𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aassalamu alaikum. Ina soyayya da wata budurwa har cikin rayuwata da aure nake son ta sai ta zama idan muka haɗu, sai ta ringa nema na da alfahari (zina), ni kuma ina gudun haka. Daga karshe sai ta yi nasara harya kai mu ga yin zina sai na zo muka tuba Amma duk da haka Idan muka haɗu duk yanda zan iya rike Sha'awana sai ta kureni muka sake yin na biyu sai ni kam nasake Neman tuba wurin Allah na yi wa ubangijina alkawarin ba ita ba ma duk macen dake Duniyar Nan ba zan Kara kusantar ta da sunan zina ba in Sha Allahu. Tambaya a nan ita ce;
1. Shin ko Allah ze
amshi tubana dana yi gare shi?
2. Idan na aureta,
zunubin Alfashan (zina) da muka yi yana kanmu ne har yanzu?
3. Idan na yi amfani
da kuɗin da ta ba ni ajiya
na fanshi Al-Ƙur'an na kai Zuwa masallaci Dan Allah ya yafemata dakuma
yazama ladan karatun da za Ayi da shi yakai gareta me hukuncin hakan gareni ni
kuma?
DUK LOKACIN DA MUKA
HAƊU DA BUDURWATA SAI TA RINGA NEMA NA DA
ALFASHA (ZINA)
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumussalam
warahmatullah wabarakatuh
Hakika tabbas zina
babban laifi ne wanda in banda shirka babu laifin da ya fishi girma. Duk matar
da ta yi zina tabbas ta saɓawa Allah, kuma taci amanar kanta, taci amanar iyayenta
da danginta, kuma taci amanar mijin da zai aureta, harma zuriyar da za ta haifa
nan gaba. Kuma in har ta mutu ba ta tuba ba, Allah zai azabtar da ita da irin
azabar da ya yi tanadinta ga mazina ta.
Allah maɗaukakin sarki idan ya
haramta wani abu yakan haramta dukkan wata hanya komai kankantarta da za ta kai
zuwa ga aikata wannan abun. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
وَلَا
تَقْرَبُوا الزِّنَا إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَآءَ سَبِيل
“Kuma kada ku kusanci
zina, lalle ita alfasha ce kuma hanya ce mummuna.”
Wannan aya yana nuna
cewa ba wai kawai zina ce aka hana ba, har ma da duk abin da zai kai zuwa gare
ta ko ya buɗe ƙofarta. Haka kuma
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi gargaɗi mai tsanani game da
mu’amala tsakanin namiji da mace wadda ba ta halatta ba. Kamar yanda Sahabi
Abdullahi bn Abbas (RA) yarawaito cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam) ya ce: “Kada wani namiji ya kebanta da mace, inbahaka sai shaiɗan ya zama na ukun
su." (Sunan At-Tirmidhi da Musnad Ahmad.)
Idan mutum (namiji ko
mace) bai taɓa yin aure ba, sannan
ya yi zina, Za a yi masa bulala guda ɗari kamar yadda yake a Suratu An-Nur aya ta 2
اَلزَّانِيَةُ
وَالزَّانِىۡ فَاجۡلِدُوۡا كُلَّ وَاحِدٍ مِّنۡهُمَا مِائَةَ جَلۡدَةٍ وَّلَا
تَاۡخُذۡكُمۡ بِهِمَا رَاۡفَةٌ فِىۡ دِيۡنِ اللّٰهِ اِنۡ كُنۡتُمۡ تُؤۡمِنُوۡنَ
بِاللّٰهِ وَالۡيَوۡمِ الۡاٰخِرِۚ وَلۡيَشۡهَدۡ عَذَابَهُمَا طَآٮِٕفَةٌ مِّنَ
الۡمُؤۡمِنِيۡنَ
Mazinaciya da mazinaci,
to, ku yi bũlala ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlala ɗari. Kuma kada tausayi ya kama ku game
da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kun yin ĩmani da Allah da Ranar Lahira.
Kuma wani yankin jama'a daga mũminai, su halarci azabarsu. (Surah: An-Noor,
Ayat: 2).
Malaman fikihu da
yawa sun tafi a kan cewa za a kore shi daga garinsu na tsawon shekara ɗaya (bisa koyarwar
Sunnah).
Idan mutum ya taɓa yin aure hukuncinsa
a shari'ance shi ne a jife shi da duwatsu har sai ya mutu. Wannan hukunci ya
tabba ta ta hanyar Sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da kuma
ijma'in malamai.
Kafin a zartar da waɗannan hukunce-hukunce
na shari'a (waɗanda hukuma ce kawai
take da ikon yinsu, ba daidaikun mutane ba), dole ne a sami ɗaya daga cikin
abubuwa biyu:
1. SHAIDU HUƊU: Mutane huɗu adalai (maza
musulmi) su shaida cewa sun ga lokacin da jima'in yake faruwa fili-fili. Idan
wanda ya yi zargi bai kawo shaidu huɗu ba, shi da kansa za a yi masa bulala 80
saboda laifin ƙazafi (yin ƙaryar zargi).
2. FURUNCI (IKRARI):
Wanda ya yi zinar da kansa ya yi ikrari da bakinsa a gaban alkali (yana da
hankalinsa kuma ba tare da an tilasta shi ba). Mafi alheri ga wanda ya yi
zunubi a asiri shi ne ya rufe kansa, ya nemi gafarar Allah ba tare da ya
tallata wa mutane laifinsa ba.
Idan ka yanke
shawarar aurenta, Wajibi ne ta ga al'ada a kalla sau ɗaya kafin a daura
aure, domin a tabba tar ba ta dauki juna biyu daga zinar da kuka yi ba. zunubin
da kuka yi a baya ya riga ya wuce muddin kun yi tuba ta gaskiya. Musulunci ya
koyar da cewa "Mai tuba daga zunubi kamar wanda bai taɓa yin zunubin ba
ne". Idan mutum ya yi tuba na gaskiya (Tauba tan Nasuha), ya yi
da-na-sani, ya daina, kuma ya kuduri niyyar ba zai sake komawa ba, Allah mai
gafara ne da jin ƙai. Duk wanda ya tuba daga zunubi kuma ya yi nadama
sannan ya nisanci wannan laifin, to Allah zai gafarta masa wannan laifin koda
kuwa ya yi shekaru masu yawa yana aikatawa.
Manzon Allah (sallal
Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam) Ya ce "Hakika Allah yana shimfida
rahamarsa da daddare domin karɓar tuban waɗanda suka aikata zunubbai da rana. Kuma yana
shimfida rahamarsa da rana domin waɗanda suka aikata zunubai cikin dare su tuba.
(Ba zai gushe yana yin haka ba) har zuwa sanda rana za ta ɓullo daga
mafadarta".
Allah Madaukaki ya ce
...وَتُوبُوا
إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Kuma ku tũba zuwa ga
Allah gaba ɗaya, ya ku mũminai!
Tsammaninku, ku sami babban rabo. (Suratul Nur Aya ta 31).
قُلۡ
يٰعِبَادِىَ الَّذِيۡنَ اَسۡرَفُوۡا عَلٰٓى اَنۡفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُوۡا مِنۡ
رَّحۡمَةِ اللّٰهِ ؕ اِنَّ اللّٰهَ يَغۡفِرُ الذُّنُوۡبَ جَمِيۡعًا ؕ اِنَّهٗ هُوَ
الۡغَفُوۡرُ الرَّحِيۡمُ
“Kace Musu: Ya Ku
Bayina Wadanda Suka Yi Wa Kansu Barna akan rayukansu! Kada Ku Fidda Tsammani
Daga Rahamar Allah. Hakika Allah Yana Gafarta Dukkan Zunubai Baki Ɗaya, Lalle Shĩ,
Shĩ ne Mai gafara, Mai jin ƙai."
(Suratuz-Zumar, Aya Ta 53).
وَالَّذِيۡنَ
لَا يَدۡعُوۡنَ مَعَ اللّٰهِ اِلٰهًا اٰخَرَ وَلَا يَقۡتُلُوۡنَ النَّفۡسَ
الَّتِىۡ حَرَّمَ اللّٰهُ اِلَّا بِالۡحَـقِّ وَلَا يَزۡنُوۡنَ ۚ وَمَنۡ يَّفۡعَلۡ
ذٰ لِكَ يَلۡقَ اَثَامًا يُضٰعَفۡ لَهُ الۡعَذَابُ يَوۡمَ الۡقِيٰمَةِ
وَيَخۡلُدۡ فِيۡهٖ مُهَانًا ۖ اِلَّا مَنۡ تَابَ وَاٰمَنَ وَعَمِلَ
عَمَلًاصَالِحًـا فَاُولٰٓٮِٕكَ يُبَدِّلُ اللّٰهُ سَيِّاٰتِهِمۡ حَسَنٰتٍ ؕ
وَكَانَ اللّٰهُ غَفُوۡرًا رَّحِيۡمًا
Kuma waɗanda ba su kiran wani
ubangiji tare da Allah, kuma ba su kashe rai wanda Allah Ya haramta face da
hakki kuma ba su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da azaba, A riɓanya masa azaba a Ranar
Alkiyama. Kuma ya tabba ta a cikinta yana wulakantacce. Sai wanda ya tũba, kuma
ya yi ĩmani, kuma ya aikata aiki na ƙwa rai to, waɗancan Allah Yana musanya
miyagun ayyukansu da masu kyau. Allah Ya kasance Mai gafara Mai jin ƙai. (Suratul Furƙan: Aya ta 68–70).
Bai halatta ka taɓa ko ka yi amfani da
kudin ajiyar da aka baka ba tare da izinin mai kuɗin ba, ko da kuwa don kyakkyawan aiki
ne kamar siyan Alkur'ani ko sadaka. Wannan ya saɓa wa ka'idar rike amana a Musulunci.
Ba za a taɓa gina lada ko neman
gafara a kan abin da aka karba ba tare da izini ba. Wajibi ne ka mayar mata da
kudinta cikakku ba tare da ragi ba.
Idan kana son yi mata
kyakkyawan fata ko neman gafara, yi amfani da kudinka na halal ka sayi
Alkur'ani ɗin ka kai masallaci,
ko kuma ka nemi izininta kafin ka yi amfani da kuɗin nata.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.