Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Auren Saurayin Da Yake Neman Budurwarsa Da Zina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu'alaikum, malam ƙawata ke da saurayi tana Kano yana Kaduna ya so su aikata zina har so biyu ta ƙi yarda toh sai kuma yanzu aka ce za a yi mata aure tafitto da miji sai ta fada masa Amma ya ce zai samu lokaci had kassan kwana uku bai ce komai ba ko ta kira baya ɗauka shin meye mafita? Ina godiya

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Abu na farko shi ne ta kara yiwa Allah godiya da har Allah ya sa ba ta biyewa son zuciya da biyewa kaidin saurayin ta wajen yin Zina da ita ba. Da ta yi hakan da ya samu abun da yake so ke nan, da kuma zai ya tafi ya bar ta, tunda daman abun da ya gani yake so ke nan har ya yi karyar cewa zai Aure ta, toh ya samu abun tun a waje, yanzu Auren me zai mata?

Na 2 shi ne, Shawarar da zan ba ta, ai idan ni mãce ce duk lokacin da Namiji ya bijiron min da irin wannan alfashan bai ji tsoron Allah ba, bai ji kunya ta ba, bai ji kunyar Ubangijin sa cewa yana kallon sa ba, toh ina ji wallahi duk son da nake masa koda ace zan mutu idan na rabu da shi, toh na gwammaci daga wannan rana da ya ce min zai yi zina da ni, toh na share babin sa ke nan a rayuwa ta har abada zan rabu da shi, wadda zai zama mijina sannan ya yi min haka kuma wai na zo ace min na fitar da mijin aure har na fara tunanin sa? Wallahi hakan ba zai yiwu ba.

Domin wannan ba Namijin da mãce tagari zata Aura har su gina al'umma nagari ba su samu Aljannah, watakila ma aikin sa ke nan yin Zina da yaran mutane, domin duk mai yin zina damuwar sa ke nan ya yi da ɗiyar kowa ko a jikin sa, shi ba Auren zai yi ba zinar ce kaɗai a gaban sa. Ke nan bai kamata ta fara tunanin cewa shi ne zata fitar a matsayin miji har ta kira sa a waya wai ya fito a yi maganar Aure, ai ya san da zai Aure ta amma bai zo neman Auren ta ba sai ya fara da neman Zina da ita, sabida haka matukar miji nagari take son Aura, toh wannan ba nagari bane, idan tana son wadda ko bayan sun yi aure ya je yana neman mãtan banza a waje, toh ta aure shi ya cika wannan siffar.

Duk wadda ya nemi ya lalata rayuwar ki, Yar'uwana wannan ai ba masoyin ki na kirki ko na ƙwarai bane, kuma ba za ki ɗauke shi a matsayin mutumin kirki mai daraja ba, kuma idan kina neman makiyin ki a duniya da lahirar ki toh idan kin same shi shike nan, tunda hakane ke nan wannan bai cancanci ya zama mijin ta ba, sai dai idan itama aikin ta ke nan irin wannan, toh nan kam daiɗai ne, domin Allah Ya ce

الزَّانِي لَا يَنكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً وَالزَّانِيَةُ لَا يَنكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ وَحُرِّمَ ذَٰلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ

Mazinãci bã ya aure fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai. (Suratul Nur Ayata 3).

Tunda haka Allah Ya ce mana sai ga shi kuma tun a wajen wai Ya ce yana son ta amma kuma sai ya fara da cewa su yi Zina kin ga ke nan dãman aikin sa ke nan ga Yaran mutane idan ta Aure shi watakila ta Auri Mazinaci.

Sa'annan idan ma yana yi mãta karya ai yana son ta, kuma so da kauna na tsakanin sa da Allah ne toh gaya mãta haka ne don ta ji daɗi domin ya samu abun da yake so a jikin ta, don wallahi karya yake yi, sabida babu wani Namiji mai tsoron Allah, namiji mai Addini, sannan Namiji mai son mace tsakanin sa da Allah, Namiji wadda yake son wannan Yarin ya ta zama Uwar yaran sa domin su gina al'umma nagari ta dalilin haka su samu Aljannah gaba ɗayan su, Namiji mai kunyar Ubangijin sa ko da ace bai ganin sa, namiji mai kunyar Budurwar sa gurin kiyaye furta mãta kalmomin batsa, namiji wadda ya san darajar Iyayen Budurwar sa, Namiji wadda ya san Ƙima da darajar ita budurwar, Namiji mai tausayin Budurwar sa wadda bai son ganin ta aikata saɓon Allah, namiji wadda bai son ganin Budurwar sa a cikin halaka, toh wallahi ba zai taɓa tunanin yin zina da ita ba, kai ko hannun ta yana jin tsoron ya kama balle ya furta mãta kalmar batsa bal ma a je har ya ce zayi zina da ke.

