Ticker

6/recent/ticker-posts

Magayakin Kano, Malam Magaji Galadima Abdullahi

Jagora:

Alhaji Magaji Galadiman mutan Maitsidau,

Kowag gaji bai saba ba,

Uban Shamaki dogo mai salati,

Uban Sarkin Fada kasko,

Uban Musa mai doki,

Uban Jarmai Muzammilu,

Wai ba horo ba duna,

Uban Abdullahi Kurata babban p.a,

Ba horo ba ɗan marayan zaki,

Ya biya ni na gode ma,

Naji daɗi iri-iri".

Magayaƙin Kano, Malam Magaji Galadima Abdullahi

☝️☝️☝️☝️☝️Daga cikin tamburan mai girma Magayaƙin Kano, Malam Magaji Galadima Abdullahi na Makaɗa Shagari ɗan Makaɗa Adhama ɗan Makaɗa Dagajirau ne.

Makaɗa Dagajirau yayi tarayyar kiɗa da waƙa da Galadiman Maitsidau Abdullahi Maikano dake masarautar Kano. A gidansa yake sauka idan aka zo bikin sallah a birni kuma yana binsa da kiɗa da 'yan tauri a wajen hawan sallah.

Bayan gushewarsu ɗansa Makaɗa Adhama ya ci gaba da biyar Galadiman Maitsidau Muhammadu Lawan wato ɗan Galadima Abdullahi Maikano bayan wafatinsu a halin yanzu sai jikan Makaɗa Dagajirau wato Shagari ɗan Makaɗa Adhama ya ɗauki maigirma Magayaƙin Kano Malam Magaji Abdullahi ɗan Galadiman Maitsidau Muhammadu Lawan wato jikan Galadima Abdullahi Maikano a matsayin ubangida domin ɗorewar taren data faru fiye da shekaru 100 da suka gabata.

Tun zamanin Sarkin Kano Muhammadu Abbas ɗan Sarki Abdullahi maje Karofi ɗan Sarki Malam Ibrahim Dabo wanda ya yi sarauta daga shekarar 1903 zuwa 1919 ya ƙafa wata ƙungiyar 'yan sintiri da ake kira 'Yan-bata- kulki dake sintiri a cikin birnin Kano don taimakawa ' yan gadi wajen tsabtace birni daga ɓata-gari. 'Yan -bata-kulki akasari 'yan tauri ne da hatsabibai daga ko'ina a ƙasar Kano, shi Dagajirau ne ke yi masu kiɗa don ƙara tsima su. Irin wannan tarayya tana raya al'adu da adabin Hausa.

Dattaku da adalci da karimci da amana da kyautatawa daga gefen uwayen gida ke saka Makaɗa da Mawaƙa riƙon wannan igiya yayin da haƙuri da ƙana'a da juriya da biyayyar Makaɗa da Mawaƙa zuwa ga iyayen gidansu ke matsayin sinidarin tabbatar da wanzuwar irin wannan zamantakewa.

A masarautar Maradun ta Jihar Zamfara Makaɗa Usman Ɗankwanaga Ɗankadu da 'ya'yansa Makaɗa Abdu Kurna da Alh. Musa Ɗanƙwairo da jikokinsa Daudu Garba da Ciroma Abubakar da kuma kamakunnensa Alh. Muhammadu Ɗanjuma Muhammadu Musa(Ɗanƙwairo na yanzu) sun fake wannan tare da Sarakunan Maradun tun daga Sarkin Ƙaya Ibrahim I har zuwa ga Sarki Abubakar /Bubakar da Sarki Muhammadu Bello Tambari da Sarki Ibrahim Maigandi II har zuwa ga mai martaba Sarkin Ƙaya Alh. Garba Muhammad Tambari MFR na yanzu.

An samu irin haka a masarautar Yauri ta Jihar Kebbi inda tun daga mai martaba Sarkin Yauri Abdullahi Jibrin Abarshi ya zuwa ga mai martaba Sarki Tukur Abdullahi da Sarki Shu'aibu Yakubu Abarshi har zuwa ga mai martaba Sarki Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi na yanzu zuriyar Makaɗa Aliyu Ɗandawo Shuni wato ɗansa Sani Aliyu Ɗandawo da jikansa Makaɗa Alh. Ibrahim Sani Aliyu Ɗandawo dake jagorancin ƙungiyar kiɗa ta wannan gida a halin yanzu yana ci gaba da yauƙaƙa wannan tare da ta wanzu shekaru masu dama da suka wuce.

A taimaka muna da ire-iren wannan tare da muke tunanin idan aka farfaɗo da ita sabgar kiɗa da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙen gargajiya na Hausa da ta shiga wani mawuyacin hali na iya samun sa'ida.

Mun samu tsarabar waƙa da wasu muhimman bayanai ne daga taskar maigirma Magayaƙin Kano, Malam Magaji Galadima Abdullahi. Allah SWT ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

A wannan hoto maigirma Magayaƙin Kano Malam Magaji Galadima Abdullahi ne.

Daga taskar:

Hon. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji) Jihar Zamfara, Nijeriya.
09/08/2026.

Post a Comment

0 Comments