Cite this article as: Bakura, A. R., & Sani, A-U. (2026). Zuwan Turawa da sauye-sauyen al'amura a ƙasar Hausa: Matashiya daga rubutattun ƙagaggun labarai. Paper presented at the 10th Annual Conference of the Lagos Studies Association, Lagos, Nigeria.
ZUWAN TURAWA DA SAUYE-SAUYEN AL’AMURA A ƘASAR HAUSA: MATASHIYA DAGA RUBUTATTUN ƘAGAGGUN LABARAI
Na
Adamu RABI’U BAKURA Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Phone: 08064893336
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara,
Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Paper presented at the 10th Annual Conference of the Lagos Studies Association (LSA) on "The State of African Studies in the 21st Century: The Lagos Studies Association @10," held in hybrid format (Lagos and virtual), June 16–20, 2026.
Tsakure
Manufar
wannan takarda ita ce fito da sauye-sauyen da aka samu a ɗabi’un Hausawa a sanadiyyar zuwan Turawa. Takardar ta yi
la’akari da cewa, kafin cuɗanyar Hausawa da
wasu al’ummomi na kusa da na nesa, suna da hanyoyin ilmantarwa waɗanda suka zama sinadarin gina ɗan’adam
bisa kyakkyawan godabe. Bugu da ƙari, Hausawa suna da tsarin tattalin arziki da shugabanci da
kuma yanayin zamantakewa mai kyau. An yi amfani da hanyoyin bincike waɗanda suka haɗa da, karance-karancen ayyuka masu dangantaka da nazarin,
sannan an tuntuɓi waɗanda suke da masaniya game da lamarin da aka tattauna a
kansa. An yi amfani da Ra’in Bayan
Mulkin Mallaka (Postcolonial Theory) a matsayin wata maɓuɓɓuga ta ilimi da
aka ɗora nazarin a
kanta. Aikin da Edward Said ya
gudanar a littafinsa mai suna, Orientalism a shekarar 1978 shi ne ya zama
tushen samuwar ra’in. Takardar ta yi garkuwa da wasu ƙagaggun labarai na
zube kamar, ‘Idan So Cuta Ne’ da ‘Ƙarkon Dabino’ da kuma gajerun
labaran gasar ‘Aminiya Trust 2020’ waɗanda aka samu jirwayen ɗabi’un Turawa a cikinsu. Daga ƙarshe, takardar ta
gano cewa, zuwan Turawa ƙasar Hausa ya wanzar da koma baya ga kyawawan al’adunmu da ɗabi’unmu da
falsafofinmu. Hanyar da aka bi wajen rusa tsarin al’adun ƙasar Indiya, irinta aka yi amfani da ita wajen kawar da
kyawawan ɗabi’unmu da al’adunmu da tsarin shugabancinmu. Lamarin ya
kai ga yau an wayi gari wasu tsirarun jama’a ne kawai suke abin da suka so. Ba
sa kula da maslahar mafi rinjayen al’ummar ƙasa.
Fitilun Kalmomi: Turawa, sauye-sauye, ƙasar Hausa, da ƙagaggun labarai.
1.0
Gabatarwa
Turawa suna
tafiyar da al’amurransu ne a tsare tare da manufa ɗaya a kan
dukkanin al’ummomin da suka yi wa mulkin mallaka. Suna tafiyar da lamuransu
cikin ruwan sanyi da yaudara ko kuma ta hanyar amfani da makaman zamani. Sukan
tsara makidodinsu a cikin tsarin ilimin da sukan ƙaddamar a ƙasashen da suka
mulka – kamar dai yadda suka yi wannan tsarin a Indiya, kamar yadda aka kawo a
ayyukan Kumar da wasu (2014) da Ali (2021) da Shukla (2025) da sauransu
makamantansu.
Tamkar yadda ta
faru a ƙasar Indiya, haka lamarin ya gudana a Nijeriya wadda
farfajiyar ƙasar Hausa take cikinta. Lamarin ya fi ta’azzar a ƙasar Hausa,
musamman idan aka yi la’akari da bayanan da suke biye a cikin wannan takarda.
1.1 Hanyoyin Gudanar da Bincike
Masana sun haƙiƙance cewa, bincike
na ilimi yana buƙatar a fayyace hanyoyin da aka yi amfani da su wajen
farauto bayanan da suke ƙunshe a cikinsa. Farko, wannan takarda ta mayar da
hankali a kan bitar littattafan da aka keɓe domin laluɓo batun da ake
tattataunawa a kai. Har wa yau, an yi amfani da karance-karancen ayyukan da
suke da dangantaka da wannan nazari. An yi haka ne domin samo bayanai
nagartattu.
Bugu da ƙari, takardar ta tuntuɓi mutanen da suke da wata masaniya a kan batun da take
tattaunawa, saboda a ƙara samun haske daga gare su. Waɗannan hanyoyi, sun taimaka wajen haska wa takardar
ingantattun bayanai waɗanda su ne suka
sanya ta kaucewa daga abin da Hausawa suke cewa: “Jita-jita hadisin Bamaguje.”
1.2 Rain Bincike
Ra’i tamkar wata maɓuɓɓuga ce ta ilimi
wadda take daidaita akalar bincike da tunanin da magabata suka assasa. Wannan
dalili ya sa ake buƙatar jingina ayyukan bincike zuwa ga tunanin wani
manazarci, saboda ƙoƙarin samun nagarta. Sakamakon haka, wannan takarda an ɗora ta a kan tunanin Ra’in Bayan Mulkin Mallaka (Postcolonial Theory).
Wanan ra’i dai taron dangin masana ne suka samar da shi.
Ra’in ya samo tushensa ne daga tarsashin ayyukan Edward Said a sanadiyyar wani
littafi da ya rubuta mai take, Orientalism
a shekarar 1978. Ra’in ya mayar da hankali ne a kan fayyace yadda tsarin mulkin
mallaka na Turawa ya yi tasiri a ayyukan adabi da na al’ada. Shi
ne ya sa aka samu tasirin Turawa a
harkokin zamantakewar al’uma kamar na shugabanci da kuma ɗabi’unsu.
Har ila yau, ra’in ya kalli yadda mulkin mallakar Turawa
ya yi tasiri a kan Harshe da Adabi da kuma Al’adun al’umma. Wasu daga cikin
masanan da suka yi ayyukansu bisa tunanin wannan ra’i sun haɗa da, Sapivak (1988) a wani littafinsa mai taken, Can the Subaltern Speak? Shi ma Bhabha, (1994) ya yi amfani da wannan ra’i a wani
littafinsa mai suna, The Location of
Culture.
Mayar da hankali da ra’in ya yi wajen fayyace tasirin da
mulkin mallakar da Turawa suka yi a kan zamantakewar mutanen da suka
mulka, shi ne alaƙarsa da wannan nazari. Sakamakon nazartar tasirin, ya
taimaka wajen fito da yadda al’adun Hausawa suka jirkita a cikin adabin da
Turawan suka koyar da su.
2.0
Halayen Al’ummar Ƙasar
Hausa Kafin Zuwan Turawa
Al’ummar ƙasar Hausa sun yi amanna da mutunci ya fi kuɗi. Irin
wannan aƙidar ce ta sa suka gudanar da ruyuwarsu baki ɗaya wajen
taimakon raunanan da suke cikinsu. Hakan ya samu ne a sakamakon bin kyakkyawar
turbar da addinin Musulunci ya aza su a kanta. Sun kasance masu kirki da
nagartattun halayen da ake buƙatar kowane
kamilin mutun ya mallake su.
Rayuwar magabatan
nahiyar ƙasar Hausa ta kasance cike da mutunci da riƙon amana; da kunya
da gaskiya da tsoron
Allah da mutunta kai da kuma
son juna (Shehu da Sani, 2018 sh. 274). Ganin irin waɗannan
halaye ya sa Canon Robinson ya shawarci Mr. Morel da cewa:
“Duk
wanda zai tafi Nijeriya, idan yana buƙatar
abokin mu’amala na
gari mai riƙon amana, to, ya nemi Musulmi” (Abdullahi, 1985 shf. 11).
Haka a cikin
littafi mai suna: Affairs of West
Africa, an kawo bayanan da Gwamna Lugga da Sir. Bryan Sharwood Smith
suka yi dangane da kyawun tsarin
shari’armu da nagartattun halayen
alƙalanmu (Abdullahi 1985 shf.11).
Tarihi ya
tabbatar da wanzuwar nagartattun shugabanni a farfajiyar ƙasar Hausa. Waɗannan shugabanni
sun samu damar da
za su tara abin duniya ta hanyar haramun, amma suka fi ƙarfin zukatansu. Sun fifita lahirarsu a kan duniya, har aka wayi gari suna
gudun karɓar muƙami (Abdullahi,
1985 shf. 17).
Tun kafin
bayyanar addinin Musulunci a farfajiyar ƙasar
Hausa, Bahaushe bai amince da lamarin jima’i tsakanin namiji da mace kafin ƙulla aure ba. Duk kuwa da kasancewar akwai al’adar tsarance, budurwa takan
je ɗakin saurayinta ta kwana ba tare da wani abin assha ya auku a tsakaninsu
ba. Wannan ne ya sa suke aiwatar da wasu tadodin tsafi domin a tabbatar da
amarya ba ta taɓa sanin ɗa namiji ba gabanin aure. A irin waɗannan al’adun,
idan yarinyar ta yi jima’i da wani kafin auren, za ta kunyata a bainar jama’a.
Idan ta ɓoye ba ta faɗa ba za ta mutu, kamar yadda Ibrahim (1985 shf. 5) ya
tabbatar.
Bayyanar
Musulunci a ƙasar Hausa ya kawo tsare-tsaren da suka kare aukuwar
saduwar namiji da mace kafin aure. Hausawa kuma suka rungumi lamarin hannu
bibbiyu. Turawa ma da kansu sun ba da tabbacin haka, inda suka bayar da shaidar
cewa: “Musulmin da yake Nijeriya da
Afirka ta Yamma, ya ƙi jinin yin ta’ammali da karuwai. Shi mutun ne mai tsananin kishin
matansa da yin kaffa-kaffa da ‘ya’yansa mata. Ba ya barin su su shiga ko’ina
barkatai kamar tumaki” (Morel,
1911 shf. 225).
Ta fuskar suturce
jiki kuwa, a nan ma Bahaushe ba a bar shi a baya ba, tun kafin zuwan addinin
Musulunci da Turawa. Yayin da Musulunci ya bayyana sai ya daɗa inganta
yanayin suturce al’aurar namiji da ta mace, tare da
fayyace iyakokin jikin da za a bari a fili. Morel ya tabbatar da cewa: “Ɗan Afirka ya fi kyawun gani a cikin kayansa na iyaye da
kakanni, musammam ma wanda yake Musulmi. Irin kayansu sun fi kare lafiyarsu (Morel,1911
shf. 220). Ya kuma bayyana cewa: “Kowane nau’in aiki na wannan zamanin, kayan
da ’yan Afirka suke sanyawa, musamman a sassan Arewacin Nijeriya, ɗan abu kaɗan ne za
a yi musu, sai a aiwatar da aiki da su.”
A cikin irin
wannan halayyar da ke tattare da kyawawan ɗabi’a da
al’adu Turawa suka sami magabatanmu. Abubuwan da suka lura da su, sun haɗa da abin da
suka gani da idanunsu a zahiri, tare da abin da suka nazarta dangane da adabin
Bahaushe da hikimominsa, a cikin sigar rubutun ajami da na Larabci. Turawan sun
yi amfani da kitsattsiyar manufarsu da suka kitsa tun kafin su shigo ƙasashenmu. Sun zo da nufin rusa ruhinmu domin cimma
muradansu. A wajen cimma manufarsu sun yi ƙoƙarin kawar da tsarin iliminmu na al’ada da aƙidojin da muka
gada kaka da kakanni, har muka kasance a yau tamkar yadda suke buƙata.
3.0
Sakamakon Bayyanar Turawa a Ƙasar
Hausa
Yayin da Turawa
suka tabbatar da samuwar makarantun boko a farfajiyar ƙasar Hausa, sun yi ƙoƙarin karkatar da tunanin al’umma ga karatun Islama. Hakan ya sa matasa suka karkata
wajen karatun boko. A makarantun bokon ne suka sami damar cusa wa matasa
nau’o’in al’adunsu da ra’ayoyinsu, ta hanyar karanta littattafan da suka saka a
tsarin manhajar iliminsu. An wayi gari matasan sun kasance suna ƙyamar ilimin addinin Islama, wanda iyayensu da kakanninsu
suke alfahari da shi - sakamakon suna tsammanin samun ƙyale-ƙyalen rayuwar duniya idan suka yi karatun da Turawan suka
zo da shi. Wannan ya wanzar da sauyin tunanin wannan al’ummar da ruhinsu daga
na neman sakamakon lahiri zuwa ga na jin daɗin
rayuwar duniya ta kowace hanya.
Turawa sun kawo
wasu abubuwan da cutarsu ta fi amfaninsu yawa. Haka abin yake musamman idan aka
yi la’akari da munanan halaye da ɗabi’un da aka koya ta hanyarsu. Abubuwan kuwa sun haɗa da: silima
da talabijin da jarida da mujallu da otel-otel da caca. Waɗannan
abubuwan sun zama sinadarin lalacewar matasan wannan al’umma.
Yayin da aka
nazarci ƙunshiyar wainar da ake toyawa a waɗannan
wurare ɗaya bayan ɗaya. Za a yarda cewa, matasan Hausawa a silima da
talabijin ne suka fara fahimtar hanyoyin neman matan banza da yadda namiji yake
sarrafa mace. A can ne suka koyi shan giya da ƙwaya da ganye da nau’o’in caca.
Ta kafar ne suka
koyi yadda ake tsara tayar da tarzoma da rashin gaskiya, da kuma dabarun sata
da fashi da makami da kuma hanyar kashe mutun cikin sauƙi (Kano, 1981 shf. 38). Waɗannan kafofin ne suka yi tasiri a zukatan matasanmu har
aka samu nau’o’in ɓata gari da suke addabar al’umma. Wasu daga cikinsu sun
haɗa da, ‘yan sara-suka da masu bangar siyasa da kuma fashin daji
da dangogin ayyukan ta’addanci.
3.1 Gina
Otel-Otel
Samuwar irin waɗannan
muhallai a ƙasar Hausa ya kawo babbar illa a tsarin al’adun Hausawa. A wuraren ne suke aiwatar da duk nau’in
fasadi da fitsara da suka gani a silima da talabijin. A nan ne sukan tare su
sami kowace nau’in giya ta cikin gida da ƙasashen
waje. Idan sun sha suka yi tatil, hankulansu suka gushe, sai husuma ta tashi a
tsakaninsu wadda take zama sanadin salwantar rayuwa.
A nan ake shirya
nau’o’in caca, a bazzarantar da kuɗaɗe da dukiyoyin da aka mallaka, cikin ƙanƙanin lokaci. Akan
yi hakan ne duk a sanadin gushewar tunani da neman tara abin duniya da gumin
wasu. Sakamakon haka ne gubar rashin gaskiya da rashin amana suka yi kane-kane
a cikin zukatan al’ummar wannan zamani. An wayi gari kunya da tausayi sun gushe
daga zukata, saboda fifita rayuwar duniya fiye da ta gobe ƙiyama.
A nan ne akan
kafa kulob-kulob domin gudanar da shaye-shaye na masha’a da kuma raye-raye. Irin
waɗannan wurare ne sukan zama matattarar
‘yan iska, inda mazambata kan fake su cuci bayin Allah. Mafi yawan matasa mata
da maza ne sukan haɗa guiwa su kafa kulob, domin samun damar sheƙe ayarsu ba tare da wani cikas ba, (Kano, 1981 shf. 39).
3.2 Ƙagaggun
Labarai
Ƙagaggun labarai suna ɗaya daga cikin rukunnan adabin Hausa na zamani. Masana
adabin Hausa kamar, Yahaya, da Wasu (1992) da ‘Yar’adua, (1996) da Malumfashi (2009) sun kira su da suna zube. Shi
ne rukunin farko, kafin wasan kwaikwayo.
Rubutaccen ƙagaggen labari, shiryayye ne da aka tsara cikin azanci da
hikima da yake koyar da dabarun zaman duniya a matakai mabambanta. Wannan
nau’in rubutu ƙirƙirarre ne bai taɓa faruwa ba. An
samar da shi ne domin hannunka mai sanda, tare da faɗakar da
al’umma a kan lamuran rayuwa da suke faruwa na zahiri. Labaran suna iya amfanar
da al’umma ko akasin haka.
4.0
Dalilan Samar da Ƙagaggun
Labarai
Zamani yakan
sauya a sakamakon wasu abubuwa da sukan faru a tsakanin al’umma. Misali, cuɗanyar
al’umma da wata baƙuwar jama’a,
yakan yi tasiri a rayuwar masu masaukansu. Irin wannan ne yakan haifar da
sauyawar ra’ayoyin al’ummar da falsafarsu ta zaman rayuwa. Su marubutan wannan
zamanin sukan kalli ciki da wajen rayuwar al’ummarsu ta lokacin domin mayar da
su bisa turba. Kowane lokaci suka hango an kauce wa madaidaiciyar hanyar da ta
saɓa wa al’adu da ɗabi’un al’ummar, sukan ja hankullansu zuwa ga managarcin
tafarkin rayuwa.
Sauyawar lamura
bayan sake mayar da mulkin ƙasar nan a hannun
farar hula a shekarar 1990, ya haifar da gushewar kyawawan halaye da ɗabi’u.
Wanzuwar gurbin rashin gaskiya da cin amana da handama da babakeri da dukiyar
bayin Allah; a tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka
sun samu gindin zama. Waɗannan lamuran sun yi tasiri matuƙa a rayuwar al’ummar
Arewacin Nijeriya, da kuma marubutanta. Shi ne ya sa bai zama abin al’ajabi ba,
idan marubuci ya rubuta bayanan abubuwan da suke faruwa sakamakon sauyin zamani
wanda cuɗanya da Turawa ya kawo. Abubuwan sun zama alaƙaƙai a tsakanin al’umma, saboda kauce wa turbar da aka gada kaka da kakanni.
A wannan ƙarnin da ake ciki, an samu gwamnatoci da kamfanoni da
jagororin al’umma da
suka buɗe fagagen rubuta ƙagaggun
labaran Hausa, kamar:
1.
Gwamnatin Jihar
Kano, a ƙarƙashin shugabancin
Gwamna Ibrahim Shekarau, wanda ya kafa Hukumar a Daidata Sahu, 4/9/2011.
2.
Aminiya-Trust,
Dambarwar Siyasa 2023.
3.
Arc. Ahmed Musa Ɗangiwa Literary Competition (wanda ake yi duk bayan
shekaru biyu), da dai sauransu.
Daga cikin ire-iren
waɗannan rubuce-rubucen ne muka zaƙulo waɗanda suke
da nasaba da wannan fage. Farko, mun dubi littafin nan mai suna, Idan So Cuta Ne... saboda
muhimmancinsa a wannan ƙarni na 21.
4.1 Idan
So Cuta Ne ...
A tsarin karatun
boko da Turawa suka kawo a wannan ƙasar, ɗaliban
jami’a suna da ‘yancin haɗuwa maza da mata a azuzuwan karatu, ko wajen cin abinci
ba tare da wata doka ba. Idan aka cire dokar da ta hana wa ɗalibi
namiji shiga ɗakin baccin ɗalibai mata, amma ita tana da halin zuwa muhallin namiji (Kano, 1981 shf. 43). Wannan tsarin an gina shi
ne bisa tsarin al’dun Turawa wanda ya ba ‘yarsu ‘yancin jima’i da duk wanda
take so kuma yake son ta. Su a wajensu ba aibu ba ne. Hasali ma suna da
magungunan hana ɗaukar ciki. ‘Yan boko mata sun kwaikwayi wannan muguwar
al’ada, har suka kai matakin da suke hangen sun mallaki ‘yancin yin abota da
duk saurayin da suke so. Irin wannan abotar takan soma ne daga zancen aure,
daga ƙarshe sai a ɓuge ga aikata fasadi, lamarin ya tarwatse sakamakon
yaudara.
Marubuta ƙagaggun labarai sukan dubi yanayin rayuwar al’ummar wannan lokacin, sai su gabatar da littafi domin faɗakarwa da
ilmantarwa tare da kawo hanyoyin daidaita lamura. A littafin Idan So Cuta
Ne... an byyana aukuwar soyayya tsakanin Abdulmalik da Farida, waɗanda suka
yi amanar ƙulla aure a tsakaninsu.
Tsawon lokacin da
suke tare, ba wani abin fasadi da ya taɓa wakana a
tsakaninsu; ko sumbantar juna ba su taɓa yi ba. Damar da
suke da ita ta haɗuwa a lokacin da suke so, ba ta sa sun yi haka ba. Suna
cikin irin wannan yanayin ne Haruna ya kunno kai da rana tsaka ya ƙwace wa Abdulmalik Farida. Sakamakon son da Farida take
yi wa Abdulmalik, ta same shi har ɗakinsa da nufin su aikata fasadi, shi kuwa ya ƙi amsa tayin da ta yi masa. Tsoron Allah da yake tattare
da shi da dauriyarsa, sai ya rubuta wa Farida takarda yana umurtar ta da ta yi
haƙuri ta zauna da mijinta lafiya.
Duk da kasancewar
Haruna ya raba Abdulmalik da masoyiyarsa, bai hana su ƙulla zumunta tsakaninsu ta hanyar haɗa ‘ya’yansu aure
ba. A lokacin ne ɗan Abdulmalik ya auri ‘yar gidan Haruna wadda suka haifa
tare da Farida.
Daga ɗan taƙaitaccen bayanin nan za a fahimci wanzuwar ilimin boko a
tsakanin matasa maza da mata, ya kawar da kunyar da aka gada kaka da kakanni.
Ya kuma haddasa dangogin kaba’ira a tsakanin al’umma. A can da, budurwa ba ta
bin hanyar da ta san za ta yi arba da wanda zai aure ta. Haka shi ma ko bayan
an yi auren, abokansa sun kai shi ɗakin amaryarsa a daren farko, ba mai sanin lokacin da
yake shiga ɗakinta, ballantana sa’ilin fitarsa. Mummunar ɗabi’ar da
Turawa suka kawo a ƙasar nan, ta
hanyar kallace-kallacen silima da talabiji da kuma karance-karancen mujallunsu
da littattafansu na nishaɗi a makarantu da jami’o’i, ita ce ta sauya wannan al’ada.
4.2 Ciki
Da Gaskiya
Wannan labari ne
da Zaharuddeen Ibrahim Kallah ya rubuta a shekarar 2005. An buga labarin a ciki
littafi mai suna: Ƙarkon Dabino wanda
Hukumar a Daidaita Sahu, Shirin Gwamnatin Jihar Kano suka wallafa. Kamar sauran
marubuta, shi ma ya dubi yanayin yadda ƙusoshin gwamnati suke karkatar da kuɗaɗen da aka
keɓe domin gina ƙasa, zuwa ga
aljifansu.
An kawo bayanin
wani matashi mai suna Sabi’u Isa, wanda ya samu aiki a wata hukuma daga cikin
hukumomin jihar Kano. Bayan ya samu aiki, mahaifinsa ya yi masa gargaɗi
tsattsaura dangane da tsare gaskiya da riƙon amanar
da aka ba shi. Ya kuma ƙarfafa masa guiwa
a kan ɗabi’ar riƙon amana da gaskiya komai rintsi (sh. 6-8).
Sabi’u ya fara
zuwa ma’aikatar da aka ɗauke shi aiki da ƙudurin
bayar da tasa gudummawa domin gina al’umma. Bayan Sabi’u ya kai
muƙamin Akanta, ya sami matsala - sakamakon an tura masa
takardar fitar da kuɗin aikin zaizayar ƙasa a
wasu ƙananan hukumomi guda huɗu. An ruɓanya
adadin kuɗin sau biyu, wato miliyan 40 a madadin 20. Ya yi ƙememe ya ƙi sa hannu domin
fitar da kuɗi. Hasali ma Jirge ya bayyana masa ta haka suke samun
abin da suke harka, kuma shi ma akwai kason da za a ba shi. Sabi’u ya tsaya kai
da fata, ya ƙi sa hannu. Lamarin da ya janyo Daraktan ma’aikatar ya
fusata, har ya zama silar mayar da shi saniyar ware. Ba a komai da shi, hatta
masinjan hukumar ya fi shi walwala (shf. 9-10).
Abokansa suna
zargin sa da rashin ba da haɗin kai wajen wasoson dukiyoyin al’umma, har ta kai Lawal
yana ce wa Sabi’u:
Abokina
mun rasa yadda za ka dawo kan hanya, yanzu duk cikin abokanmu kai ne ba ka
mallaki gida ba, gwanda yanzu ma ka sayi wannan tsohuwar motar. Koyaushe kai
nake ɗora wa wannan laifi, na sha ji daga mutane suna cewa, ka ƙi yarda a yi da kai. Ya kamata ka sani yanzu zamani ya
sauya. Idan ba ka bai wa abokan aikinka haɗin kai
ba, to za ka dauwama a inda kake. (shf. 12 -13)
Jin wannan
mummunar huɗubar da Lawal ya yi masa ta sa Sabi’u murmushin mamaki,
har yake cewa:
Lawan ke
nan, wato kana ganin cin hanci ne zai yi mini maganin matsala. Ai komai ɗaga
hankalina, arziki na Allah ne. Ban fara aiki da irin wannan manufa ba. Ka sani
tun muna makaranta nake da wannan aƙidar. Zan
so kai ma ka yi tunanin wannan maganar. Na ɗauka muna
aiki ne don cigaban jiharmu da mutanenmu. Kana ganin ya dace a fitar da kuɗi za a yi
wa jama’a aiki, sannan wasu tsirarun mutane su yi kwana da kuɗin. (shf. 12 -13)
Ko da Turawa suka
same mu, sun tarar muna da tsarin iliminmu na addinin Islama wanda ya horar da
mu ɗabi’un riƙon gaskiya da
amana. Ya hana mu yaudara, yayin da waɗannan ababen sun
kasance al’adu ne na Turawa. Shi kuwa tsarin iliminsu da falsafarsu abubuwan da
suka ƙunsa ke nan. Shi kansa mulkin mallakar da suka kawo a ƙasashen da suka mamaye, tattare yake da su. Sakamakon
haka, duk ƙasar da suka kutsa da wannan gubar ce suke rusa ruhin al’ummarta, su kawar da imaninta. Irin wannan gubar ba ta
tsaya ga ‘yan boko kawai ba, ta yi naso har a cikin ruhin sauran al’umma. Shi
ne ya sa wasu suka karkata wajen neman ƙulla
dangantaka da irin waɗannan mazambata, ba manufarsu mutanen kirki ba.
Marubucin ya nuna
Sabi’u yana neman Asabe da aure, amma saboda ba ya cikin jinsin mayaudara, sai
aka hana shi aka ba wanda bai kai shi matsayi ba, wato Bashari. An yi haka ne
domin shi Bashari yana cikin sahun mayaudara sakamakon tasirin rashawa da cin
hanci (shf. 13). Hasali ma abokansa suka ba shi baya, sun ɗauka ba
shi da ƙashin arziki. Su kuwa al’ummar unguwarsu cewa suke, tsabagen rashin gaskiyarsa ne
ya hana shi tsinana komai a rayuwarsa, idan aka yi la’akari da aikinsa (shf. 14).
Marubucin ya nuna
Sabi’u ya bar aikinsa, cikin ikon Allah ya sami wani aikin a ƙarƙashin Ƙungiyar Agaji ta Gwamnatin Amurka. Ya sami sauyi cikin ɗan lokaci
kaɗan. Hakan ya sa mahaifinsa ya kira shi, ya ce masa ya tabbata ɗa nagari,
kuma yana sane da duk lamarin da yake faruwa a gare shi a wajen aikinsa. Ya ƙara jaddada masa cewa, matuƙar ya tsare gaskiya, Allah ba zai tozarta shi ba (shf. 15-16).
4.3
Dambarwar Siyasa
A cikin littafin
an kawo gajerun labaran Gasar Aminiya Trust 2020 waɗanda
marubuta daban-daban suka gabatar. Littafin ya ƙunshi sauyin da zamani ya wanzar a ɓangaren jan
ragamar tafiyar da mulkin al’ummar ƙasar.
Kafin bayyanar Turawa, ana tafiyar da lamuran mulkin al’umma ne bisa tsari kamar yadda shara’ar Musulunci ta shata. Akwai ayyanannun rukunnan jama’a
da aka ɗora wa alhakin zaɓar shugaba. Waɗanda akan
zaɓa ba neman matsayin suke ba. Akan ba su ne bisa cancanta.
Zuwan Turawa ya
haifar da sauye-sauye a wannan ƙasar kamar yadda
ya zo cikin Dimokuraɗiyyar Talaka wanda Rufaida Umar Ibrahim ta
rubuta. An nuna yadda Alhaji Nababa Jatau ya janye hankalin wani matshi da ake
kira Rabi’u ɗan Atine, daga sana’arsa ta halaliya, zuwa ga wadda ba ta
da tabbas. An yi amfani da matasan ne domin cimma wata manufa ɓoyayyiya.
An yi amfani da hanyar raba kayan masarufi domin samun goyon bayan al’umma.
Haka kuma, an yi amfani da malamai da matsibbata domin samun galabar zaɓe (sh. 4).
Waɗannan wasu abubuwa ne
da Turawa suka haifar da su.
Yaudara a lamarin
tafiyar da mulkin al’umma, ita ma sabon zuwa ce. An koye ta ne ta hanyar
karance-karancen mujallu da kallace-kallacen finafinan ƙasashen ƙetare. Shugabanni sukan yaudari al’umma ta hanyar yi musu alƙawuran da ba sa cikawa. Sakamakon haka ne ‘yan bangarsu sukan fito fili su
zage su, kamar yadda aka nuna a shafi na 5 a cikin litttafin, inda Rabi’u ya
zagi ubangidansa na siyasa. Lamarin ya kauce wa tarbiyyar ƙasar Hausa da tsarin Islama. A Muslunci zagin wani ma haramun ne balle
shugaba.
A zamanin siyasa,
masu zawarcin wani muƙami sukan yi wa
tsageru kyautar ƙasaita, domin su
ja hankalinsu wajen nema musu al’umma don samun nasarar cin zaɓe, kamar
yadda aka nuna a cikin labarin (shf. 8-9).
5.0 Sakamakon Bincike
An fahimci zuwan
Turawa ƙasar Hausa ya wanzar da koma bayan al’adun Hausa da ɗabi’unsu da
falsafofinsu. Haka kuma, binciken ya gano cewa, hanyar da aka bi wajen rusa
tsarin al’adun ƙasar Indiya,
irinta aka bi yayin lalata na ƙasar Hausa. Ta shafi tsarin karatu na zamani da kuma wasu abubuwan
da ake kawowa na zamani masu alaƙa da kallace-kallace da karance-karance. Irin
wannan hanya aka yi amfani da ita aka kawar da kyawawan ɗabi’un
Hausawa da al’adunsu da tsarin shugabancinsu, har aka wayi gari wasu tsirarun
jama’a ne kawai suke abin da suka so. Ba sa kula da maslahar mafi rinjayen
al’ummar ƙasa. Burinsu tara abin duniya ta kowane hali.
Bugu da ƙari, an
kawar da tunanin lahira daga zukatan al’umma, sai waɗanda
Allah ya tsare. Akasari an raja’a ne ga rayuwar duniya. Al’umma ta watsar da
abubuwan da ta gada kaka da kakanni. Alfasha ya yawaita a tsakanin al’umma. Kunya
ta yi ƙaranci. A kullum ana ƙara karkata kan salon rayuwar Turawa, wanda a yau
shi ne ya kasance abin burgewa.
5.1
Kammalawa
Wannan takarda ta
bayyana yadda halayen Hausawa suka kasance kafin cuɗanyarsu
da Turawa, da taɓarɓarewar da aka samu a sakamakon haɗuwarsu da
su. Takardar ta yi ƙarin haske
dangane da matsayin ƙagaggun labarai a
adabin Hausa da dalilan samar da su. Ta la’akari da ɓangarorin
labaran da aka nazarta, al’adun Turawa yana ƙara yin tasiri a kan Hausawa. Wannan
ƙalubale ne babba da yake buƙatar tashi tsaye domin yaƙar sa. Zamani ya zo ne
domin ya tsaya – ba zai yiwu a koma baya ko a yi watsi da sauye-sauyen da
zamani ya kawo ba. A bisa haka, mafita ita ce Hausawa su yi amfani da zamani
yadda ya kamata. Su fitar da hanyoyin da za su ci gajiyar zamanin tare da kawar
da duk wasu abubuwa da suke matsayin illa ga al’adunsu kyawawa da addininsu da
mutuncinsu.
Manazarta
Abdullahi, S.
U. (1985). Gaskiya dokin ƙarfe. Mainasara Printing Press.
Adamu, Y. M. (1989). Idan so cuta ne. A. J. Publishers.
Ahmed, A. A. (2017). Rupert Moultrie East 1898–1975: Tarihinsa da
sharhi a kan gudummawarsa. WhalesAdverts Limited.
Ali, M. A. (2021). The adverse effects of British colonialism on the
culture and psychology of the Indians: A postcolonial study. Green
University Review of Social Sciences, 7(1-2), 22–34. https://doi.org/10.3329/gurss.v7i1-2.62679
Aminu, N. (2015). Ɓera baƙin dole: Nason al'adun Turawa ga al'adun Hausawa a lardin
Sakkwato da Gwandu da Argungu 1903-2010 [Unpublished
doctoral dissertation]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Argungu, A.
I., & Argungu, I. A. (2016). Sauye-sauyen
zamani a rayuwar Hausawa. Bakaba Journal of Hausa Studies, 2(2),
90-97.
Ashcroft, B.,
Griffiths, G., & Tiffin, H. (1989). The
empire writes back: Theory and practice in post-colonial literature.
Routledge.
Bunza, A. M. (2013). Hutawa ka alewa man gyaɗa ka tuyar ƙosai (barazanar yanayi da kutsowar lokaci ga al'adunmu). In A.
M. Bunza et al. (Eds.), Taɓarɓarewar al'adun Hausawa (The deterioration of Hausa culture) (pp. 3-30). Ahmadu Bello University Press.
Bunza, A. M. (2025). Gurɓacewar al'adun Hausawa, ɗabi'unsu
da halayensu a ƙarninmu [Conference presentation].
I Care Women and Youth Initiative (ICWYI), Afficent Event Centre.
Bunza, D. B. (2013). Zama da maɗaukin kanwa ke sa farin kai: Nason baƙin al'adu cikin al'adun auren Hausawa. In A. M. Bunza et al.
(Eds.), Taɓarɓarewar al'adun Hausawa (The
deterioration of Hausa culture) (pp. 101-112). Ahmadu
Bello University Press.
Bunza, U. A. (2015). Mishan ɓadda
musulmi: Ɓurɓushin aƙidun mishan a cikin littafin Ruwan Bagaja [Conference presentation]. Taron ƙara wa juna sani, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar
Usmanu Ɗanfodiyo.
Chamo, I. Y. (2004). Tasirin al'adun Turawa a cikin finafinan Hausa.
In Hausa home videos: Technology, economy, and society.
Jami'ar Bayero.
Griffiths,
G., & Tiffin, H. (1989). The
empire writes back. Routledge.
Griffiths,
G., & Tiffin, H. (1998). Post-colonial
studies: The key concepts. Routledge.
Gusau, S. M. (1999). Tarbiyya a idon Bahaushe. Algaita
Journal of Hausa Studies, 1(1). Jami'ar Bayero.
Gusau, S. M. (2011). Adabin Hausa a sauƙaƙe. Century Research and
Publishing Limited.
Ibrahim, M.
S. (1985). Auren Hausawa: Gargajiya da Musulunci.
Shonuga Commercial Press.
Ka'oje, U. I. (2006). Tarbiyya a ƙagaggun labaran Hausa: Nazari kan 'ya'yan hutu na Malama Bilkisu
Funtuwa [Unpublished bachelor's thesis]. Sashen Koyar
da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Kano, A. D.
S. (2005). Ƙarkon dabino. Hukumar a daidaita sahu.
Kumar, N.,
Pankaj, A. K., & Pandey, A. K. (2014).
The construction of the subaltern through education: Historical failure of mass
education in India. In Subalternity, exclusion and social change in
India (pp. 175-204). Cambridge University Press.
Malumfashi,
I. (2009). Adabin Abubakar Imam. Garkuwa
Media Services Ltd.
Malumfashi,
I. A. M., & Ahmad, A. A. (2006). Colonial legacy
and writing competitions in the development of Hausa novels. In The
novel tradition in Northern Nigeria: Proceedings of the 4th conference on
literature in Northern Nigeria. Department of English and French,
Bayero University.
Morel, E. D. (1911). Nigeria: Its people and its problems (2nd
ed.). Smith, Elder & Company.
Shehu, M.,
& Sani, A-U. (2018). Zamantakewar
Hausawa jiya da yau. Yobe Journal of Language, Literature and
Culture (YOJOLLAC), 6, 274-284. https://www.amsoshi.com/2019/02/zamantakewar-hausawa-jiya-da-yau.html
Shukla, Y. (2025). From colony to classroom: British rule and
contemporary educational outcomes in India (Honors Thesis No.
1527). Colby Digital Commons.
Spivak, G. C. (1988). Can the subaltern speak? Macmillan.
Trust, A. (2021). Dambarmar siyasa. Test and Print
Ventures.
Yahaya, I. Y., Zariya, M. S., Gusau,
S. M., & Yar'adua, I. M. (1992). Darussan Hausa: Don manyan makarantun
sakandare (Vols. 1-3). University Press PLC.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.