Kai har ma ya buɗi baki da kansa a waya ko a zahiri kina kallon sa yana kallon ki wai ya cewa budurwar sa su yi Zina, Wallahi babu wani Namijin da zai yi wa Budurwar sa irin wannan, duk Saurayin da ya ce miki yana son ki tsakanin sa da Allah yana kaunar ki tsakanin sa da Allah sannan sai ya ce ku yi Zina, toh wallahi dãman karya yake yi ba son ki yake yi ba, kuma ba Auren ki zai yi ba, kawai bukatar shi ke nan shi ne abun da ya bayyana miki a yanzu na cewa ya yi Zina da ke ya tafi ya bar ki.

Ya zubar miki da darajar ki, dãman bai san wannan ba, ya zubar miki da mutuncin ki Ƴancin ki, ƙimar ki, Martaban ki, Budurcin ki, dãman duk waɗannan bai san su kawai abun da ya sani ya yi Zina da ke ya tafi, ya zubar da Mutuncin Iyayen ki, ya ci amanar Iyayen ki, ya ci Amanar Allah da Manzon Allah ﷺ, kuma wai shi ne zai zama Uban yaran ki? Har ya iya rike ki da Yaran ku tsakanin sa da Allah? Haba ƴar'uwar, wadda zai cutar da ke irin wannan, ya ci Amanar Iyayen ki, ya ci Amanar ki, Uwa Uba ya ci Amanar Allah da Manzon Allah ﷺ, kuma shi ne wai zai zama Mijin ki, wadda zai iya aikata irin wannan shi ne idan ya Aure ki ba zai iya cin Amanar ki ba? Ko cutar da ke ba? Ai ba zai yiwu ba. Dole ne ke ma ko ya Aure ki a samu matsala domin abun da ya aikata tun farko, shiyasa Allah Ya ce

وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا

 "Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya." (Suratul-Isra'i: 32).

Allah Ya ce mana kada mu kusancin zina bawai kada mu yi sa a'a kusa da gurin ma kada mu kasance shi, ai sai kin zo gurin ne za ki iya aikata abun toh aka ce kada ma ki matso gurin, amma sai kika ce a'a bari ki nuna masa so da kauna sabida ya gane cewa kina son sa, toh kin mutu tun kwanan ki bai kare ba.

Don haka babu wani mutumin kirki da zai so mãce tsakanin sa da Allah, sannan ya ce wai zai yi Zina da ita kuma wai zai Aure ta karya yake yi. Don haka idan ita mutumiyar kirki ce tana son ta Auri miji nagari wadda za su zauna lafiya na har abada a matsayin mijin ta kuma su gina al'umma Nagari su samu Aljannah, toh ta yi gaggawan share babin wannan ɗan iskan, kar ma ta sake kiran sa a waya, kai ta ma goge duk wani abun da zai sa ta tuna waye shi, sannan ta yi Addu'ar Allah Ya kawo mata Miji nagari mai Addini da tsoron Allah mai son ta tsakanin sa da Allah.

Idan kuma ta ce a'a wancan take so sai ta matsawa kanta dole sai ta Aure shi, toh ina tabbatar miki da cewa sai ta sake dawowa wajen ki ta ce ki nema mata shawara cewa ta ce ya Sake ta, ko kuma ta ci gaba da zama da shi? Domin ta gaji da irin wannan rayuwar Auren da shi. Don haka mafita ke nan ta goge dukkan abun da zai sa ta gani har ta tuna shi har ma ta ji wai ta sake kiran sa ya fito saboda ya zama mijin ta. Subhanallah.

Wannan zamanin namu ba'a aikata zina ba yaya zaman gidan miji yake karewa balle ace tun a farkon nema Saurayi ya fara miki da kalmar zina, ai wannan ai ya bayyana miki dabi'un sa da halayyen sa ne, don haka ba ki bukatar wani bincike mai zurfi a kansa kawai ki rabu da shi, amma idan ya gyara halin sa da dabi'un sa shike nan idan kina son sa a hakan sai ya fito ya Aure ki, amma dai a karon farko kin san waye shi don haka kada ki Aure shi daga baya ki samu cewa ai yana neman mãtan banza a waje ki ce wallahi kema ba ki sani ba sai yanzu, kin yaudari kanki. Allah Ya Shirya. Da fatan kun fahimta?

WALLAHU A'ALAMU.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments