahihu Muslim hadisi na 645.

4. Sunanul Baihaƙiy (juzu'i na 7 shafi na 93).

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments