Article Citation: Atiku A. Dunfawa (2019). Nusarwa a Cikin Waƙoƙin Yaran Hausawa: Nazarin Waƙoƙin Tatsunuyar Ƙaure da ta Sandata. DEGEL: The Journal of the Faculty of Arts and Islamic Studies, Vol. 17, No. 2. ISSN 0794-9316
NUSARWA A CIKIN WAƘOƘIN YARAN HAUSAWA: NAZARIN WAƘOƘIN TATSUNIYAR ƁAURE DA TA SANDATA
Na
Atiku A. Dunfawa
Abstract
Children songs in Hausa are composed specifically for the children or by
children themselves. There is no much study on such songs, probably the
attention of Hausa literary scholars was taken away by other categories of oral
songs which their themes go more with adult thinking. The aim of this paper is
to examine two folklore songs of “Tatsuniyar Ɓore” and “Tatsuniyar Sandata” to bring out the stylistic devices used in
teaching children the appreciation of the relationship in natural happenings both
at the scientific and at the social contents. Whereas the first song focuses on
the scientific aspect; the second, explores the social one.
Shimfiɗa
Nazarin a kan waƙoƙin yara ya ƙaranta idan aka kwatanta shi da wanda aka
gudanar a kan waƙoƙin da suka shafi manya. Ƙila haka
ya faru ne saboda hankalin manazarta ya fi komawa ga waƙoƙin manyan waɗanda saƙonninsu suka fi dacewa da tunanin manya. Duk da haka, malamai sun ce
wani abu a kan irin waɗannan waƙoƙin, kamar Abubakar(1981) da Bichi(1984) da
Muhammad (1985) da Yahya(1986 da kuma 1994) da Dunfawa 2002da 2011). Waaɗannan malamai da ɗalibansu sun yi ayyuka a kan nazarin waƙoƙin yara ta fuskoki daban-daban. Daga cikin amfanin waƙa akwai nusarwa, wadda ke nufin lurarwa, wato
lurar da waɗanda ake yi wa waƙa ko masu sauraren ta a kan wani abu musamman da ake son jawo hankalinsu
zuwa gare shi. Kusan kowane ɓangare na adabin Hausa lurar da mutane yake yi a
kan rayuwar yau da kullum da ke tsakanin jama’a. Manufar wannan maƙala shi ne ta dubi wasu waƙoƙi na yara da sukan tuzgo a cikin tatsuniya masu ɗauke da wata nusarwa ga yara ko bayan jigon da tatsuniyar take ɗauke da shi. Kasancewar tatsuniya wata makarantar farko ga yaran Hausawa
ake saka saƙonni iri-iri a cikinta domin yara. A irin wannan
ma, akan yi amfani da waƙa a cikin tatsuniya domin jaddada saƙon da take ɗauke da shi ga yara domin waƙa a irin ɗabi’arta salo ne na ƙara jawo hankali. Irin wannan nusarwar ta cikin
tatsuniya mafi yawa takan zo ne a cikin waƙa, kuma takan kasance a kan yadda dangantakar faruwar wasu abubuwa take
a kimiyance (scientifically), ko a hulɗance, wato hulɗa ta yau da kullum (socially) waɗanda sau da yawa sukan tuzgo a
cikin adabin bakan Bahaushe (zube da adabi da wasan kwakwayo). Maƙalar ta dubi wasu waƙoƙi biyu ne da ke cikin “Tatsuniyar Ɓore” da “Tatsuniyar Sandata” domin fito da hanyoyi da salon da Hausawa
ke amfani da shi wajen nusar da ƙananan yara a cikin waƙoƙin. Maƙalar ta dubi yadda aka yi amfani da wani salo a cikin waƙoƙin domin nusarwa ga yara dangantakar da ke akwai ga faruwar abubuwa a
kimiyance da kuma hulɗance. Waƙa ta farko nusar da yara take yi dangantakar faruwar abubuwa a
kimiyance, ita kuwa waƙa ta biyu tana nusar da su faruwar abubuwa a hulɗance, wato ta hulɗar zamantakewa.
Suwane Ne Yara
Yara jam’in kalmar yaro ne wanda ke nufin ɗan mutum da bai balaga ba
(CNHN, 2006). Wannan shi ya nuna yaro wata halitta ce irin ta mutum wadda ba ta
cika zakkar (mizanin) da ake amfani da ita wajen auna mutum ba. Dubin haka ya
sa Hausawa ke danganta wasu kalamai ga yaro ta la’akari da matsayinsa. Sukan
ce, "Yaro ba mutum ba sai ya girma". Ko kuma, “Yaro masomin mutum”.
Waɗannan kalamai da Bahaushe ya jingina ga yaro su
ke nuna ba halittar jiki irin ta mutum kawai ake dubi a kira mutum da sunan
mutum ba face sai halittar ta ƙunshi
wasu abubuwa da wasu ma ba a iya ganin su bale a taɓa, sannan ake iya kiran sa mutum. Daga cikin irin waɗannan abubuwa akwai hankali(Allen,1982). Shi ko yaro ko yana da hankali,
to ba cikakke ba ne, shi ya sa Bahaushe a cikin hikima ya kore zamansa mutum
face idan ya girma, wato ya sami cikakken hankali.
Ga masu nazarin ilmin mutuntaka (psychology) suna ganin yaro shi ne
wanda shekarunsa na haihuwa suka tashi daga 5-12 ko 13, wato shekarun shiga
Firamare zuwa ƙaramar Sakandare (Farran, 1964). Yara masu irin
waɗannan shekaru su ake yi wa tatsuniya domin nusar
da su dabarun rayuwar da za su fuskanta a nan gaba cikin duniya. Mai irin waɗannan shekaru ya fi saurin riƙe saƙon da aka ƙunsa a cikin zuciyarsa da tunaninsa musamman idan aka saka saƙon a cikin waƙa kasancewar waƙa mai tafiya tare da zuciya (Muhammad,1997).
Sanin haka ne ya sa Hausawa suke shirya darussan dabarun rayuwa da ilmantarwa
cikin ‘yan waƙoƙi su riƙa rera wa ‘ya’yansu a cikin tatsuniyoyi. A cikin
darussan da ake ƙunsawa a waƙoƙin tatsuniya domin wannan manufa akwai ɓurɓushin kimiya dangane da abubuwan da ke cikin
muhallin Bahaushe ko kuma hulɗar zamantakewar cuɗe ni- in cuɗe ka da ke gudana tsakanin mutane.
Waɗanne Waƙoƙi
Ne Na Yara
Waƙoƙin yara su ne waƙoƙin
da aka tsara domin yara ko kuma su yaran suka tsara wa kansu domin amfanin
kansu (Dunfawa, 2002). Irin waɗannan waƙoƙin
kamar yadda bayani ya nuna, yara ne da kansu ke tsara abinsu ko kuma wani
lokaci manya su tsara dominsu. Waƙoƙin yara sun haɗa
da waƙoƙin
cikin tatsuniya da waƙoƙin bukukuwa da waƙoƙin
dandali(waƙoƙin
wasanni) da kuma waƙoƙin tashe. Sai dai wannan maƙala kamar yadda takenta ya nuna tana zance ne a kan
waƙoƙin
yara na cikin tatsuniya.
Mine Ne Jigogin Waƙoƙin
Yara
Jigo na nufin saƙon da waƙa
ko manufa ko bayani wanda waƙa
take ɗauke da shi domin isarwa ga mai saurare (Yahya, 1997).
Jigogin waƙoƙin
yara musamman waɗanda ake samu a cikin tatsuniya suna koyar da
ladabi da biyayya ga na gaba, kamar waƙar
da ke cikin tatsuniyar Ruwan Bagaja, da tsaron amana, kamar waƙar da ke cikin tatsuniyar Maɗaci,
da aikata gaskiya, kamar waƙar
da ke cikin tatsuniyar Baba Dogaji da gargaɗi,
kamar waƙar da ke cikin tatsuniyar Ɗan’auta, da koyar da dabarun zaman duniya da
nusarwa a kan yadda al’amurra ke gudana a cikin rayuwar yau da kullum, kamar waɗannan
waƙoƙi
da maƙalar ke tsokaci kansu, wato na cikin tatsuniyar Ɓore da ta Sandata. Wasu lokuta akan sami waƙoƙin
da ke cikin tatsuniya suna ɗauke da wani saƙo daban daga wanda gundarin tatsuniyar ke magana
kansa musamman ta salon da aka tsara waƙar
aka kuma rera ta da shi. Irin wannan salon ne maƙalar ta duba a cikin tatsuniyar ta Ɓore da ta Sandata.
Nusarwarwa A Cikin Waƙoƙin
Tatsuniya
Ana samun nusarwa iri daban-daban a waƙoƙin
da kan tuzgo a cikin tatsoyoyin Hausawa domin faɗakar
da yara alfanu wasu abubuwa da shekarunsu bai kai su fahimce su ba a lokacin. Ƙila Bahaushe na yin haka ne domin ya saka
yaransa zama cikin shirin ko-ta-kwana a kan waɗannan abubuwa da ya tabbata za
su bijiro ma yaran a nan gaba. An duba irin wannan nusarwa a waɗannan waƙoƙin tatsuniyoyin da aka ambata, wato waƙar cikin tatsuniyar ɓore da tatsuniyar Sandata.
Waƙar Tatsuniyar Ɓore
Tatsuniyar Ɓore tatsuniya ce da aka tsara domin nuna wa yara
cewa zakaran da Allah ya nufa da cara mazuru da shaho ba za su iya hana shi ba.
Tatsuniyar ta nuna wata mata da ke zaune da ‘ya’ya biyu mata ; ɗaya ‘yar cikinta, ɗaya kuma ‘yar kishiyarta da ba ta nan. An shirya
wani buki da za a je domin ɗan sarki ya zaɓi mata amma tana son ta hana
‘yar kishiyar tata damar halartar bukin domin kyakkyawa ce kuma tana tsoron ɗan sarki ya zaɓe ta a matsayin mata. Sai ta ƙulla wani makirci da ke iya hana yarinyar zuwa
bukin, ta ce ba za ta ba ta kayan da za ta yi ado domin zuwa bukin ba sai ta je
jeji ta ɗebo mata ‘ya’yan ɓore, alhalin lokacin rani ne
kwam sadda ɓore ba ya da ‘ya’ya. Tana ganin idan ta je ba za
ta iya samowa ba, to sai ta fake nan ta hana ta kayan adon wanda yin haka zai
hana ta halartar bukin. Allah
Karimi ! Da yarinyar ta je sai ga shi ta zo da ‘ya’yan ɓoren
ta kawo mata. To amma akwai yadda aka yi har
ta sami ‘ya’yan ɓoren. Yarinyar ta je gun Ɓore ne ta roƙe shi ya ba ta ‘ya’yan ta hanyar rera masa wata waƙa. Da ya ji bukatarta sai ya tura ta zuwa wajen
Saniya domin ta samo masa sanadarin da ke iya sa ya samar da ‘ya’ya, wato taki.
Daga Saniya zuwa ga Gamaba da Girgije wanda daga haka ne ta sami biyan bukata
kai tsaye. Kowane ta je wurin sa daga cikin waɗannan sai ta roƙe shi wani abu da ake samu daga gare shi ta
hanyar rera masa waƙa, har daga ƙarshe ta sami biyan bukatarta. Ga yadda take rera waƙar
a duk wajen da ta je. Da ta je ga Ɓore
ga abin da ta ce :
Yarinya : Ɓore, Ɓore gare ka na zaka,
Ɓore: Yarinya in ba ki me?
Yarinya:
A ka ba ni ‘ya’ya,
Ɓore ;
‘Ya’ya a ki kai ma wa ?
Yarinya : A ni kai ma Inna,
Ɓore :
Inna a ta ba ki me ?
Yarinya Inna a ta ba ni kaya,
Ɓore :
Kaya a ki je ina?
Yarinya: A na je ka gasa, tsara duka sun
tafi.
Da yarinyar ta gama rera wa Ɓore waƙar
ya ji bukatarta, sai ya ce, "To yarinya ke ga ba ni da taki da zai iya ba
ni damar samar da ‘ya’ya, sai ki je wajen saniya ki samo mani taki. Sai yarinya
ta wuce zuwa wajen saniya. A nan ɓore alamci ne na sauran kayan da
ake shukawa a sami amfani ko wani abin moriya daga gare su. Wato ta haka
Bahaushe na son ilmantar da ‘ya’yansa cewa kayan gona da sauran tsirai da ɗan
Adam ke amfana da su ba su yin inganci su samar da abin da ake na amfani sai
tare da wani sanadrai da taki ke bayarwa. Ashe ke nan zuba shuka ba tare da samar mata taki ba kamar aikin baban
giwa ne. Kimiyanci, yaro zai fara sanin amfani taki ga aikin gona tun da ƙuruciyarsa, kasancewar noma babbar sana’ar da
Bahaushe na wancan lokaci ke zaton ɗansa ya aiwatar idan ya girma.
Ashe akwai bukatar ya sanar da shi abin da ke kyautata noma da inganta shi tun
da ƙuruciya. Bayan yaro ya sami wannan nusarwa game
da dangantakar taki da ingancin shuka, sai kuma a gaba aka nusar da shi cewa
shi ma takin akwai abin da ke samar da shi wato dabbobi, don haka Ɓore ya tura ta wajen Saniya. Da yarinya ta wuce
zuwa ga saniya sai ta sanar da ita bukatarta ta hanyara rera waƙarta tana cewa:
Yarinya: Saniya, saniya gare ki na zaka,
Saniya: Yarinya in ba ki me?
Yarinya:
A ki ba ni kanjilo1,
Saniya: Kanjilo a ki kai ma wa?
Yarinya: A ni kai ma Ɓore,
Saniya : Ɓore a ya ba ki me ?
Yarinya: A ya ba ni ‘ya’ya,
Saniya: ‘Ya’ya a ki kai ma wa? (Har
zuwa ƙarshe).
Wannan shi ne mataki na biyu na
nusarwar da ke cikin waƙar. Saniya a nan alamci ce na
sauran dabbobi da ake iya samun taki daga tarosonsu. A wancan lokaci da ke da ƙarancin ilmin fasaha, dabbobi ne kawai hanya mafi
inganci ta sama wa shuka taki. Ana ƙoƙarin nusar da yara wannan hanyar ta samun taki a
cikin wannan waƙa. Wato kamar ana cewa dole manomi ya yi kiyo ko ya
yi hulɗa da makiyaya idan yana son ya sami takin saka wa
shukarsa domin samun amfani mai yawa. To amma su ma dabbobni ba haka kawai suke
samar da taki ba, akwai abin da suke bukata kafin su samar da shi. Dabbobi
tamkar inji ne da ke sarrafa wasu abubwa ya samar da taki. Wannan ya sa saniya
ta gaya wa yarinya cewa,"Ke ga babu ciyawa da zan ci in iya samar da taki.
Sai ki je wajen Gamaba ki faɗa mata ta ba ki toho ki ɗebo
ki kawo mani, sai in ci sannan in iya ba ki taki”. Sai yarinyar ta wuce zuwa
wajen Gamba ta rera waƙa tana cewa:
Yarinya : Gamba, Gamba gare ki na zaka,
Gamba: Yarinya in ba ki me?
Yarinya:
A ki ba ni toho,
Gamba: Toho a ki kai ma wa ?
Yarinya: A ni kai ma saniya,
Gamba : Saniya a ta ba ki me ?
Yarinya: A ta ba ni kanjilo,
Gama: Kanjilo a ki kai ma wa?
Yarinya: A ni kai ma Ɓore…(har
zuwa ƙarshe).
A nan gamba ita ce alamci na ciyayi da sauran
abincin da dabbobi ke ci. Wato ke nan nusar da yara ake yi a kan yadda taki ke
iya samuwa daga dabbobi ta hanyar abincin da suke ci. Ƙila yaro a matsayin shekarunsa da hankalinsa ba zai
kula da haka ba, amma tsara masa shi a cikin waƙa na nusar da shi ga fahimtar haka.Daga nan sai
yaro ya san ciyawa da sauran abincin da dabbobi ke ci su ne sanadarin samun
taki daga gare su. Sai dai ita kanta ciyawar tana
bukatar wani abu kafin ta iya toho. Wannan
ya sa Gamba ta umurci yarinya ta cewa "Ke ga babu ruwa bale in iya toho.
Sai ki je ki roƙi girgije ya yi ruwa sai in sami damar yin toho ki ɗiba".
Sai yarinya ta wuce zuwa ga girgije ta rera masa waƙar.
Yarinya: Girgie, girgije gare ka na zaka,
Girgije: Yarinya in ba ki me?
Yarinya:
A ka ba ni ruwa,
Girgije: Ruwa a ki kai ma wa ?
Yarinya : A ni kai ma Gamba,
Girgije : Gamba a ta ba ki me?
Yarinya: A ta ba ni toho,
Girgije : Toho a ki kai ma wa ?
Yarinya : A ni kai ma saniya…(zuwa
ƙarshe).
Girgije alamci ne na ruwa kuma ruwan aka nema daga
gare shi. Ruwa kuwa wani sanadari ne da
kusan kowace rayuwa take da bukata da shi. Ke nan amfani da ake samu daga
shuke-shuke da ita kanta shukar da dabbobin da ke samar da taki ga shuka da
ciyayin da dabbobin ke ci su samar da taki duk sun dogara ne ga ruwa masu ɗauke da wani sanadarin da kusan kowace halitta ke da bukata da shi.
Wannan ya tabbatar da faɗar Allah(SWT) na cewa "mun saka ruwa ya
zama rayuwa ga kowane abu" (21:30). Hanya da dabara da aka yi amfani da
ita ta kawo abubuwa daki-daki da nuna yadda kowane ɗayansu yake da dangantaka wajen samuwar ɗaya wani salo ne na nusar da
yara masu ƙananan shekaru kimiyar halitta. Da babba ake son
a sanar, da ana iya yin haka cikin jumla ɗaya ko biyu, amma a yaro sai
an yi amfani da wata dabara da salo daidai da hankalinsa kafin ya iya kama saƙon da ake cusa masa domin ya fahimta.
Waƙar Sandata
Jigon tatsuniyar Sandata yana ƙoƙarin koya wa yara cewa jari ba ya da kaɗan tare da nusar da su girmama abin da mahaifi ya sama wa ɗansa komin ƙarancinsa domin samun albarkar a cikin abin. Duk
yadda abin da uba ya ba ɗansa yake kaɗan, idan bai rena ba kuma ya
tatatala shi yana iya zama babban abin da zai iya dogara da shi iya rayuwarsa.
Wannan ita ce nusarwar da ke cikin waƙar. Tatsuniyar ta bayar da labarin wani mutum da ya je jeji ya ɗebo sanda ya ba matarsa sanda take ɗauke da ciki, ya ce ta ajiye
wa ɗanta idan ya girma ta ba shi. Bayan haka sai
mutumen ya rasu. Matar tasa ta cika wasiccin da mijinta ya bar mata, ta ba
yaron sandar bayan ya zama ɗan saurayi, ta kuma sanar da shi labarin dajin
da mahaifinsa ya je ya ɗebo masa sandar. Da yaron ya karɓi sandar sai ya shiga duniya neman abin rayuwa. Yana tafiya sai ya haɗu da wani maharbi ya harbi wani tsuntsu amma tsuntsun ya saƙale ga bishiya bai faɗo ba. Maharbin ya nemi yaron ya ara masa sandarsa, sai ya ba shi.
Maharbi ya wurga sandar sai tsuntsun ya faɗo amma sanda ta sagale. Ya ɗauki tsuntsunsa zai wuce sai yaro ya fasa masa kuka yana cewa :
Yaro: Sandata! Sandata,
Da uba yaɗebo uwa ta gyara,
Bakin dajin Katuru,
Katuru ko ba kusa ba,
Balle yaro ya je can,
Ya ɗebo mani sandata.
Da maharbi ya ji jawabin yaro sai ya ce masa "To amshi tsuntsun
maimakon sandarka" . Sai yaro ya karɓa kowa ya wuce. Sanda a nan
ita ce alamcin jari. Aron da ya bayar na sanda shi ne alamcin juya jari.Tsuntsu
da aka ba yaro shi ne alamcin ribar da ake samu idan an jujjuya jari. Wato daga
sanda yaro ya sami tsuntsu. Da ba ya da sanda da ba a karɓi aro ba. Da hulɗar aro ba ta shiga ba da bai sami tsuntsu ba.
Wannan yana nuna wa yara yadda ake samun wani abu saboda hulɗa ta wani abu da wani daban, kamar yadda samun tsuntsu yake da
dangantaka da bayar da sanda kafin a same shi.
Yaro ya ci gaba da tafiya yana riƙe da tsuntsunsa, sai ya haɗu da mata suna sussuka. Daga cikinsu akwai wata mai ciki, sai ta ce ya ba
ta tsuntsun. Sai ya ba ta ya koma gefe ɗaya ya zauna. Mai ciki da kwaɗai,
sai ta gashe tsuntsun ta cinye. Bayan sun ƙare sussuka sun ƙone ƙaiƙayinsu za su wuce, sai yaro ya ce:
Yaro: Tsuntuna! Tsuntsuna da majefi ya ba ni,
Majefi ɓar da sandata.
Sandata da uba ya ɗebo
uwa ta gyara,
Bakin dajin Katuru,
Katuru ko ba kusa ba,
Balle yaro ya je can,
Ya ɗebo mani sandata.
Da jin haka
sai matar ta ɗebi tokar ƙaiƙayinta da ta ƙona
ta ba yaron a madadin tsuntunsa. Sanda daga tsuntsu ta koma toka. Yaro ya karɓa
ya wuce gaba. Yana tafiya sai ya kai wani gida ya tarar matar gidan tana tuwo
amma ba ta da tokar da za ta yi amfani da ita ta saka a tuwon, sai ta ce ya ba
ta tokarsa. Yaro ya ba ta. Bayan an ƙare tuwo sai yaro ya ce:
Yaro: Tokata! Tokata da masheƙi ta ba ni,
Masheƙi bar da tsuntsuna.
Tsuntsuna
da majefi ya ba ni,
Majefi ɓar da sandata.
Sandata da uaba ya ɗebu
uwa ta gyra,
Bakin dajin Katuru.
Katuru ko ba kusa ba,
Balle yaro ya je can,
Ya ɗebo mani sandata.
Da mai tuwao ta ji abin da yaro yake cewa sai ta ɗebo marar tuwo ta ba shi a maimakon sandarsa. Yaro ya karɓa ya wuce. Ya taɓa tafiya sai ya taras da maƙera suna ƙira yunwa ta kama su ba abinci, sai suka ce ya ba su tuwonsa, sai ya ba
su ya koma gefe ɗaya ya zauna. Bayan sun gama ƙira za su wuce sai yaro ya ce:
Yaro : Tuwona! Tuwona da matuƙi ta ba ni,
Matuƙi bar da tokata.
Tokata
da masheƙi ta ba ni,
Masheƙi bar da tsuntuna.
Tsuntsuna
da majefi ya ba ni,
Majefi bar da sandata.
Sandata da uba ya ɗebo uwa ta gyara,
Bakin dajin Katuru,
Katuru ko bak usa ba,
Balle yaro ya zo can,
Ya ɗebo mani sandata.
Da maƙera suka ji haka, sai suka ba shi garma a
madadin tuwonsa. Yaro ya karɓa ya wuce. Ya taɓa tafiya sai ya haɗu da manoma garmarsu ta kare. Suka ce ya ba su garmarsa, sai ya ba su. Suka yi hoɗa abin gona ya yi kyawo. Aka ɗebe amfanin gona sai yaro ya ce garmarsa. Aka kwashi rikici har gidan
Sarki. Sarki ya hukunta a raba amfanin biyu a ba yaro rabi domin in babu
garmarsa da ba a yi noman ba. Yaro
ya amshi amfaninsa ya adana ya zama mai hali a cikin mutanen gari.
Duk wannan abu ana iya faɗin sa a cikin jumala ɗaya ko biyu idan manyan mutune ake son a koyar. Da yake yara ne ake son
koyarwa ta la’akari da hankalinsu, to ana bukatar yin amfani da wani salo domin
su iya fahimtar abin da ake son koya masu. Muhimmin salo guda ne aka yi amfani
da shi domin cim ma burin isar da waɗannan saƙonni zuwa ga yara. Salon shi ne salon jaddadawa.
Idan aka lura da yadda ake yawan jaddada kowani abu ɗaya da ake son bayyanawa a cikin waƙar sai an nanata shi. Kowane abu ɗaya aka ambata sai an nanata
shi an nuna dangantakarsa zuwa ga sauran da aka fara ambata domin tabbatar saƙon dangantakar da ke tsakanin abubuwan da ake
son yara su fahimta ya shiga zuciyarsu. Misali, a waƙa ta farko, kowane abu aka je gare shi aka faɗa masa bukata sai ya tambayi yarin abin da za ta yi da abin da take roƙa. Idan ta amsa, sai a sake tambayar shi wancan
abin me zai ba ta. Haka za ta riƙa maimaita zance tana fito da dangantakar kowane abu da ɗan uwansa ta hanyar jaddadawa da maimaitawa ta yadda hankalin yaro zai
iya kama saƙon. Da wuya yaro ƙarami ya san amfanin taki ga shuka ko amfanin ciyawa ga samun taki, ko
kuma ruwa ga ciyawa idan ba don salon jaddadawa da aka yi amfani da shi a waƙar ba.
Haka ma a waƙar tatsuniya ta biyu, yana da wahala yaro ƙarami ya iya sanin yadda ƙaramin jari ke iya zamma babba idan ba an nuna
masa yiyuwar haka bata salon da aka tsara waƙar da yadda aka rera ta ba. Salon jaddadawa ne da aka yi amfani da shi
ya sauƙaƙa masu fahimtar haka. Kowane abu an nuna yadda ya juya ya koma wani abin
amfani daban saɓanin na farko ta hanyar bayar da shi a karɓi wani, kamar dai yadda zuba jari ke kasancewa.
Naɗewa
Hankalin yaro ƙaramin hankali ne wanda ke bukatar taka-tsantsan
da hattara tare da amfani da dabaru da salailai masu kaifi domin cusa masa
fahimtar abu sosai. Maƙalar ta nuna salon jaddadawa a matsayin wani
salo da ya dace a yi amfani da shi wajen koyar da yara kowane irin darasi domin
su sami sauƙin fahimtar sa. Salon jaddadawa a cikin waɗannan waƙoƙi ya taimaka gaya wajen nusar da yaran Hausawa danagantakar abubuwa a
kimiyance da kuma hulɗance ta hanya jaddada ambaton dangantakar
abubuwan da junansu a cikin waƙoƙin da aka yi nazari.
Haka ma, maƙalar ta fito da abubuwan da yaran Hausawa ke
koyo a makarantar gargajiya ta farko(tatsuniya) kafin wucewarsu wasu makarantu
na gaba. Daga cikin abubuwan da suke koyo a wannan makaranta ya haɗa har da kimiya da fasaha da ake ganin kamar sai a yanzu Bahaushe ya san
da su, ko kuma sai a makarantun zamani ake fara koyon su.
Wani abu kuma shi ne, dabarar koyarwar da Bahaushe ke amfani da ita a
wannan makaranta ta farko ta yi daidai da wadda ake amfani da ita a makarantun
zamani ga ƙananan yara. Wato saka darussa a cikin waƙa da kuma yawan jaddada abinda ake son koya wa
yaro ta hanyar yawan kai da komo ga maimaita ambaton sa.
Har ila yau, muƙalar ta yi tsokaci a kana yadda ya kamata
koyarwa ta kasance a ƙaramin mataki, wato ta dace da yadda hankalin
wanda ke wannan matakin ke iya kama abin da ake ƙoƙarin koya masa cikin sauƙi. Wannan shi ya fito da irin juriya da haƙurin da mai koya wa yara ya kamata ya sifantu da
su a lokacin koyawarsa, wato rashin ƙosawa wajen maimaita abin da darasi ya ƙunsa ga yara domin ya zauna cikin ƙwaƙwalwarsu su fahimce shi sosai. Dubi yadda aka
jure wa maimaita kowane abu a cikn waƙoƙin da aka yi nazari. A kowane ɗa sai an maimaita tun daga abin da aka fara ambata har zuwa wanda ake
kansa. Duka wannan domin taimaka wa yaro ya haɗa abin da aka fara ambata da
wanda ake kansa domin iya kwatanta su da dangantakar da ke tsakaninsu.
Manazarta
Abubakar, Y. (1981) “Nazri A
Kan Waƙoƙin Yara A Birnin Gwari”, kundin B. A., Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
da Na Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Allen, R.T. (1982) The
Essential Task of Education, NNPC, Zaria.
Bichi, A.Y. (1984) “Wedding
Songs As Regulators of Social Control Among Hausa of Nigeria”, kundin Ph.D.,
Jami’ar Pennsylvania, USA.
BUK (2006), Ƙamusun Hausa, Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Dunfawa, A.A. (2002) “Waƙa A Tunanin Yara”, Kundin Ph.D., Sashen Koyar Da
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Dunfawa, A.A. (2011) “ Waƙoƙin Yara A Matsayin Tubalan Gina Tunani”, a cikin Algaita,
mujallar
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.
Farran, J.F. (1964), Principles
And Practice of Education, Longman, London.
Gusau, S.M. (2008) Dabarun
Nazarin Adabin Hausa, Benchmark Publishers, Kano.
Koko, H. S. (2009), Jigon
NazarinTatsuniya, Sokoto (No oublisher).
Muhammad, B. (1985) “Nazarin
Waƙoƙin Yara Na Gargajiya Da Muhimmancinsa Ga rayuwar Hausawa”, Kundin NCE,
Kwalejin Ilmi ta Jahar Kano.
Muhammad (1997), a cikin
gabatarwar Salo Asirin Waƙa na A.B. Yahya, FISBAS Media
Services, Kaduna.
Yahaya, I. Y. (1979) “Oral Art
and Socialisation Process: A Socio-Folkloric of Initiation From Childhood To
Adult Hausa Community Life” Kundin Ph.D., Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Yahya, A. B. (1997) Jigon Nazarin Waƙa, FISBAS Media Services, Kaduna.
Yahya, A. B. (2001)
“Dangantakar Waƙa Da Tarbiyyar ‘Ya’yan Hausawa”, a cikin
mujallar Harsunan Nijeriya XIX, CNHN, Jami’ar Bayero, Kano.
Yahya, A. B. (2004) “Tattalin
Zaɓen Rubutattun Waƙoƙin Hausa Domin Yara”, a cikin mujallar FAIS
Journal of Humanities, Jami’ar Bayero Kano.
Yahya, A. B. (2001) Salo Asirin Waƙa, FISBAS Media Services, Kaduna.
The official website of the DEGEL Jounal is https://www.degeljournal.com

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.