Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Wanda Ya Tuba Don Wahala, Allah Zai Karbi Tubansa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaiku malam Dan Allah ina da tambaya Na aikata zububi mai yawa a rayuwata malam yanda na ji mutane na fadin cewa Idan mutun wahala ta sa shi ya tuba ba a karba tubanshi Dan Allah malam ka taimake ni da addu'oi, Istigifari Dan Allah Kuma inasamu lokaci zan gaya maka baban laifin Dana aikata arayuwata malam nayi nadama malam innacikin damuwa inhar namutu ba a Anshi tubanaba malam ka taimake ni da addu'oi Dan Allah na roƙe ka

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Kofofin rahamar Allah (SWT) suna da fadi sosai, kuma Allah yana karbar tuban bawa a kowane hali muddin yana da rai kuma rana ba ta fito ta yamma ba. Babu shakka saɓon Allah abune dake haifarwa da bawa matsaloli masu yawa. Wahala, jarrabawa, ko damuwa galibi suna zama sanadiyyar da Allah ke so ya dawo da bawa gare Shi kuma Allah mai yalwar falalane matukar mutum yayi nadama yagane kuskurensa ya tuba to lallai Allah mai yawan gafarta zunubaine, Allah maɗaukakin sarki ya ce:

...وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ

Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba ɗaya, ya ku muminai! Tsammaninku, ku sami babban rabo. (Suratul Nur Aya ta 31).

Allah yasake cewa:

قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ

Ka ce: (Allah Ya ce): "Ya bayĩNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rayukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gafarta zunubai gaba ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gafara, Mai jin ƙai." (Suratul zumar:l Aya ta 53).

Malamai sun ambaci sharuddan tuba, waɗanda suka dakko daka Alƙur'ani da hadisai:

1. Barin zunubi da gaggawa.

2. Yin dana-sani akan abunda ka riga ka aikata na laifuka.

3. Ƙudurta niyyar bazaka sake komawa wannan laifi ba.

4. Maida hakkin wanda ka zalunta, Idan zunubin ya shafi kayan wani ko mutuncin wani, a mayar musu ko a nemi yafiya. Kuma a barranta daka azzallumai idan da kaine kake taimaka musu.

Bayan waɗannan kada mutum ya manta dawasu al'amuran nadaban waɗanda sunada mahimmanci kwarai wajen tabbatuwar tuba nagartacce, wato Ya zamto Dan Allah mutum yatuba daka zunubi, ba dan wani abu yabar laifin ba ko dan bashi da ikon aikata laifin, ko kuma ka bar zunubi dan tsoran maganar mutane, ba tuba bane wanda yabar zunubi dan kare mutuncinsa wajan mutane, ko dan bashi da iko, ko dan kare lafiyarsa daka wata cuta da'ake samu daka zunubin, ko yabar cin hanci ko karɓar rashawa dan yana tsoran kada akamashi yasha tozarci, haka wanda yabar zina dan kada yaɗau cutukan datake haifarwa, ko mai shan-giyar da yabar shanta dan illolin datake haifarwa, ko ɓarawon da bashi da ikon yinsata ko Ɗan-fashin da rashin samun dama ce tasa ya tuba, duk wani laifi indai ba dan tsoran ukubar da Allah ya tanadar akai ba ka tuba daka gareshi, to bakayi tuba wanda Allah yakeso ba.

Wajibine ka dunga jin bakin ciki duk lokacin da katuno aikin zunubin daka aikata abaya da kuma illarsa. Ana nufin tuba ingantacce baya yiwuwa tare da kana jin daɗin abunda ka aikata abaya inkatuna, ko ma kadunga burin inama kasake komawa nan gaba.

Bayan duk kabi matakan tuba idan kanada wasu abokai da kuke aikata wannan zunubi wajibine ka canjasu da wasu, domin dayawa mutum kan tuba daka zunubi amma sanadiyyar rashin rabuwa dawanda suke aikata laifin tare sai mutum yakoma yasake fadawa cikin ɓata sama da wanda yake abaya, ko gurine ko majalisa dakake tasirantuwa da ita wajibine ka kaurace mata kacanza dawata wacce zaka samu ingantuwar tubanka da imaninka, kasamu abokai nagari masu addini waɗanda koda basu umarceka da kyakkyawa ba zaka tasirantu da su wajan aikata mai kyau kaima.

Ka rinka yin Sallah akan lokaci, Sallah tana wanke zunubai kamar yadda ruwa ke wanke datti. Ka yaiwata aikata kyawawan ayyuka domin kyawawan ayyuka suna share munana. Allah maɗaukakin sarki acikin SURATUL FURƘAAN bayan jero dangin manyan zunubai wanda muminai nagari basa aikatawa kuma duk wanda ya aikata su za'a rufanya masa azaba sai ya ce:

إِلَّا مَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ عَمَلًا صَالِحًا فَأُولَٰئِكَ يُبَدِّلُ اللَّهُ سَيِّئَاتِهِمْ حَسَنَاتٍ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا

"Sai wanda ya tuba, kuma ya yi ĩmani, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yana musanya miyagun ayyukansu da masu kyau. Allah Ya kasance Mai gafara Mai jin ƙai" (Suratul Furƙan Aya ta 70).

Ka fadi wadannan Addu'o'i da Istigifari Masu Karfi da harshenka da kuma zuciyarka:

اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ لَكَ بِذَنْبِي فَاغْفِرْ لِي، فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ

"Ya Allah kai ne Ubangijina, babu wani abin bauta da gaskiya sai dai kai. Kai ne ka halicceni Ni kuma bawanka ne. Kuma ina nan bisa alwashinka da Alkawarinka (wanda na ɗauka) mutukar ikona. Ina neman tsarinka daga sharrin abinda na aikata, Ina yin furuci gareka da ni'imarka agareni, kuma ina yin furuci da zunubaina. Ka gafarta min domin babu mai yin gafarar zunubai sai dai Kai".

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce "Duk Wanda Ya Fadeta Da Rana Alhali Yana Da Cikakken Yaƙini Da Ita, To Idan Ya Mutu Awannan Ranar Kafin Dare, Zai Shiga Aljannah. Wanda Kuma Ya Fadeta Da Daddare Alhali Yana Da Cikakken Yaƙini Da Ita, Idan Ya Mutu Kafin Wayewar Gari, Zai Shiga Aljannah". Imamul Bukhariy ne ya ruwaitoshi.

أسْتَغْفِرُ اللهَ العَظِيمَ الَّذِي لاَ إلَهَ إلاَّ هُوَ، الحَيُّ القَيُّومُ، وَأتُوبُ إلَيهِ

"Ina neman gafarar Allah, Allah babu abin bautawa da gaskiya sai shi, rayayye, Mai tsayuwa da komai, kuma ina tuba zuwa gare shi".

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: Allah zai yafe wa duk wanda ya karanta wannan addu'ar, ko da zunubinsa ya kai na wanda ya juyo baya a fagen jihadi.

 ﻻ ﺇﻟﻪَ ﺇﻟَّﺎ ﺃﻧﺖَ ﺳﺒﺤﺎﻧَﻚ ﺇﻧِّﻲ ﻛﻨﺖُ ﻣﻦ ﺍﻟﻈﺎﻟﻤﻴﻦَ

"Babu abun bautawa da gaskiya sai Kai, tsarki ya tabbata a gare Ka, lallai ni na kasance cikin azzalumai".

Muna rokon Allah ya shiryar damu zuwa ga abunda yakeso kuma ya yarda dashi, yakarbi tuban mu gaba ɗaya domin shi mai yawan karbar tuba ne mai jinkai.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments