Article Citation: Salisu Garba (2019). Hotoncin Zuci a Waƙar Sabo Wakilin Tauri ta Hamisu Sarkin Kiɗi. DEGEL: The Journal of the Faculty of Arts and Islamic Studies, Vol. 17, No. 2. ISSN 0794-9316
HOTONCIN ZUCI A WAƘAR SABO WAKILIN TAURI TA HAMISU SARKIN KIƊI
Na
Salisu Garba
Tsakure
Salo dai kamar yadda masana suka bayyana shi ne,
dabaru da hikimomin jawo hankali domin isar da saƙo cikin sauƙi da burgewa ga mai saurare. Wannan
ya sa fasihai kan yi ƙoƙarin darzo salon da zai taimaka masu wajen kama hankalin masu saurarensu
domin samun damar cim ma muradinsu. A ƙoƙarin fasihai na cim ma wannan muradi
nasu sukan sarrafa dubaru daban-daban, yayin da wasu ke ƙoƙarin dabbantar da mutane, wasu kuma
su mutuntar da dabbobi, wasu kuwa su abuntar da su, wasu ma har salon jirwaye
ko habaici suke sarrafawa. Wannan maƙala ta mayar da hankali ne wajen
nazartar fitaccen salon nan na hotoncin-zuci
wandaHamisu Sarkin Kiɗi Kano ya sarrafa a waƙar Sabo Wakilin Tauri. Watau dabarar suranta wani ɓoyayyen abu a cikin zukatan masu saurare ta yadda za
su iya hararo shi da idanun zuciyoyinsu. Ita wannan maƙala ta mayar da hankali ne wajen
nazartar yadda Hamisu Sarkin kiɗi ya dunƙule manufofi masu tarin yawa a cikin
kalmar arne tare da ƙoƙarin suranta waɗannan ma’anoni a zukatan masu saurare domin bayyanar
da jarunta da bajintar gwaninsa, a zukatanmasu saurare. Daga ƙarshe maƙalar ta gano yadda Hamisu Sarkin Kiɗi ya yi ta ƙoƙarin suranta jaruntar Sabo Wakilin
Tauri, waɗanda ya dunƙule su a cikin Kalmar arne da kuma yadda ya suranta kowace
ma’ana faifai-faifai, ta hanyar ƙirƙirar wata gwagwarmaya tare da
danganta ta da Sabo Wakilin Tauri. Wani abin burgewan da maƙalar ta gano shi ne, kaɗaituwar Hamisu Sarkin kiɗi da irin wannan salo, iyaka sanin wannan maƙala, tamkar dai yadda Aƙilu Aliyu ya kaɗaita da wannan salo a marubuta waƙoƙi.
Shimfiɗa
Sanannen abu ne cewa salo shi ne asirin waƙa kuma dokin jigo, don haka idan
salo ya kasance mai gwaɓi da karsashi, sai manufa da saƙon waƙa su zama masu gwaɓi da armashi. Idan kuma suka zama raunana kuma lami, sai
komai na waƙar ya gaza biyan buƙata (Yahya 2001 da Ɗangambo 2007;38). Sannan kuma iya zaɓin salo babbar alama ce ta shaidar basira da ƙwarewar fasihi a fagen adabi,
musamman waƙa.
Hamisu Sarkin kiɗi kuwa sananne ne kuma fitacce ƙwarai a fagen waƙa, kada ma dai a ce waƙar maza masu farauta. Haka kuma ya rera
fitattun waƙoƙi tun daga na mazaje har na sarauta, musamman dai waƙarsa ta Sabo Wakilin Tauri wadda ake ganin ta fi shahara a cikin waƙoƙinsa na maza, wataƙila shaharar gwarzon da aka waƙe ne da kuma yadda aka kwarzanta shi a
cikinta, ya jawo mata kwarjini tare da mawaƙinta.
Shi kuwa Sabo Wakilin Tauri wani
fitaccen jarumi ne kuma jagora a fagen farauta da kuma harkar tauri a Kano.
Sabo Wakilin tauri ya rasu a Kano a shekara ta 1983. Wataƙila, shahararsa ce ta sa ake yi masa laƙabi da Wakilin Tauri. Watau idan ka gan shi, ka ga tauri, ba tare da wata tantama ko shakka
ba.
Ita kuwa kalmar arne,
ɗaya cedagakalmomin harshen Hausa waɗanda suka sami faɗaɗar ma’ana gwargwadon yadda zamani ke
juyawa. A gargaliyance Hausawa sukan sarrafa kalmar arne da ma’anar abokin gaba
ko hamayya ko Jarumi, amma bayan bayyanar Musulunci kuwa, sai Bahaushe ya
faɗaɗa ma’anarta zuwa abokin gaban
Allah. Watau Hausawan da suka ƙi karɓar Musulunci, daga baya ta sake faɗaɗa ta haɗe da duk wanda ya ƙi Musulunci, a kowace ƙabila ya kasance.
Wannan maƙala ta mayar da hankali ne wajen
nazartar ƙoƙarin Hamisu Sarkin kiɗi ta fuskar
iya ƙirƙirar salo da ƙoƙarin suranta shi a cikin tunanin jama’a domin bayyanar da gwarzantakar
gwaninsa Sabo Wakilin Tauri. Haka kuma maƙalar ta ƙoƙarta fito da hikimar Sarkin kiɗi wajen iya tsara salon hotoncin zuci faifai-faifai
dangane da manufofi daban-daban da suke bayyanar da jaruntar jarumi.
Jarunta
Gusau (2008:387) ya bayyana cewa, kalma ce mai nufin juriya da ƙarfin hali ko bajinta a lokacin aiwatar da wani abu.
Masanin ya ƙara da cewa, mai jaruntaka shi ne gwarzon namijin da ba ya faɗuwar gaba ballantana tsoro, sai dai shi a ji tsoronsa.
Sannan kuma shi ne wanda duk inda ya sa gaba ba ya waiwaye ko kaucewa,
ballantana juyowa, ai sai ya dire.
Shi kuwa Awde (1996:73) da Dikko da Macciɗo (1991:52) Kalmar jaruntaka ita ake cewa, jar zuciya, watau zuciyar da ake tsoro
amma ita ba ta tsoron komai. Don haka idan aka ce ‘wane mai jan hali ne’ , to,
ana nufin ‘ wanda ba ya tsoron haɗari kuma shi haɗari ne ga wasu’. Mutumin da ya
siffantu da waɗannan halaye shi ake kira jarumi
Arne
A maguzance Hausawa sukan sarrafa kalmar arne da ma’anar abokin gaba ko Jarumi ko abokin hamayya, amma bayan bayyanar
Musulunci kuwa, sai Bahaushe ya faɗaɗa ma’anarta zuwa abokin gaban Allah. Watau Hausawan da
suka ƙi karɓar Musulunci, sun zaɓI su yi gaba da Ubangiji ke nen, domin sun doge a kan
abubuwan da yake ƙi. a fahimtar Hausawa, babu mai dogewa a kan wani abin da wani ba ya so,
sai abokin gabansa, wanda kuma ba ya ƙaunarsa. Yayin da Bargery (1993) da
Awde (1996) suka kalli ma’anar kalmar arne bayan bayyanar Musulunci, a matsayin
wanda ba ya bautar Ubangiji Allah (Bamaguje). Shi kuwa Abraham (1968), ƙarawa ya yi da cewa tana ɗaukar ma’anar gwani,
watau ƙwararre a kan wani abu, musamman Katsinanci. Amma su kuwa fasihai a
harshen Hausa, musamman mawaƙa, suna sarrafa dukkan ma’anonin wannan kalma a waƙe, gwargwadon fasaharsu wajen
zayyanawa da siffanta wanda suke zugawa ko yabawa. Misali inda Ɗanƙwairo ya ambace ta da ma’anar abokin
hamayya a waƙar Sarkin Das ‘ arna kun ji
tamburan sarkin Das mai kayan zamani’
da kuma inda ya sarrafa taa waƙarsa ta Sarkin Muri, Umarun Abba: “
da ka zaka lokacin a buga ne, da arna ba su sha da daɗi ba’.
A waɗannan
muhallai, Ɗanƙwairo ya sarrafa wannan kalma ta arne da ma’anar abokin hamayya ne ga waɗannan
Sarakuna, ba wasu marasa sallah ba.
Sai kuma wurin da Ɗanƙwairo ya sarrafa ta da ma’anar
abokin gaban Ubangiji, inda yake cewa: Daga
Mayanci sai in wuce Zuru,in gano wadda arna ka bankaura sun sha giyad dawa’.
A wannan muhalli, arna masu shan giyar dawa, na nufin maguzawan Zamfarwa waɗanda suke
shan giya kuma su yi ta faman tamɓele.
Watau abokan gaban Ubangiji ne, domin sun ƙi
umurninsa, sun doge a bias gargajiyarsu. Sannnan kuma saiinda Ɗan’anace ya sarrafa ta da ma’anar
jarumi a waƙar Shago- ‘ arne kututturu na Bakura’.
Watau jarumi
kututturu na Bakura. Don haka, wannan ya tabbatar da cewa, Kalmar arne na ɗaukar dukkan
waɗannan ma’anoni, gwargwadon fasahar wanda ya sarrafa ta.
Hotoncin Zuci
Masana irin su Abrams da Harpham
(2009:151) da Baldict (2005:) sun bayyana cewa, wannan salo ne wanda fasihai,
musamman mawaƙa, suke iya sifantawa tare da zayyana wani abu ko wasu siffofi a tunanin
masu saurarensu domin fito da wata manufa ƙarara ta hanyar amfani da wasu kalmomi
na musamman. Masanan, sun ƙara da cewa, ana sarrafa wannan salo ta
fuska uku: ƙoƙarin suranta wani abu ko wata siffa waɗanda ɗa’adam zai iya hararo su a tunaninsa da idanunsa na zuci. Haka kuma sun ƙara da cewa, wannan kaso bai taƙaita ga siffofin da za a iya hararo
ganinsu ba kawai, ya haɗa har da waɗanda za a iya hararo taɓawa ko jin su a jika (zafi ko sanyi) ko shaƙarsu ko ɗanɗanonsu ko kuma ake iya jin motsinsu. Na biyu kuma shi ne wanda akan ware wasu abubuwan
zahiri na musamman, a keɓe su da ambato. Sai kuma inda ake kallonsa a matsayin
wata siga ce ta kwalliya da tamka. Idan aka lura da kyau, za a gane cewa ko dai
a sarrafa harshen a sake ne ko kuma a sigar ado. Don haka nau’i na biyu, ya
kamata ya narke a cikin na farko ne ko na uku, gwargwadon sigar da aka sarrafa.
Bugu da ƙari kuma, sun bayyana cewa, salo ne mai haifar da karsashi ga waƙa, ya kuma tsima masu saurarenta.
Abrams da Harpham (2009:151-152), sun ƙara da cewa, wannan dabara ba ta taƙaita a kan sifanta abin da za a iya
gani kawai ba, ta haɗa har da ƙoƙarin da fasihai kan yi na suranta
halaye da siffofin da za a iya taɓawa ko jin su a jiki ko waɗanda ake iya shaƙarsu ko jin ɗanɗanonsu ko ake iya jin motsinsu.
Shi ma Baldick (2004:121) tamkar sauran
da aka ambata sai dai ya ƙara da cewa, salo ne wanda ya haɗa da dukkan wata dabara da aka sarrafa wajen bayyyana
wani ɓoyayyen abu, ta yadda zai iya fitowa a
zahiri ko dai ta hanyar ƙirƙirar wani yanayi ko kuma a surance
faifai- faifai, yadda zai yi sauƙin hararowa ga masu saurare ko karatu.
Shi kuwa Muhammad (1978) ya yi tsokaci
ne game da wannan salo tare da tsokaci daga waƙoƙin Aliyu Namangi da Audu Makaho Birnin
Kabi, waɗanda kuma dukkansu makafi ne. A cikin
wannan maƙala tasa, ya bayyana cewa Aliyu Namangi ya sarrafa nau’i biyu ne, sigar
bayani da sigar adon harshe. Daga nan sai masanin ya ambaci ƙoƙarin Aliyu Namangi wajen iya suranta
siffofi da ɗabi’un Manzon Allah, da yadda ya
suranta halittar Mala’ikan mutuwa da ‘yan matan Aljanna, ta yadda za a iya
hararo halaye da siffofinsu ƙarara da idanun zuciya. Muhammad () ya ƙara da cewa, dukkan misalan da Aliyu
Namangi ya sarrafa, misalai ne na sakakken harshe. Sai kuma ya bayyana yadda
Aliyu Namangi ya iya suranta kan sa a matsayin mai gani, da yadda ya siffanta
ilimi da haske, jahilci kuma da duhu, sannan kuma ya faɗaɗa ma’anar haske da Manzon Allah (SAW), duhu kuma
arnanci dukkansu misalai ne na sigar adon harshe.
Muhammad (1978:17), ya ƙara jaddada cewa, za a iya kallon
hotoncin zuci ta fuska biyu manya: na farko shi ne, na adon harshe, watau yadda fasihai kan yi ƙoƙarin kwatanta wani abu ta hanyar
sarrafa sigogin adon harshe a ƙoƙarinsa na zayyana wannan abin a tunanin
masu saurarensa. Na biyu kuma shi ne, na
bayani, watau yadda fasihai kan kyautata bayani a kan wani abu ta yadda
masu saurare za su iya hararo shi a cikin tunaninsu.
Sabo Wakilin
Tauri a Bakin Hamisu Sarkin Kiɗi
Hamisu sarkin kiɗi ya sarrafa dabaru masu dama wajen ƙoƙarin suranta jaruntar Sabo Wakilin
tauri a tunanin masu saurarensa. Hamisu ya yi ƙoƙarin tsara bayanansa faifai-faifai
tare da la’akari da siffofin da ke tattare da ma’anar jarunta. Wannan sashe zai
bayyana kaɗan daga cikinsu kamar haka:
Jan Hali
A wannan muhalli, Hamisu ya yi ƙoƙarin suranta Sabo a matsayin mai jar
zuciya ne wadda kowa ke tsoron gamuwa da ita, ita kuma ba ta tsoron gamuwa da
kowa. Ga abin da yake cewa:
a)
“saboda kai aka ɗinka bami,
Da baduhu layar zana”.
b)
“
Marga-margan dutse, Sabo,
Ɗanwaire na ƙarshen
zamani”.
Abin lura a nan, shi ne yadda Hamisu ya nuna dukkan
wani nau’in kariya na jiki ko na kai, ana yin sa ne domin tsoron gamuwa da
Sabo. Don haka, kowa tsoronsa yake ji, amma shi ba ya tsoron kowa saboda jar
zuciyarsa. Idan aka duba (b) kuma za a tarar Hamisu ya yi amfani da adon harshe
ne ya kwatanta Sabo da Ɗanwaire. Watau yadda a wancan lokaci Ɗanwaire ya zama abin gudu, da yadda
garuruwa ke watsewa idan suka ji labarin Ɗanwaire ya nufo su, tamkar dai yadda
yau garuruwa ke watsewa idan suka ji ‘yan boko haram sun darkako, haka Sabo
yake a wajen mafarauta. Wannan za ta sanya mai saurare hararo tunkarowar Sabo
da idanun zuciyarsa, da kuma watsewar garuruwan da yake tunkara.
Bugu da ƙari, ya yi ƙoƙarin suranta Sabo ta yadda masu
saurare za su iya hararowa da idon zuciyarsu tamkar ga mafarauta nan da sauran
mazaje suna faman ɗinka layu da sauran kariyar jiki
gudun haɗuwarsu da Sabo. Haka kuma ya
siffanta shi da marga-margan dutse wanda masu saurare za su iya hararo
gangarowarsa da watsewar jama’a don gudun illarsa a kan su.
Ƙarfin Hali
Bahaushe kan ce, ƙarfin hali ɓarawo da sallama,
yayin da yake ƙoƙarin siffanta jaruntar ɓarawo wajen
bayyanar da kutsawarsa zuwa ga haɗari.
A wannan muhallin kuma Hamisu ya yi ƙoƙarin bayyana Sabo ne a matsayin
wanda ba ya gudun abin tsoro kuma har ma cusa kan sa gare shi yake yi.
a) “ A ran da an yi farautar kura,
An fashe an bar shi,
Arnen, ya kwan a cikin darbajiya”
b)
“ko
da ya gan ta, ta gan shi kura,
Arnen sai ya yiwo fito, ta zo”
c) “ sai ya tad da masu farauta arna,
An fashe an bar shi”
A wannan faifan kuma, Hamisu ya yi ƙoƙarin suranta irin tsananin ƙarfin halin Sabo Wakilin Tauri ne,
ta yadda ganin kura bai sanya shi gudu ko kuma kyarma da ruɗewa ba. Maimakon haka, sai jarumin ya kira ta kuma ta zo.
Haka kuma, ƙarfin halinsa ya ƙara bayyana, tamkar yadda ya fito a ɗiyoyin (b) yayin da aka yi kiciɓis da arna (abokan gaba) a daji, sai kowa ya watse ya bar
Sabo a cikinsu, ba tare da tsoro ba. Don haka mai saurare zai iya hangen Sabo
da idon zuciyarsa, shi kaɗai, a tsaye a tsakiyar abokan gaba, a matsayinsa na mai ƙarfin hali. Haka kuma, yadda kowa ke
tsoron cusa kan sa a cikin duhun darbajiya ko da kuwa da rana ne, amma shi, da
dare ma ya shiga ya kwana, ba tare da tsoro ba. Wannan zai sa mai saurare ya
iya hangen Sabo da idonsa na zuci a cikin duhun runkin darbajiya.
Bajinta
A wannan muhallin kuma Hamisu ya yi ƙoƙarin suranta Sabo ne a matsayin gwarzon
namiji mai cusa kan sa ga haɗari ba tare da nuna damuwa ba, saboda bajinta.
a)
“sai aka danna
uwar kora,
Naman ya faɗi, sai ya
danne naman,
Sai sararsa su ke, arnen ba ya taɓo”.
Bayan duk an watse an bar Sabo a
tsakiyar arna, sai kuma aka danna uwar kora, sai Sabo ya danne naman, su kuma
sai suka hau shi da sara amma saboda jaruntarsa ba su iya komai da shi ba.
Kammalawa
A taƙaice maƙalar ta ƙoƙarta ne game da yadda Hamisu a cikin
hikima da fasaha ya ƙirƙiri hoton zuci wanda zai taimaka wajen hararo ma’anar
kalmar jarumi a cikin faifai guda uku. Watau faifai na jan hali da ƙarfin halin rashin tsoho da gwarzantaka da kuma nuna
bajinta. Sannan kuma da ƙoƙarin Hamisu wajen darzo kalmar arne, ya kuma sarrafa ta
da ma’anar jarumi da kuma abokin gaba. Haka kuma maƙalar ta yi ƙoƙarin fito da nau’in hotoncin zuci guda biyu. Watau yadda
ya sarrafa sakakken salo yayin da ya yi ƙoƙarin suranta gwarzontakarsa da ƙarfin halin Sabo. Sai kuma inda ya sarrafa hotoncin zuci
na adon harshe yayin da ya bayyana Sabo a matsayin Ɗanwaire da marga-margan dutse (abin tsoro). A ƙarshe, maƙalar ta fahimci
cikakkiyar hikimar Hamisu wajen iya suranta jaruntaka a cikin tunanin masu
saurarensa cikin nishaɗi da burgewa da kuma yadda ya dunƙule dukkan ma’anonin jarumi a cikin Kalmar arne, wanda
kuma salo ne farad.
Manazarta
Abraham,
R.C.(1968). Dictionary of the Hausa
Language, London University Press.
Abrams,M.H.and
Harpham, G.G. (2009). A Glossory of
Literary Terms, Ninth Edition, United State of America, Wardsworth Cengage
Learning, Nelson Education Ltd.
Baldick,
C. (2004). Oxford Concise Dictionary of
Literary Terms, Oxford University Press, New York.
Bargery,
G.P. (1993). A Hausa- English Dictionary
and English Hausa Vocabulary (2nd ed), Zaria, Ahmadu Bello
University Press Ltd.
Dikko, I.
& Macciɗo, U. (1991). Ƙamus Na
Adon Magana, Zaria, NNPC, Ltd.
Garba, S.
(2011). Salon Sarrafa Harshe A Waƙoƙin Aƙilu Aliyu, an unpublished PhD Thesis,
Department of African Languages and Cultures, Ahmadu Bello University, Zaria.
Garba,S. (2012).Salo Dokin Jigo.
NazarinWaƙar Ƙalubale Ta Aƙilu Aliyu,(pp265-275) in Champion of Hausa
Cikin Hausa.A Festschrift in Honour of Ɗalhatu Muhammad, Zaria, Department of African Labguages and Cultures, Ahmadu
Bello University, Zaria- Nigeria.
Garba,S. (2013a). Ƙayen Harshe: NazarinWaƙar Saƙo A Hannun Mumini. A paper presented
in the First Hausa National Conference on Language, Litrature and Culture,
Kano, Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano-
Nigeria.
Gusau,
S.M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka, Kano, Benchmark Ltd.
Gusau, S.M. (2008a). Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa, yanaye-yanayensu da Sigoginsu,Kano, Benchmark publishers limited,
Kano- Nigeria.
Gusau, S.M. (2008). Waƙoƙin Baka A Ƙasar
Hausa, Kano,Benchmark Publishers, Ltd.
Gusau, S.M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka, Kano, Century Research and
Publishing,Ltd.
Leech,
G.P. (1968). A Linguistic Guide,to the
Study of Poetry, London.
Muhammad,
D. (1973). Sharhin Hausa Mai Ban Haushi, Harsunan
Nijeriya, III, 47-67.
Muhammad, D. (1977). The Individual Talent in the Hausa Poetic Tradition. A Study of Aƙilu Aliyu and his Arts, London,
an unpublished PhD Thesis, SOAS, London.
Muhammad,
D. (1978a).Waƙa
Bahaushiya: A cikin Ibrahim, Y.Y.da Rufa’i, A. (edit),Studies of Hausa Language, Literature and Culture, the first Hausa
International Conference, Kano, Centre for the Study of Nigerian Languages,
Bayero University, Kano.
Muhammad,
D. (edit). (1978b). Fasaha Aƙiliya, Zaria, Northern Nigerian
Publishing Company, Zaria. Ltd.
Muhammad,
D. (1978d). Visual Imagery, A Paper
presented in the Department of Nigerian and African Languages, Zaria, Ahmadu
Bello University.
Muhammad,
D. (edit). (1990). Hausa Meta Language,
Ibadan, University Press Ltd.
Muhammad,
D. (1978c).The two facets of Rhyme in Hausa poetry: Syllabic and Tonal, Harshe, vol.1.(6-18). Department of
Nigerian and African Languages, Ahmadu Bello University, Zaria.
The official website of the DEGEL Jounal is https://www.degeljournal.com

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.